Shin me ya sa ƴan siyasa ke ziyartar 'Chatham House' a Landan

..
    • Marubuci, Ahmad Tijjani Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi Media Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Chattam House dai wata cibiya ce ta bincike kan manufofi da kuma kudure-kuduren gwamnatocin ƙasashe a duniya.

Cibiyar ta fi mayar da hankali ne kan abubuwa da dama kamar lafiya da ci gaba da tattalin arziki da hada-hadar ƙasa da ƙasa da sauransu.

Ta ƙasance cibiya mai zaman kanta wadda ba ta gwamnati ba. Wani tsohon soja ne ya kafa ta a 1923. Ana kuma kiranta da Chattam House ne saboda wajen da take yana kusa da tsakiyar birnin Landan.

Asalin sunan cibiyar shi ne Royal Institute for International Affairs. Gidan na da sahalewar gidan Sarautar Birtaniya.

Kafin zaɓen 2015 sai da Shugaba Buhari na Najeriya ya kai ziyara cibiyar inda ya je ya yi jawabi.

Sa'annan ko a kwanakin baya sai da manyan ‘yan siyasar Najeriyar suka kai ziyara zuwa wannan gida kamar ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar inda ya je tun a 2018.

Haka kuma a bara ma ɗan takarar Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu shi ma ya je.

Ana kuma sa ran sauran ‘yan takaran kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyun NNPP da Labour wato Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Peter Obi za su kai ziyara Chatham House din.

Muhimmancin gidan Chatham House

..

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gidan Chatham na da muhimmancin gaske saboda ƙasashen duniya da dama sun yarda da inganci da sahihancin bincike da suke gudanarwa kan shugabanci da manufofi ko kudurorin gwamnati kamar yadda Dakta Kabiru Sa’id Sufi, malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami’a da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya bayyana.

Malam Kabiru Sufi ya ce hakan ne ma ya sa cibiyar ta fitar da wata kyauta da take bayarwa ga ƙungiyoyi da kuma ƙasashen da suka yi fice wajen taimaka wa shugabanci da harkokin gwamnati mai suna Chatham Award, wadda aka fara bayarwa a 2005.

Ya ce ita ma Najeriya tana cikin sahun ƙasashe da suka yarda da binciken cibiyar saboda duk abin da ta faɗa ana yarda da shi.

Mai sharhin ya ce gidan ya ƙasance yana shirya taruka inda ake tattauna abubuwa na shugabancin ƙasashe musamman waɗanda suke tunkarar zaɓe domin gano manufofin ‘yan takara da kuma tantance su.

‘‘Ba kowa ne ke iya magana a gidan na Chatham House ba, hasali ma sai an gayyaci mutum kafin yake samun damar zuwa ya baje kolin irin manufofi da yake muradi ko shirin yi idan aka zaɓe shi,’’ in ji malamin.

Tasirin gidan Chatham ga siyasar Najeriya

Dangane da irin tasirin da Chatham House yake da shi ga siyasar Najeriya kuwa, Dakta Kabiru Sufi ya ce wuri ne da kowane ɗan takara idan matsayinsa ya kai zai so a ba shi dama ya je, saboda duk abin da zai faɗa a wurin, gaskiya zai faɗa saboda dokokin da cibiyar ke da shi.

Ya ce tasirin sa ga siyasar ƙasar shi ne duk lokacin da ɗan takara ya je ya yi wani bayani na abin da ke damun ƙasarsa, ya kuma yi alkawarin magance shi, to cibiyar za ta yi bincike don ganin ko ɗan siyasar ya cika alkawarinsa.

‘‘Suna gayyatar ‘yan takara da ke gaba-gaba waɗanda ke da karfi ko ake kyautata musu zato don su je su baje kolin manufofinsu da kudurorinsu,’’ a cewar malamin.

Sannan ya ce kafofin ƴaɗa labarai ma na taimakawa wajen ɗaukar abubuwan da aka tattauna a wurin da kuma yaɗa su wanda hakan zai ɗauki hankalin duniya har ma da Najeriya.

Ya ce ‘yan takara na tafiya da manufofi ƙwarara da bayyana manufofinsu, da kuma ganin cewa sun yi kokarin cika alkawari saboda duk abin da suka faɗa cibiyar tana adana bayanai domin bincike a gaba ko ɗan takara ya cika alkawari ko akasin haka waɗanda kuma abubuwa ne da mai sharhin ya ce za su taimaka wa siyasar Najeriya ba kaɗan ba.

A ina cibiyar ke samun ƙuɗaɗenta?

Dakta Kabiru Sufi ya ce Chatham house na samun kuɗaɗen gudanarwa ne daga gwamnatocin ƙasashe da mutane masu bayar da tallafi da kuma wajen mambobinta.

Ya ce duk wani mamban cibiyar na bayar da wasu kuɗaɗe domin ci gaba da zama ɗan cibiyar.

Ya kuma ce yawancin mambobin sun kasance masu bincike da masana da kuma malaman jami’o’i.

Malamin ya ce duk lokacin da cibiyar ta kira taron bayyana manufofi, hankalin duniya na zuwa gare ta domin mutane su ji kuma su ƙaru, saboda yawancin mutane basu ma san akwai abin da zai faru a wata kasa ba sai an je taron.

‘‘Alal misali, lokacin da za a yi zaɓen 2017 a Kamaru, mutane da dama basu san akwai ‘yan takara da ke adawa da shugaban kasar ba, saboda ba a ji duriyar su ba, ita cibiyar ce ta gayyato waɗannan ‘yan takara domin su zo su faɗi manufofinsu,’’ in ji Dr Sufi.