Yadda za ku gane wanda ya kamu da cutar sanƙarau

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Sanƙarau wata cuta da ke shafar fatar da ke kare ƙwaƙwalwa da kuma lakkar ɗan'adam - wato yaɗi guda uku da suka zagaye ƙwaƙwalwa da kuma lakka.

Cuta ce da ta fi yaɗuwa a lokacin zafi, sannan kuma akwai abubuwa da dama da ke haddasa ta.

Sanƙarau ta ƙwayar cutar bakteriya: Wannan ce cutar sanƙarau mafi haɗari, kuma tana iya yin kisa cikin ƙanƙanin lokaci idan ba a samu kulawa cikin lokaci ba. Nau'ukan ƙwayoyin bakteriya da ke haddasa wannan cuta na haifar da guba a cikin jini, sannan ya yaɗa ta zuwa sassan jikin ɗan'adam.

Sanƙarau ta ƙwayar cutar Virus: Wannan ce wadda ta fi yawa cikin nau'ukan cutar sanƙarau, sai dai kuma ita ce wadda ta fi rashin hatsari. Duk da cewa tana sanya mutum cikin hali na rashin lafiya amma ba ta cika yin kisa ba.

Wane ne sanƙarau ya fi kamawa?

...

Asalin hoton, Getty Images

Cutar sanƙarau za ta iya kama kowa, duk da dai ta fi kama yara. Sai dai manyan mutane masu fama da cutar da kan shafi garkuwar jiki, kamar masu fama da cutar kansa, na cikin hatsarin kamuwa da cutar sosai.

Ta yaya sanƙarau ke yaɗuwa?

Ƙwayoyin cutar da ke haddasa cutar sanƙarau na yaɗuwa ne daga mutum zuwa mutum ta hanyar kusanci ko haɗa jiki ko kuma ta hanyar tari ko atishawa ko sumbata ko cin abinci da cokali ɗaya.

Wasu mutanen na iya yaɗa cutar ba tare da sun san suna ɗauke da ita ba, akasarin mutanen da ke ɗauke da ita ba su sani ba.

Matsalar ita ce waɗanda ke ɗauke da cutar ba tare da suna da masaniya ba, suna iya yaɗa ta ga mutane masu rauni kamar ƙananan yara da kuma tsofaffi.

Shi ya sa yara ɗalibai waɗanda ke karatu a makarantu masu cunkoso suke saurin kamawa da kuma yaɗa cutar.

Alamomin sanƙarau

Duk da cewa akwai nau'ukan sanƙarau daban-daban, to amma akwai wasu alamomi da za a iya lura da su waɗanda za su nuna cewa mutum ya kamu da cutar:

  • Zazzaɓi
  • Amai da gudawa
  • Ciwon kai mai tsanani
  • Rashin son haske
  • Taurin wuya
  • Ɗimaucewa
  • Fita daga hayyaci
  • Shiɗewa
  • Fitowar ƙuraje

Ƙarin alamomin sanƙarau ga yara

Wasu ƙarin alamu da suka kamata a lura da su a yara su ne:

  • Rashin cin abinci
  • Kumburi mai tashi a kai
  • Rashin kuzari
  • Taurin jiki

Me ya kamata a yi idan aka ga alama?

Masan na cewa da zarar aka ga irin waɗannan alamu to ya kamata a hanzarta zuwa asibiti nan take - sannan kuma ba dole ne sai an jira an ga dukkanin alamun da aka lissafa ba.

Kariya

Babbar hanyar kariya daga cutar sanƙarau ita ce ta hanyar rigakafi. Gwamnatoci da dama na samar da rigakafin sanƙarau kyauta a asibitoci, waɗanda ake sakawa cikin jerin alluran rigakafi na wajibi.

Saura matakan kariya daga cutar sun hada da:

  • Tsafta
  • Buɗe tagogi
  • Kauce wa cunkoso a cikin ɗaki