Bikin baje-kolin fina-finai da masu buga kwallo cikin hotunan Afrika na mako

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan yankin a wasu sassan duniya.

Senegal

Asalin hoton, ZOHRA BENSEMRA / REUTERS

Bayanan hoto, Ranar Talata lokacin wasan ƙwallo ne a Dakar da ke Senegal, inda waɗannan maza ke wasa a kusa da tafki.
Masar

Asalin hoton, MOHAMED ABD EL GHANY / REUTERS

Bayanan hoto, Washegari ranar Lahadi ne kuma manoma suka fara girbi a arewacin Masar, yankin da mabiya Addinin Islama da dama suke zaune.
Pantsula

Asalin hoton, ALET PRETORIUS / GALLO IMAGES / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mambobin ƙungiyar City of Pantsula na shirin faretin da za a gudanar a titin Hillbrow ranar Asabar.
Afrika ta Kudu

Asalin hoton, ALET PRETORIUS / GALLO IMAGES / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mawaƙa da jama'a da dama sun halarci bikin wanda ake gudanarwa duk shekara a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.
Bikin fina-finai

Asalin hoton, SAMEER AL-DOUMY / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A nan kuma ɗan wasan ƙwallo da ƴar fim a wurin bikin baje-kolin fina-finai.
Tennis

Asalin hoton, JULIEN DE ROSA / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mayar Sherif ƴar ƙasar Masar yayin da ta fuskanci abokiyar karawar ta a ƙwallon Tennis Liudmila Samsonova ƴar ƙasar Rasha ranar Litinin a birnin Paris.
Mc Alger

Asalin hoton, BILLEL BENSALEM / NURPHOTO / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A babban birnin Algeria wasu mata na kallon zanen hoton ƴan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta MC Alger ranar Lahadi.
Kabilar Zulu

Asalin hoton, RAJESH JANTILAL / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mambobin ƙungiyar Isicathamiya ta Afrika ta Kudu lokacin da suke rera waƙa a Durban ranar Asabar. Waƙoƙin ƙungiyar sun samo asali ne daga ƙabilar Zulu da suka yi hijira.
Kongo

Asalin hoton, HUGH KINSELLA CUNNINGHAM / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ma'aikatan gandun dabbobi na bin sawun garken giwa ta hanyar amfani da na'urar bin diddigi a dajin Upembi da ke Kudu maso Gabashin Kongo.
Moroko

Asalin hoton, JEWEL SAMAD / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wani mai shago zaune a ƙofar kanti yana jiran masu sayen kaya ranar Laraba a Rabat babban birnin Moroko
Libya

Asalin hoton, MAHMUD TURKIA / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wannan babban kifin na daga cikin kifayen da aka kai kasuwa don sayarwa a Tripoli babban birnin ƙasar Libiya, ranar Juma'a.
Dodon koɗi

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Dodon Koɗi na cin ganye da mangoro yayin nunin kayan amfanin gona a Ivory Coast ranar Lahadi.
Namibia

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Laraba ne Namibia ta gudanar da bikin tunawa da kisan kiyashi na farko yayin da ƙasar ke ci gaba da neman diyya daga Jamus.
Kelly Smith

Asalin hoton, SUMAYA HISHAM / REUTERS

Bayanan hoto, Wata uwa ƴar Afirka ta Kudu mai suna Kelly Smith na hawaye ranar Alhamis yayin da aka yanke mata hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda ta sayar da ƴarta mai shekara shida Joshlin Smith, a watan Fabrairun shekara ta 2024.
Tunisia

Asalin hoton, FETHI BELAID / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Nan kuma lokaci ne da wasu karnuka uku nau'in saluki ke yin tsere a bakin kogi a Tunisia ranar Juma'a.