Yunwa da fyaɗe sun mamaye mutanen da suka tsira daga yaƙin Sudan

d

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Fararen hular da yaƙin basasar Sudan ya rutsa da su, sun bayyana wa BBC yadda fyaɗe da rikicin ƙabilanci da kuma kashe mutane kan titi suka riƙa tayar musu da hankali.

Wakilin mu ya samu damar tattaunawa da wasu mutane da ke yankin da ake wannan yaƙi a Khartoum babban birnin Sudan.

Manyan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce rikicin ya jefa Sudan cikin "ɗaya daga cikin waɗanda suka jefa fararen hula cikin matsanancin hali a tarihin duniya na baya-bayan nan" kuma zai iya haifar da yanayin yunwa mafi muni a duniya.

Akwai kuma fargabar cewa a Darfur da ke yammacin ƙasar, za a iya samun maimaicin abin da Amurka ta kira kisan ƙare dangi da aka yi shekaru 20 baya, a ƙasar.

A gefe guda kuma, an samu wata mummunar fashewar wani abu a Omdurman. Yansanda sun ruɗe suna ta ihu suna gudu, ba su sani ba suna tafiya ne inda ake ci gaba da harbi: "ku koma baya, ku koma baya, za a iya samun ƙarin fashewar." yayin da baƙin hayaƙi ya mamaye ko'ina.

Gabanin nan, an riƙa dukan mutanen da suke tafiya a kasa saboda kwasar shinkafa da biredi da kuma kayan miya da suke yi daga wasu shaguna, waɗanda sai kwanan nan ake sake buɗe su.

A tsakiyar watan Febrairu kuwa, dakarun Sudan sun sake karɓe iko da birnin - ɗaya daga cikin yankun da ke gefen Kogin Nilu da suka kafa wagegen birnin Khartoum.

Yanzu dai fararen hulu sun fara komawa, sai dai har yanzu akan samun saukar manyan abubuwan fashewa irin wanda suka riƙa fashewa a tsakiyar titunan birnin a baya.

Ga kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje, abu ne mawuyaci samun labaran wannan yaƙi na basasa wanda aka fara a watan Afrilun bara - amma BBC ta yi sa'ar samun wannan dama.

d

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Neman iko ta kowanne hali tsakanin sojin Sudan da tsofaffin ƙawayenta, RSF, ya yi sanadin mutuwar mutum 14,000 a faɗin ƙasar - kuma da yiwuwar adadin ya zarce haka.

Kimanin shekara guda, ɓangarorin biyu suna ta yaƙi da juna domin samun iko da Khartoum da kuma wasu birane da suke makwabtaka da shi.

Dakarun RSF su ne ke da iko da yankunan kudancin babban birnin, da kuma wani sashe mai girma na Darfur da yake da tsirrai, wanda ya kwashe shekaru cikin tashin hankali tsakanin ƙasashen Afrika da ƙasashen Larabawa.

Matan da suka kuɓuta daga Darfur zuwa Chadi da ke makwabtaka sun faɗa wa BBC yadda aka riƙa yi musu fyade - sau da yawa mayaƙan da ke riƙe da makamai ne ke yi musu. Mazajensu kuma sun ce sun yi nasarar tsallake kisan da ake yi musu a gefen titi da kuma sace su da ake yi.

Tawagar BBC da ta samu shiga Omdurman tare da sojoji an riƙa fada mata yadda za ta riƙa ɗaukar labaranta a hankali - muna tare da mai sanya musu idanu a cikinmu amma an hana shi ɗaukar yadda masu ɗauke da bindigar ke ayyukansu.

Sojojin na fargabar duk wani bayani da zai iya ba da haske kan yadda suke ayyukansu a birnin.

A

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Yayin da mai ɗaukar hoton namu ya fara ɗaukar yadda garin ya zama bayan fashewar wani roka, wasu mutane ɗauke da makamai cikin fararen kaya suka zagaye shi, ɗaya daga cikinsu ma ya riƙa nuna shi da bindiga a kai.

Daga baya mun gano masu leken asiri ne da dakarun da ke ɗauke da makamai, amma hakan ya nuna mana irin haɗarin da yankin ke da shi.

Duk da cewa sojoji sun sake karɓe iko da Omdurman, amma mu kan ji harbe-harbe lokaci zuwa lokaci.

g

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Wani ɓangare da suke fafatawar sun yi sansani a gefen Nilu, kogin da ya raba Khartoum da ɓangaren gabashi da kuma Omdurman, inda nan ne yammacin kogin.

Dakarun RSF sun shaida mana cewa sojin Sudan sun girke kwararrun maharba a wasu gidaje da ke tsallaken ruwan waɗanda a baya gine-ginen majalisar dokokin ƙasar ne.

Tsohuwar kasuwar Omdurman da a baya ake yawan hada-hada kuma ba a raba ta da baƙi, yanzu ta durƙushe, an sace kusan duka kayan da ke cikin shagunanta. Mafi yawan ababen hawan da ake gani a kan titi na sojoji ne.

Sama da mutum miliyan uku ne suka tsere daga Khartoum cikin watanni 11 da suka gabata, sai dai wasu mazauna birnin Omdurman sun ƙi ficewa daga birnin. Mafi yawan waɗanda muka haɗu da su tsofaffi ne.

F

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Kasa da kilomita guda daga inda ake fafatawar, wani mutum ne mai suna Mukhtar al-Badri Mohieddin ke tafiya da wata sanda kusa da wani masallaci da aka lalata hasumiyarsa.

" Akwai kimanin mutum 150 da aka binne a nan. Nasan mafi yawansu, Mohamed da Abdallah da Jalal," in ji shi, ya ɗan yi shiru jim ƙadan gabanin ya kira sunan wani Dr Youssef al-Habr, wani fitaccen masanin yaren Larabci.

"Ni ɗaya ne na rage," ya kara da cewa.

An riƙa sukar sojin Sudan kan amfani da manya-manyan bamabamai, ciki har da yankunan fararen hula inda mayaƙan RSF ke ɓoyewa - ko da yake suna yawan cewa "suna ɗaukar matakan kariya" iya iyawarsu domin kare fararen hula.

Mutane da dama sun rika sukar RSF kan sata da hare-hare kan mutane yayin da suke iko da yankin.

"Sun kwashe komai a gidan, sun sace motoci da talabijin, sun riƙa zane tsofaffin mutane har da mata," in ji Muhammad Abdel Muttalib.

Afaf Muhammad Salem, wata dattijuwa ce da ke daf da shiga shekara 60, tana zaune ne da ɗan uwanta a Khartoum lokacin da aka fara rikicin ƙasar.

Ta ce an kai su kusa da kogin Nilu ta hanyar Omdurman bayan da dakarun RSF suka sace su, waɗanda suka sace komai na gidansu kuma suka harbi ɗan uwanta a ƙafa.

"Sun riƙa zane mata da yi wa 'yan mata barazana," in ji ta.

Akwai bayanai kan cin zarafi ta hanyar lalata waɗanda ba a iya tattaunasu a Sudan.

"Cin zarafi ya fi tashin hankali sama da a kwashe kuɗaɗenka baki ɗaya," in ji ta.

'Makamin ɗaukar fansa'

'Makamin ɗaukar fansa'

C

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Waɗanda aka yi wa fyaɗe kan fuskanci kyama da koma baya tsakanin mutane da iyalansu da ma inda suke rayuwa. Shi ya sa da yawan mutane a Omdurman ba su son tattauna wannan batu.

Kilomita 1,000 daga yammaci akwai wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kan iyakar Chadi, wanda a nan sai da aka samu shaida kan cin zarafin mata, wani abu da ya janyo yadda suka riƙa bayar da labaransu.

F

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Amina wata ce da muka sakaya sunanta saboda kare ta, ta ce wani kyamis da ƙungiyar likitoci ta duniya ke tafiyar da shi tana so a zubar mata da ciki ba tare da wani tunani ba.

Matashiyar mai shekara 19 da ta tsere dafa Darfur, ta gano ta samu ciki ne a kwanakin baya. Ta shiga damuwa domin ba ta son iyayenta su sani.

"Ba ni da aure, ban san namiji ba ma," ta bayyana mana cikin damuwa.

Ta shaida mana cewa a watan Nuwamba ne, wani ɗan bindiga ya kama ta, tare da ƙanwarta da wata yayarta lokacin da suke kan hanyarsu ta ficewa daga garinsu Ardamta zuwa Geneina da ke makwabtaka.

"Sauran sun tsere amma ni sai da na shafe yinin tare da su. Su biyu ne, ɗayan ya yi ta yi min fyaɗe kafin daga bisani nima na gudu," in ji ta.

R

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Yadda dakarun RSF ke ƙara faɗaɗa ikonsu a Darfur, tare da goyon bayan ƙawancen masu ɗauke da bindiga na Larabawa, ya haifar da hare-haren ƙabilanci kan ƙabilun bakake na yankin Afrika, musamman ƙabilar Masalit.

Labarin Amina ɗaya ne cikin dubu na labaran cin zarafi kan fararen hula da ya faru a watan Nuwamba, lokacin da RSF da ƙawayenta suka kwace garin Ardamata daga wajen sojojin Sudan.

MDD ta shaida wa BBC cewa sama da mutum 10,000 aka kashe a yankin tun daga watan Afrilun bara.

MDD ta tara shaida ta mutum 120 da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata a faɗin ƙasar, wanda ake cewa lamarin ya fi haka a zahiri.

Maryamu ita ma ba sunanta ba ne - wani ɗan bindiga ne ya yi mata fyaɗe, wanda ya naɗe kansa da rawani, da ka gan shi, kaga mayaƙin larabawa, kuma hakan ya faru ne a watan Nuwamba a garin Geneina.

Da kyar take tafiya bayan faruwar lamarin, in ji ta, tana cewa hakan ya hana ta ficewa daga yankin ta daɗin rai: "Mutane suna ta gudu amma mu ba za mu iya ba, kakata ta tsufa, ni kuma ina ta zubar da jini."

Zahra Khamis wadda ke lura da walwalar al'umma wadda ke sansanin 'yan gudun hijira tana tafiyar da ƙungiyar.

Daga Amina har Maryamu sun fito ne daga ƙabilun Afrika, kamar yadda Zahra ta bayyana, ta ce an fi far wa 'yan ƙabilar Masalit da ke Darfur.

F

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

A lokacin da aka yi yaƙin Darfur shekara 20 baya, wata tawagar Larabawa da ake kira Janjaweed wadda daga nan RSF ta samo asalinta - Shugaban lokacin Omar al-Bashir ya kafa ƙungiyar domin su yi maganin 'yan tawaye na wannan lokaci.

MDD ta ce an kashe mutane sama da 300,000 an kuma yi fyaɗe da yawa kan baƙaƙen ƙabilun Afrika tare da tilasta musu tserewa.

Wasu shugabanin Janjaweed da Shugaba Bashir sun shiga jerin sunanyen waɗanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta duniya ta zarga da kisan kiyashi da aikata laifukan yaƙi. Sun musanta tuhumar da ake musu, babu kuma wanda aka gabatar gaban kotu cikinsu.

Zahra ta yi amannar cewa an riƙa yin fyaɗe tamkar wata "hanyar ɗaukar fansa".

"Suna yi wa mata haka ne, domin sun san suna bar musu baƙin taɓo cikin zuri'arsu," in ji ta.

'In kai ɗan ƙabilar Masalit, kashe ka suke yi'

j

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

A wani tanti na gaba a cikin sansanin, mun gaisa da Ahmat yayin da yake kallon wani bidiyo, wanda BBC ta tabbatar da shi, wanda ya nuna wasu mutane biyar ba tare da makamai ba, an gurfanar da su a kan titi a Ardamata a watan Nuwamba.

"Zan kashe su ne kawai," wata murya take faɗa a cikin bidiyon da larabcin Sudan, kafin daga baya a kashe wasu daga cikinsu.

"Wannan Amir ne wannan kuma Abbas.... Ahmat ya faɗa yana hawaye.

k

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Wannan ne karon farko da matashin mai shekara 30, wanda muka sakaya sunansa ya ga bidiyon yadda aka harbe shi. Ɗaya daga cikin 'yan bindigar ne ya yi bidiyon a watan Nuwamba lokacin da RSF suka kwace iko da garin - sun kuma wallafa bidiyon a intanet.

Ahmat ya ce nan take Amir da abokinsa Abbas suka mutu, amma shi da sauran wasu mutum biyu sun tsira.

Wani katoton taɓo da ke bayan shi ya nuna yadda harsashin da ake harbe shi ya fita ta kafaɗarsa. Ya ce shi malami ne gabanin yaƙin amma sauran fararen hula ne.

"Mun yi fakare ne muka kwanta a ƙasa kamar mun mutu, in ji shi, "Na yi ta addu'a. Ji nake kamar rayuwata ta zo ƙarshe."

Ahmat ya ce wasu dakarun RSF da ƙawayensu ne suka sace shi a kusa da gidansu.

Wasu mutum biyu sun sake bai wa BBC shaida kan sace su da wasu mutane suka yi waɗanda suke zargin suna da alaƙa da RSF a wannan lokaci.

Wani daga jikinsu Yussouf Abdallah mai shekara 55 ya ce daga baya sun tsere daga hannun 'yan bindigar.

Ya ce ya gani da idanunsa yadda suka kashe wata uwa da jaririnta.

"Sun tambaya idan daga kabilar Masalit muke, idan ka ce za su kashe ka ne kawai," in ji shi.

A 2019 ne Sudan ta tsinci kanta cikin wani sabon rikici, yayin da aka fara zanga-zanga kuma soji suka yi juyin mulki wanda ya kawo ƙarshen mulkin Bashir na kimanin shekara 30.

'Muna kan gaɓar yunwa'

h

Asalin hoton, Dany Abi Khalil / BBC

Kimanin shekara guda kenan da hukumomin bayar da agaji na MDD suka yi gargaɗin cewa za a iya fuskantar matsalar aikin agaji, a wasu wuraren kuma ana daf da faɗa wa cikin matsalar yunwa.

Manasek wata yarinya ce yar shekara uku kuma ɗaya ce daga cikin dubban yara da ke fama da tamowa. Ba ta da kwarin jikin da za ta iya tafiya kuma mawuyaci ne ka ga kanta ya tsaya cak.

Mahaifiyarta Ikram ta rungumeta a wani asibiti na Unicef a Port Sudan, wani birni da ke kusa da Baharul Ahmar, inda mutane dubbai suka rika komawa bayan sun tsere wa rikicin Khartoum - kuma nan ne inda ma'aikatun gwamnati da wasu hukumomin bayar da agaji suka koma da ayyukansu.

Ba ta sani ba ko akwai wata cutar da ke damun Manasek, kuma ba ta da kuɗin da za ta iya bayar wa a yi bincike a gano.

"Mun rasa rayuwarmu, mun rasa ayyukanmu," in ji ta, tana cewa mijinta ya tafi arewacin Sudan don yin aikatau, kuma ga farashin abinci ya tashi.

Tana ta kuka, kuma ta kasa cewa komai bayan nan.

Mun ziyarci wata makaranta a Port Sudan. Ajuzuwan da ake zama a koyawa yara karatu yanzu sun cika da iyalai 'yan gudun hijira.

Amurka ta ce duka ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna sun aikata laifukan yaƙi, RSF da ƙawayenta sun ci zarafin mutane, da kuma yunkurin shafe wata ƙabila daga doron ƙasa.

Duka ɓangarorin sun musanta zarge-zargen.

Watanni 11 kenan da aka kwashe ana yaƙin, babu wata alama da ke nuna wani daga ɓangarorin zai iya kawo ƙarshen wannan rikici.