Bikin rantsar da shugaban Senegal da mata masu dafa abincin ƙwalama cikin hotunan Afrika

.

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata aka rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon shugaban ƙasar Senegal matashi kuma shugaba na farko mai mata biyu, Marie Khone Faye da kuma Absa Faye.
.

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wata mace na leƙen abubuwan da suke faruwa a birnin Touba da ke Senegal a ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Birnin ya karɓi baƙuncin masu ziyara daga ƙungiyar Baye Fall ta mabiya addinin Islama, waɗanda suka yi fice da irin ɗinkunan su,
.

Asalin hoton, KHALED ELFIQ/EPA

Bayanan hoto, A ranar Talata a birnin Tana da ke Masar, mata sun taru don yin kahk, wani abincin ƙwalam da maƙulashe.
.

Asalin hoton, ABUBAKER LUBOWA/RETUERS

Bayanan hoto, A Uganda kuwa, wannan matar ta halarci tattakin bikin Good Friday ranar Juma'a a Kampala babban birnin ƙasar.
.

Asalin hoton, MARVELLOUS DUROWAIYA/REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a jihar Lagos, mabiya ɗariƙar Katolika sun gudanar da wasan kwaikwayo game da tarihi.
.

Asalin hoton, MONICAH MWANGI/REUTERS

Bayanan hoto, Yara ƙanana sun bi sahun manya wajen addu'o'in Easter ranar Asabar a St Joanes da ke babban birnin ƙasar Kenya
.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Mazauna Heideveld, wani yanki a birnin Cape Town sun shirya cin abinci ranar Asabar.
.

Asalin hoton, FANNY NOARO-KABRE/AFP

Bayanan hoto, Wani mutum ya tsinci takunkumin barewa lokacin bikin al'adun gargajiya na Festimasq, inda ake baje kolin takunkumai a tsakiyar Burkina Faso.
.

Asalin hoton, MARVELLOUS DUROWAIYA/REUTERS

Bayanan hoto, Akinrodoye Samuel ya faɗa ruwa ya yin da yake ninƙaya a wani kogi da ke Lagos, da nufin samar da kuɗaɗen da zai yi amfani da su wajen wayar kan mutane game da lalurar taɓin hankali don mutane su guji kashe kansu.
.

Asalin hoton, TONY KARUMBA/AFP

Bayanan hoto, Tawagar masu son kallon gasar Safari Rally a Kenya ranar Lahadi.