Maganin hawan jini ya fi amfani lokacin barci

clock and pills

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health editor, BBC News online

Domin samun nasarar amfani da maganin cutar hawan jini, yi kokari ka kiyaye shan maganin kafin ka yi barci.

Wannan wata hanya ce mai sauki da za'a iya kubutar da rayuwa kamar yadda mujallar 'European Heart' ta ruwaito.

Magungunan suna ba da kariya daga faruwar bugun zuciya da kuma shanyewar jiki, idan aka sha su da dare kafin a kwanta barci, maimakon da safe kamar yadda bincike ya nuna.

Masana sun yi ittifakin cewa jikin dan adam kamar agogo ne da ke da lokuta na musamman da ya fi bukatar karbar magani.

Samar da lokacin da ya dace don ba wa jiki magani

Akwai kwararan shaidu da suka nuna cewa magunguna da dama da suka hada da na ciwon zuciya sun fi amfani a wasu kebabbun lokuta.

Gwajin baya-bayan nan shi ne mafi girma da aka taba gudanarwa kan cutar hawan jini, da ya hada da masu shan maganin cutar 19,000.

Gwajin da aka yi a kasar Spaniya.

Da farko an kasa masu shan maganin ciwon hawan jini gida biyu.

Kashi na farko sun sha maganin ne da safe yayin da kashi na biyu suka sha da dare kafin suyi barci.

Masu gwajin sun rika bibiyar abun da ke faruwa, har tsawon kwanaki biyar ko fiye.

kashi na biyu da suka sha maganin a lokacin da za su kwanta barci sun kaucewa samun bugun zuciya da ka kai ga mutuwa ko shayewar barin jiki da kashi 50 cikin dari.

pill box

Asalin hoton, Getty Images

Da ma hawan jini ciwo ne da ke lafawa da dare, lokacin da dan adam ke hutawa ko kuma ya ke barci.

Idan har irin wannan lokaci bai sa cutar ta sauka ba, to kuwa ta yi tsanani sosai kenan, da za ta iya haifar da bugun zuciya ko shanyewar jiki ga mai ita ko da wane lokaci kamar yadda masana su ka gano.

Haka kuma binciken ya bayyana cewa shan magani da yamma ko kuma lokacin barci na sa a iya gane yadda matakin hawan jinin mutum ya ke, musamman ga wadanda ke fama da cutar.

Duk da babu wani tsari da aka fitar don shan maganin cutar hawan jini, kuma likitoci sun fi ba da shawarar shan maganin cutar da safe, da nufin saukar jini da safe wanda kuma wani dalili ne da ba ingantacce ba.

Vanessa Smith ta gidauniyar kula da zuciya ta British Heart Foundation, ta ba da shawarar cewa idan mutum yana amfani da maganin cutar hawan jini, yana da kyau ya tuntubi likita kafin ya sauya lokacin da ya ke shan magani, duk da fahimtar tasirin da zabar lokacin shan magani ya ke da shi.

Ta kara da cewa akwai dalilai da ya sa likitocin ke zabar wa marar lafiya lokacin da zai sha magani.

Yanayin tsarin rayuwa shi ma yakan yi tasiri kan cutar hawan jini.

A kan haka ne masana ke kira da a guji wasu abubuwa kamar haka:

  • Shan giya
  • Shan tabar sigari
  • Kiba
  • Rashin motsa jiki
  • Yawan cin abinci mai gishiri sosai