APC ta goyi bayan Akpabio da Tajudden don shugabancin majalisa ta 10

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta amince da rabon mukamai na shugabancin majalisa ta goma.
Ta ce ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai daga shiyyar Kudu maso Kudu.
Haka zalika, Sanata Barau Jibrin zai kasance mataimakin shugaban majalisar dattijai daga Arewa maso Yamma.
Wata sanarwa da jam'iyyar mai mulki ta fitar, ta ambato kwamitin gudanarwa na APC yana cewa matakin ya zo ne bayan rahotannin tuntuba da tarukan da jam'iyyar ta yi da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Da kuma shugabannin jam'iyya da sauran masu ruwa da tsaki game da rabon mukamai zuwa shiyyoyi daban-daban na kasar a jagorancin majalisa ta goma
A Majalisar Wakilai kuma, APC ta ce tana goyon bayan Hon Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalisar ta wakilai daga Arewa maso Yamma.
Sai Ben Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai daga Kudu maso Gabas.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sanarwar ta ce Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa ya lura cikin mutuntawa da sakamakon taruka tsakanin zababben shugaban kasa da shugabancin kwamitin.
Wannan mataki ya tabbatar da rade-radin da aka dade ana yi cewa APC ta bai wa Sanata Godswill Akpabio matsayin shugaban majalisar dattijai da kuma Abbas Tajuddeen matsayin shugaban majalisar wakilai da za a bude a nan gaba.
Da wuya a iya sani zuwa yanzu, ko wannan mataki na jam'iyyar mai mulki, zai kawo karshen dambarwa da kai ruwa-ranar da ake yi game da neman shugabancin majalisa ta goma.
Sai a watan Yuni ne za a kaddamar da sabuwar majalisar, wadda za ta yi aiki kafada da kafada da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu.
A baya, zaben shugabannin majalisun tarayya ya saba zuwa da zafi, da kuma nuna bijirewa ga shugabancin jam'iyya mai mulki har ma da bangaren zartarwa.
Ko a majalisa ta takwas a shekara ta 2015, 'yan majalisar dattijai sun bijirewa umarnin jam'iyyar APC mai mulki, inda suka zabi Sanata Abubakar Bukola Saraki, matsayin shugabansu a kan dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Ahmad Lawan.
Yayin da majalisar wakilai ta zabi Yakubu Dogara, maimakon Femi Gbajabiamila, dan takarar da jam'iyyar ta goyi baya a lokacin.
Lamarin dai ya janyo zaman doya da man ja a wa'adin farko na jam'iyyar APC, bayan ta kwace mulki daga hannun PDP.
Me zababbun 'yan majalisar suka ce?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Yan majalisar dattijai daga shiyyar Kudu maso Gabas dai, sun shawarci zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kwan da sanin illolin da matakin raba mukaman zai iya haifarwa.
Sun ce batun raba mukamai tsakanin shiyyoyi da kuma goyon bayan wani dan takara da ke neman Shugaban Majalisar Dattijai daga shiyyar Kudu maso Kudu ba tare da la'akari da shiyyar Kudu maso Gabas ba, ba shakka zai iya zama rashin adalci, lamarin da ka iya haddasa tashin-tashina.
Jan hankalin na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro da rukunin 'yan majalisar dattijai na shiyyar Kudu maso Gabas ya fitar, bayan wani taro a Abuja, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Da yake karanta sanarwar bayan taron ga manema labarai ranar Litinin, Sanata Ifeanyi Uba ya ce 'yan majalisar sun ja hankalin zababben shugaban kasar ya yi la'akari da halin da Najeriya ke ciki yanzu don tabbatar da ganin kasar ta ci gaba da bunkasa a doron raba-daidai da hadin kai da kuma adalci.
Cikin masu neman mukamin shugaban majalisar dattijai ta goma, har da Sanata Orji Uzor-Kalu da kuma zababben sanata Dave Umahi, wadanda ke kan gaba-gaba a jerin masu neman mukamin daga shiyyar Kudu maso Gabas.
Majalisar Wakilai
Zuwa yanzu ba a ji wani martani daga bangaren masu neman shugabancin Majalisar Wakilai ba tukunna.
Na gaba-gaba a cikin masu neman mukamin, har da mataimakin shugaban majalisar wakilai mai ci, Ahmed Idris Wase daga shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Akwai kuma Yusuf Adamu Gagdi, shi ma daga shiyyar Arewa ta Tsakiya, duka sun fito ne daga jihar Filato.
Da Muktar Aliyu Betara daga jihar Borno, shiyyar Arewa maso Gabas ta zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Sai 'yan majalisa irinsu Alhassan Ado Doguwa daga Kano, shi ne shugaban masu rinjaye a yanzu kuma yana wakiltar Arewa maso Yamma, shiyya daya da dan majalisar da jam'iyyar APC ta marawa baya.











