Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gidan yarin riƙaƙƙun masu laifi da ke da gidan rawa da sashen ajiye dabbobi
- Marubuci, Ronna Risquez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Special report for the BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Venezuela
Samamen da aka kai gidan yarin Tocoron bisa umarnin gwamnatin Nicolas Maduro ya tarwatsa cibiyar gudanar da ayyukan gungun Tren de Aragua, daya daga cikin kungiyoyin masu aikata laifuka da ake addabar Venezuela da nahiyar Latin Amurka.
Samamne ya yi tasiri a yankin da ke kewaye da gidan yarin. Yanzu ba a ganin dumbin mata dauke da kayan abinci da tufafi suna kaiwa ga ’yan uwansu da ke arkame a kurkukun. Haka kuma babu yaran da suke azazzalawa uwayensu don su sami daman isa tafkin ninkaya da sauri. Masu sayar da giya da galibin wuraren kasuwanci a garin Tocoron da ke jihar Aragua sun rufe.
Ginannun shaguna da rumfunan da ke gaban gidan yarin, inda ake cajin masu ziyara dala daya don adana wayoyinsu, bisa ga dukan alamun an yi watsi da su. A halin da ake ciki, ana ci gaba da rusa gine-ginen da ke cikin gidan yarin.
Ban yarda ba lokacin da gwamnati ta sanar da cewa ta sake kafa iko a gidan yarin Tocoron. Kasa da shekara guda da ta gabata na kasance a wurin, domin ina so in ga yadda gidan yarin da ya zama karagar mulkin kungiyar Tren de Aragua yake don nin sami damar kammala littafin da nake rubutawa game da wannan gungun masu aikata laifukan, wanda suka addabi nahiyar baki daya.
Wannan shi ne abin da na gani a lokacin da na shiga yankin el Niño Guerrero, shugaban kungiyar kuma wanda yanzu ya kasance daya daga cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo a nahiyar.
'In zagaya da ku ne?'
"Wannan shine karo na farko da ki ka zo nan?" Julio ya tambaye ni, shi wani fursuna ne da muka hadu da shi ranar Lahadin da na ziyarci gidan yarin kuma ya nuna mani wuraren da ake da su a gidan yarin na Aragua, wanda aka fi sani da Tocoron, ko kuma kamar yadda fursunonin ke kiransa: Babban Gida.
An gina wannan gidan yarin ne a shekara ta 1982 a garin Tocoron mai tazarar kilomita 140 ta gefen kudu maso yamma da babban birnin kasar Venezuela, Caracas. A bisa ka'ida, gidan yarin na da karfin dakuar fursunoni 750, amma ya zo ya kasance gidan fiye da fursunoni 7,000 a cikin shekarun da kungiyar Tren de Aragua ta habaka, tsakanin 2015 da 2018.
"In zagaya da ke ne?" Julio ya dage, kamar yin rangadin wuraren da ke cikin gidan yarin abu ne da bai kamata ka bari ya wuce ka ba . Ban san abin da zan gani ba.
Yayin da na ke zagaya wurin abin da na gani ya daure mun kai. Tocoron ba irin kurkukun da aka sani ba ne, filin shakatawa ne. Ya kasance kamar abin da ake gani a shirye-shiyen talabijin.
Wuraren ninkaya da gidan ajiye namun daji da filayen wasanni da kananan gidaje masu rufin kwano, da gidajen cin abinci da filin wasan baseball da ramin fadan zakara da shagunan sayar da magunguna da kuma babura da bindigogi... Dukkan hotunan da suka rika yawo a kafafen sada zumunta bayan samamen da aka kai kwanakin baya da gaske ne.
"Guerrero," in ji Julio, yana nufin Hector Rusthenford Guerrero Flores, wanda aka fi sani da el Niño Guerrero, shugaban Tocoron da Tren de Aragua, "koyaushe yana cewa ba zai huta ba har sai ya mayar da wannan kurkukun zuwa tamkar birnin Tocoron," in ji shi yayin da mu ka yi hira a wani wurin karban baki inda akwai talabijin da kujerun katako da kuma tebura.
A Venezuela, wuraren zama, inda masu matsakaici karfi da masu arziki ke zama, ana kiransu birane. Amma Tocoron ya kasance kusa da zama karamin birni.
Gidan yarin yana da katafaren kamfanin wutar lantarki wanda zai yi amfani da shi yayin gazawar samar da makamashin da ya zama ruwan dare a Venezuela. Har ma tana da nata tawagar kwararru ( fursunoni), sanye da rigar wando da riguna kala-kala, wadanda ke da alhakin kula da kula da wutar lantarkin gidan yarin.
Gidan yarin yana da katafaren tashar wutar lantarki wanda zai yi amfani da shi idan aka sami gazawar samar da makamashin da ya zama ruwan dare a Venezuela. Har ila yau gidan yarin na da tawagar kwararru ( fursunoni), wadanda ke da alhakin kula da wutar lantarkin gidan yarin.
Julio ya ce, "Kwararrun da ke nan suna da kyau sosai har a kan neme su daga waje su yi aikin gyara idan aka samu rashin wutar lantarki a garuruwan da ke kusa."
'Masu gidajen caca'
Burin Guerrero na mayar da Tocoron zuwa birni zai iya bayyana yawan gine-gine da wuraren shakatawa da ke cikin kurkukun, da kuma sha'awar samun tsari da tsaro.
Dukkanin yankunan gidan yarin mutane ne dauke da bindigogi kirar AR-15 ko AK-103, da kuma kananan bindigogin hannu kirar 9mm ne suke gadin su. Wadannan masu gadin kuma fursunoni ne da aka fi sani da “gariteros” a tsakanin fursunoni.
Gidan ajiye namun daji, wanda ke bayan wani babban dutse mai yawan ciyayi, yana da masu gadi biyu da ke kula da dabbobin. An ce Guerrero ya yi asarar wani maciji mai muhimmanci a gare shi, tun daga lokacin, shugaban ya tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
Tsuntsaye da birai da jiminai da manyan maguna da kaji da dawakai da aladu da shanu duk suna cikin keji ko sararin da aka kyallace da ya dace da kowane nau'in dabba. Har ma suna da kananan alamu ko katunan da suka bayyana yanayin duka dabbobin.
A wannan yankin kuma akwai wurin fadan zakaru, akwai wani gini mai ban sha'awa inda fursunoni za su iya yin caca a kan fadan zakarun. A kusa da wurin kuma akwai filin wasan kwallon kwando mai ciyawar da aka dasa wanda shugaban ya gyara.
Karshen Tocorón
Wasu mutane biyu dauke da bindigogi suna sa ido kan duk abin da na ke ke yi na a lokacin ziyarar ta wa daga tazarar kimanin mita uku. Na ci karo da mutane dauke da makamai a kowane mita 100, ban da wasu da ke tafiya a kan manyan babura.
Na sami wuraren da ake caca kan tseren dawaki, kuma abin da ya fi daukar hankali shi ne shagunan da aka kebe musamman don siyar da miyagun kwayoyi: daga tabar wiwi zuwa hodar iblis da sauran kayan maye da ake hada wa.
A kowane mataki na gane wuraren da na ga hotunan su ko kuma bidiyo da aka zakulo a shekarar 2016, ko kuma wanada na gane bisa bayanin mutanen da na sani. "Ga shi can. Gidan rawa na Tokio ke nan," Na fada a zuciyata lokacin da muka wuce ta sanannen wurin, wurin da aka yi shahararrun bukukuwan Tocoron.
Ya yi wahalan ganewa domin an lullube gadan da wani bakin labule. Bayan fita daga gidan yari, wani tsohon dan kungiyar ya bayyana min cewa a tsakiyar shekarar 2022 shugabannin sun samu umarni daga gwamnati (ba tare da bayyana a ina ko daga wane ba) na rufe gidan rawar ga jama’a. Abu ne na sirri, na rashin ci gaba da jan hankali, saboda an cigaba da gudanar da bukukuwan daga cikin gidan yarin.
Wannan matakin mai yiwuwa ya kasance alama ne na farkon karshen Tocoron.
A wancan lokacin, Guerrero ya kuma umarci abokan tarayyarsa da su dakatar da haramtaciyar kasuwancin sayar da motocin da ake yi daga gidajen yari daban-daban ta shafin Kasuwancin Facebook. Bangarorin al'umma daban-daban dai sun shiga cikin badakalar wanda har ma ta shafi jami'ai da dama.
'Wannan gidan yarin na masu kudi ne
Mun yi hira da Julio yayin da mu ke cin burodi nau'in baguette da na kawo masa. Ba koyaushe yake samun damar yin burodi ko abin sha ba. Ba kasfai ya ke samun baki ba.
Duk da haka, ya fada min cewa a Tocoron akwai fursunoni da ke cikin mummunar yanayi.
Wasu ana kiransu "tumaki" kuma sun kasance a kasan yanayin zamantakewa a cikin kurkukun. Su ne Fursunonin da ba su da iyali ko kuma suka keta wasu dokokin da shugaban ya kafa.
An tsare su a wasu wurare kuma ba su da damar shiga wuraren ninkaya da gidajen cin abinci da kuma gidan rawa. Don a gane su dole ne su sanya riguna masu dogon hannu da ke da zane-zane ko ratsan hannu kuma su sanya taye. Yawancin wadannan mutane sun yi kama da masu jinyunwa kuma suna tafiya kaman aljanu.
“Wannan na masu kudi ne. Wannan gidan yarin na masu kudi ne. Komai kudi ne a nan," Julio ya yi gargadi. "Dukkanmu dole ne mu biya dala 15 (wannan shine abin da fursuna ke biyan shugaban don ya ci gaba da zama a gidan yarin ba tare da an yi masa duka ba) kowane mako. "
Farashin sauran 'ayyuka' ya bambanta: dala 20 don hayar wurin kwana na mutum daya, ko dala 30 don abokan zama su kasance tare da su a karshen mako, da sauransu.
Abin ya ja hankalina da na ga cewa a cikin gidan yarin akwai wuraren kasuwancin da ke tallata Balenciaga da Gucci ko Nike a tagoginsu, wanda ya nuna alamun irin adadin kudin da ke cikin gidan yarin.
Abin da ban sami gani a gidan yarin ba shi ne gidajen shugabanni, domin suna cikin wani yanki ne da sai wqadanda ke kusa da shugabannin Tren de Aragua kadai za su iya shiga. Na gano cewa akwai wuraren ninkaya da wuraren gasa nama da aka gina wa shugabanni a wurin.
An wargaza wannan duniyar bayan samamen da gwamnatin ta kai, wanda jami’an tsaro 11,000 suka gudanar.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Venezuela Admiral Remigio Ceballos, wanda ya jagoranci kwato gidan yarin ya ce "Mun gano wasu wurare da yawa da ba su isa ba don gudanar da irin wannan wurin."
A halin da ake ciki ba a san makomar Julio ba, kamar yadda ba a san makomar dimbin fursunonin Tocoron da kuma na shugabansu, el Niño Guerrero, wanda a halin yanzu ya tsere kuma ana kan farautarsa.
Kame gidan yarin ya kawo mummunan cikas a al'amuran kungiyar masu aikata laifuka, amma ba a sani ba ko wannan shi ne karshen gungun masu tayar da hankalin wanda daga wannan gidan yari na Venezuela, suka fadada ayyukan ta'addacinsu zuwa Colombia da Brazil da Peru da Ecuador da Bolivia da Chile, da mai yiwuwa ma har da Amurka.