Cututtukan da idan aka kamu da su ba za a warke ba har abada

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
Akwai wasu cutuka da a rayuwar dan adam idan ya kamu da su ba a taɓa warkewa har abada kamar yadda masana harkar lafiya suka ce.
Da yawa daga cikin cututtukan babu ruwansu da bambancin shekaru, wasu kuma suna da alaƙa kai-tsaye da shekarun.
A wasu lokutan wasu cututtukan ana haifar yara da su, amma akwai waɗanda ake gada daga wajen iyaye ko kakanni kuma ba a warkewa.
Bari mu tattauna kan wasu daga cikin irin waɗannan cututtuka masu matukar haɗari ga rayuwar ɗan adam:
Ciwon ƙoda
Ita ƙoda tana da tsarin ɓangare biyu. Ko wacce girmanta ya kai dunƙulen hannu.
Aikinta shi ne tace sauran ruwan jiki mara amfani da kuma dattin jini sai ya zama fitsari.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ciwo na nufin ƙodar mutum ta daina aikin tace jini kamar yadda ya kamata.
Masu ciwon suga da masu fama da hawan jini sun fi kowa haɗarin kamuwa da wannan cuta.
Ana iya maganin wannan matsala ne kawai ta hanyar dashen wata ƙodar, ko kuma a rika yin wankin ƙoda lokaci zuwa lokaci.
Kana cikin haɗarin kamuwa da cutar ƙoda idan kana da waɗannan cututtukan:
- Cutar Hawan Jini
- Ciwon Suga
- Ciwon Zuciya
- Sai kuma idan a tsatsonku akwai wanda ya taɓa kamuwa da wannan cuta
A kan samu sauƙi idan aka ɗauki wadannan shawarwari:
- Rage yawan cin gishiri
- Yawan cin ganyaye kayan itace
- Motsa jiki akai-akai
- Ƙauracewa yawan shan taba da barasa

Cutar Asma
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar asma na kama kowanne irin nau'i na mutane amma ta fi kama mutum tun daga yarinta.
Cuta ce da ba ta bari a yi numfashi yadda ya kamata, kuma garin ƙoƙarin numfashin ƙirjin mai ita na toshewa sai ya riƙa numfashi tare da wata ƙara kamar fito.
Amma wuyarta da ake sha, ta danganta ga maras lafiyar, wani tana damunsa duk bayan sa'a ɗai-ɗai, wani kuma kwanaki, wani kuma yakan ɗauki dogon lokaci ba ta tashi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanayin ya ta'allaƙa da hanyoyin wucewar numfashin da suke da alaƙa da huhu, kuma hakan yakan shafar jijiyoyin da iska ke bi, don hakan sai su riƙa fusata cikin gaggawa.
Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa mafi yawan masu fama da cutar Asma ba sa amfani da na'urar daƙile cutar yadda ya kamata a lokacin gaggawa.
Binciken wanda wata cibiya mai suna UK Asthma ta gudanar, ya nuna cewa ba a koyawa masu fama da cutar ta daukewar numfashi yadda ake amfani da na'urar.
A kuma cewar wata cibiya mai suna Allergy UK, masu cutar sukan shiga rudani idan sun tashi amfani da ita.

Hawan jini
Hawan jini cuta ce da ake kamuwa da ita ta dalilin toshewar wasu jijiyoyin jini da suke kai wa ƙwaƙwalwa saƙo, kuma da zarar sun gaza ayyukansu to matsala ta faru.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, cikin wani rahotonta, ta ce akwai kimanin mutum biliyan 1.13 da ke fama da wannan cuta a duniya, kuma kashi biyu cikin uku masu matsakaicin samu ne.
Wani bincike da WHO ta yi a 2015 ya nuna cewa namiji 1 cikin 4 na fama da wannan cuta, yayin da 1 cikin 5 a mata ke fama da hawan jini.
Hawan jini cuta ce mai wahalar sha'ani wadda ba a warkewa daga gare ta da zarar an kamu da ita.

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, wani bincike da aka yi ya ce sama da mutum miliyan 100 ne ke fama da wannan cuta, kuma maimakon raguwa kullum ƙaruwa adadin yake saboda tsarin yadda mutane ke rayuwa, da kuma irin abin da mutane ke ci ko sha, in ji shugaban asibitin koyarwa na Legas Farfesa Adewale Oke.
Saboda rashin zuwa asibiti da yawan mutane na fama da wannan rashin lafiya amma ba ma su san suna da ita ba.
Abubuwan da ke janyo cutar
- Ƙiba ko kuma nauyin jiki
- Damuwa a kwakwalwa
- Shaye-shaye
- Yawan cin gishiri
- Cutar ciwon siga
- Cin abinci mai kitse
- Gado
- Rashin motsa jiki

Ciwon Suga
Da yawa a yankin kasashen nahiyar Afrika ana ganin sukari wanda a Ingilishi ake kira (White Sugar) na da alaƙa da ciwon suga (Diabetes).
Masana na cewa wannan ciwo ne da aka fi gado a mafi yawan lokaci - duk da yake a wasu lokutan kuma ko mutum bai yi gado ba, yana iya kamuwa da shi.

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa wani kwararran likita ne da ke Abuja, ya bayyana wannan cuta a matsayin gazawar wani sinadari da ake kira (Insulin) ko kuma rashin sinadarin baki daya a jiki, wanda aikinsa shi ne tunkuɗa sugan da ke cikin jinin mutum zuwa in da ya kamata ya je.
Nau'o'in Ciwon Suga
1. Akwai nau'in farko da ake kira Type 1- wanda mutanen da ba su gaji ciwon ba daga zuri'arsu ke fama da shi.
An fi samunsa a jikin kananan yara ko kuma daga kan 'yan shekara 20 zuwa kasa.
Masu wannan nau'in su ne mafi karanci a duniya, "domin yawansu bai wuce miliyan daya da digo biyu ba a duniya baki daya," in ji Dakta Salihu Kwaifa.
Masu wannan nau'in su ba su da sinadarin Insulin duka a jikinsu, kuma za a ga alamun suna dauke da ciwon saboda suna zuwa da rama da yawan fitsari da yawan jin ƙishirwa da kuma yawan shan ruwan, kamar yadda likitan ya zayyana.
2. Akwai nau'in Type 2 - wannan nau'in ya fi yawa tsakanin mutane, ya fi addabar mutanen da ke tsakanin shekara 20 zuwa 79.
Masana na cewa akwai a ƙalla masu fama da cutar a duniya fiye da mutum miliyan 560.

Ciwon ƙashi

Asalin hoton, Getty Images
Wannan wani ciwo ne da ke addabar ƙashi, ana kamuwa da wannan cuta ne ta hanyoyi daban-daban.
Wani lokaci ana kamuwa da wannan ciwo idan aka ji rauni sai ƙwayoyin cuta irin na (bacteria) suka shiga, wajen sai ya janyo ruwa a cikin gaɓar da aka ji ciwon, a wasu lokutan kuma mutum na jin rauni ne tun lokacin ƙuruciya sai girma ya zo sai ciwon ya dawo.
Wannan ciwo na da nau'uka, akwai wanda ake warkewa da wuri wanda ake kira (Acute Arthritis) ba ya wuce wata ɗaya zuwa biyu ake samun sauƙi.
Akwai na (Chronic Arthritis) wannan kan ɗauki lokaci daga wata shida zuwa sama kan a fara samun sauƙi.
Ciwo ƙashi dai ba shi da wani tsayayyan magani da za a sha a warke, sai dai maganin da ke kashe zafin raɗaɗin da ake ji.
In ku gaɓar ta cinye da yawa to sai dai a yi dashi, kamar yadda ake dashin gwiwa ko cinya, a sanya ƙarfe a cikin jikin.
Amma kafin nan a kan iya yi wa gaɓɓan gashi, domin samun sauƙi amma ba warkewa ba.
Ƙarin labarai masu alaƙa
Abubuwan da kan ƙara ta'azzara ciwon
Shekaru: Wannan cuta kan iya kama kowa, amma ta fi saurin bayyana da kuma yin illa ga manya da suka kai shekara 60.
Jinsi: Kashi biyu cikin uku na sabbin masu kamuwa da wannan cuta mata ne, don haka sun fi maza haɗarin kamuwa.
Gado: Mutanen da ake haihuwa da wasu matsaloli irin na rashin lafiya na cikin haɗarin kamuwa da wannan cuta.
Shaye-shaye: Bincike ya nuna masu shan sigari na cikin haɗarin kamuwa da wannan cuta, in kuma suna da ita to sai ta ƙara munana.
Rashin haihuwa: Matan da ba sa haihuwa sun fi haɗarin kamuwa sama da masu haihuwa.
Ƙiba: Ƙiba ita kanta na tattare da wasu matsaloli na rashin lafiya ciki kuwa har da haɗarin kamuwa da cutar ciwon ƙashi.
Akwai abu guda da ke ragewa mata haɗarin kamuwa da wannan cuta - Shayarwa: shayarwa na rage wa mata haɗarin kamuwa.











