Hanyoyin da mai cutar ulcer zai bi don yin azumi cikin sauƙi

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin abubuwan da suke jan hankali a duk lokacin da azumi ya zo, musamman a yankin arewacin Najeriya, shi ne batun cutar ulcer, inda har malamai suke yawan amsa tambayoyi kan azumin mai cutar.
Ramadan dai wata ne mai alfarma wanda musulmi suke yin azumi a cikinsa ta hanyar daina cin abinci da abin sha daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sai dai duk da cutar, wasu na ƙoƙarin ganin sun yi azumin, duk da cewa idan ta yi ƙamari mutum yakan ajiye, ya jira har ya samu sauƙi.
Cutar ulcer wadda ake kira da gyambon ciki, cuta ce da take samuwa idan wani ɓangare na jikin mutum kamar maƙoshi ko tumbi ko kuma wani ɓangare a cikin ƙaramin hanjin mutum ya buɗe ko ya ƙwarzane.
Idan aka samu haka ne sai wurin ya zama ciwo, wanda hakan ke jawowa ƙugin ciki ko zafin ciki.
Sai dai likitoci sun ce akwai wasu abubuwan da dama da suke jawo mutane su rinƙa jin zafin ciki bayan cutar ta ulcer, wanda hakan ke nufin ba daga jin zafin ba ne za a ce akwai cutar.
Haka kuma likitoci sun ce kamar yadda ciwo a waje yake warkewa, haka nan ma ciwon da yake cikin - wato ulcer - yana warkewa idan an yi abin da ya dace.
Azumin mai ulcer
BBC ta tuntuɓi likita domin amsa tambayar yadda ya kamata mai cutar ya tsara ci da sha domin ganin ya yi azumi lafiya ƙalau.
Dokta Aisha Jafar Mohammad, likita ce a asibitin ƙananan yara na Khalifa Sheikh Isyaku Rabi'u Paediatric da ke Kano, wadda ta ce akwai abubuwan da ya kamata masu ulcer su kula da su kamar haka.
- A je asibiti a tabbatar da akwai cutar ko babu ita.
- A riƙa shan magani lokacin sahur da buɗa-baki
- A guji cin abinci mai maiƙo lokacin sahur da buɗa-baki
- A guji cin soyayyen abu irin su ƙosai da sauransu
- A rage cin abinci masu yaji sosai musamman bayan buɗa-baki
- A rage cin abinci da za su kumbura ciki da ake kira gas
- A riƙa yawan cin abinci masu ruwa-ruwa marasa tsami.
- A rage shan madara saboda tana ƙara zafafa wa wasu cutar.
- A ci kaza da ƴaƴan itatuwa
- A guji kwanciya da zarar an gama cin abinci
Matakin cutar da za ta bari a yi azumi
Sai dai Dokta Aisha ta ja hankalin masu cutar da su tabbatar sun je asibiti a tabbatar da cutar, saboda a cewarta likitan ne kaɗai zai iya tabbatar ko akwai cutar ko babu, sannan ko cutar za ta iya bari ya yi azumi ko ba za ta bari ba.
Ta ce yanayin cutar ce likitan zai gani, sai ya ba da shawara a ɗauki azumin, amma a riƙa shan magani.
"Akwai magunguna da ake kira Proton pump inhibitors (PPIs) da ake ɗora masu cutar. Magunguna ne waɗanda suke hana fitowar sinadarin da jiki ke fitarwa waɗanda idan suka taɓa ciwon (olsa ɗin) sai ya tayar da zafin. Sannan akwai magangunan da ake kira anti-acid da zai riƙa sha," in ji ta.
Sai dai likitar ta yi gargaɗin cewa ba duk zafi ko ƙogin ciki ba ne cutar olsa, domin a cewarta, akwai wasu abubuwa da dama da suke jawo zafin ciki da ba cutar olsa ɗin ba ne.










