Ƴaƴa maza ne suka fi kashe iyayensu mata - Rahoto

Asalin hoton, James Wakibia/SOPA Images/LightRocket via Getty Images
- Marubuci, Helen Richardson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC North East Investigations
- Lokacin karatu: Minti 5
Yara maza na kashe iyayensu mata fiye da baƙi, a cewar sabon rahoto daga wata ƙungiya da ke bincike kan tashin hankalin da ake yi wa mata.
Sabon rahoton alƙaluman yadda ake kashe mata ya nuna cewa daga cikin mata 121 da maza suka kashe a shekarar 2022, 12 ƴaƴansu maza ne suka kashe su, yayin da 11 kuwa ba su san mazan da suka kashe su ba.
Daraktar ƙungiyar, Dr Karen Ingala Smith, ta ce a duk wata uwa da ɗanta ya kashe, akwai "iyaye mata da dama da ke rayuwa tare da yaransu maza suna jure tashin hankali da cin zarafi mai tsanani."
Wata uwa daga Midlands ta ce tun ɗanta yana da shekara biyu kacal ya fara dukanta, kuma "akwai jami'an kula da al'umma da suke nuna cewa babu abin da za mu iya iya idan hakan na faruwa."
Matar mai shekaru 34 ta ce, "Ba haka aka tarbiyantar da mu ba. Ba mu san yadda za mu fita daga wannan matsalar ba."
Ta bayyana cewa iyalinta sun shafe shekaru biyu suna neman taimako daga hukumomi, har suka sanya kyamarar tsaro ta CCTV a gidan su saboda suna jin ba a saurare su.
Mijinta ya ce, "Mun sha suka saboda muna yawan kiran 'yan sanda."
Duk da kiran 'yan sanda sama da sau 60, ma'auratan sun ce kotu ta ƙi gurfanar da ɗansu mai lallurar da ke shafar ƙwaƙalwa ta autism saboda "ba shi cikin muradin jama'a."
Mijin matar ya ce, "Wannan tashin hankali ne na gaske—wasu lokuta yana kai wa ga matse mata wuya."
"Amma jami'an sun ce mana mu zauna mu kalli talabijin na awa ɗaya tare da shi, don nuna masa cewa har yanzu muna ƙaunar sa."
An kai yaron nasu gidan kula da yara a wannan shekara bayan wani lamari da mijin ya ce "ya yi tunanin zai kashe uwar yaron."
Ya ƙara da cewa, "Yaron ya faɗar da mahaifiyarsa a ƙasa, tana taka shi daga kai zuwa ƙafa."

Asalin hoton, PA Media
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bincike da ƙungiyar alƙaluman yadda ake kashe mata ta gudanar ya gano cewa mafi yawan mata da ake kashewa ana kashe su ne ta hannun abokin rayuwa da kaso 27 ko miji da kaso 24 ko tsohon abokin rayuwa da akso 10 ko kuma tsohon miji da kaso 1.
Mafi yawan sauran lokuta na tashin hankali sun shafi mata da yaransu maza suka kashe da kaso 12 ko mahaifansu da 1 kaso 1 cikin 100.
Binciken ya duba mazan da aka same su da laifin kashe mata da mazan da aka gano sun ɗauki alhakin mutuwar mata ta hanyar binciken kotu, da kuma mazan da ake zargi ko aka yi musu tuhuma a kan kisan mata a shari'o'in da ba a kammala ba.
Dr. Ingala Smith ta ce ƙungiyar tana "magance ƙaramin ɓangare ne kawai na matsalar," tana mai cewa akwai "lokuta da dama" na tashin hankali da ba su kai ga mutuwa ba amma ba ƙramin cin zarafin mata aka yi ba.
"Matan da suka fuskanci wannan cin zarafi na iya rashin gane shi a matsayin nau'in tashin hankali na gida, kuma suna iya tunanin cewa babu wani taimako da ake da shi da zai taimaka musu," in ji ta.

Asalin hoton, Supplied
Gwamnati ta ce za ta rage cin zarafi ga mata da 'yan mata da rabi a cikin shekaru goma masu zuwa.
Ministar kula da tsaro da kuma cin zarafin mata da 'yan mata, Jess Phillips, ta ce: girman matsalar ya kamata ta zama kamar dokar ta-ɓaci ta ƙasa
Ta ce: "Shi ya sa muka yi alƙawarin rage cin zarafin mata da 'yan mata a cikin shekaru goma, ciki har da yaki da cin zarafin iyaye da yara ke yi ta hanyar samar da tsari mai kyau da zai tabbatar da gano halayen da ba su dace ba da wuri, da kuma ganin an tallafa wa wadanda abin ya shafa domin a dakile halayen da ka iya ci gaba ko yin muni."
Haka kuma, gwamnati na da shirin inganta aikin 'yan sanda da tsarin shari'a wajen yaƙi da cin zarafin cikin gida "don tabbatar da cewa an fi kare waɗanda abin ya shafa, sannan kuma masu laifi su fuskanci hukunci."

Asalin hoton, Getty Images
'Kowanenmu na cikin tashin hankali'
Bayanan baya daga alƙaluman kisan mata sun nuna cewa matan da ƴaƴansu maza na riƙo suka kashe sun fi ƙaranci sosai idan aka kwatanta da waɗanda ƴaƴan da suka haifa suka kashe wato uku ne kacal idan aka kwatanta da 172.
Dr. Ingala Smith ta ce ba sa son rage darajar dangantakar uwa uba da ɗa, amma uwar da ta haifi ɗanta "takan kasance mutum da ke tsaya a bayan ɗant a kowane yanayi.."
Wasu iyalai da suka ɗauki yaran riƙo sun shaida wa BBC cewa suna fuskantar tashin hankali akai-akai, wasu ma suna ganin babu yadda za su yi sai dai su mayar da yaran zuwa kulawar gwamnati.
Wata uwa ta ce ana "dukanta, ana barazanar kashe ta da wuka," wata kuma ta ce "rayuwa ce cike da tsoro da firgici — fargabar da tsoran ɗanka, duk da cewa kina ƙaunarsa ƙwarai."
Wata uwa daga arewa maso gabashin Ingila, wadda ta ɗauki yarinya ta riƙo tun tana jaririya shekaru goma da suka wuce, ta ce yarinyar ta fara dukanta tun tana da shekara uku.
Cikin watanni shida, ta yanke shawarar ta daina amfani da wutar lantarki sannan ta fara boye wukaken gidan a ƙarƙashin katifa domin kare kanta daga yarinyar.
"Babu ɗaya daga cikinmu da ba ya cikin tsaro," in ji ta.

A halin yanzu, dokar Ingila ba ta ɗaukar cewa yara ƙasa da shekaru 16 na iya aikata cin zarafi a gida, duk da kira da ake yi a canza hakan.
Babu hukuma da ke da nauyin doka na taimaka wa iyalai, abin kuma ya bambanta a sassa daban-daban na ƙasar.
Masana da ma'aikatan zamantakewa sun ce ya fi dacewa a shawo kan matsala da wuri maimakon amfani da ƙarfi, amma binciken jami'ar Durham ya nuna yawanci sai an jira lamarin ya zama babba ake ɗaukar mataki.
Iyayen suna ta neman taimako tun daga lokacin da yaransu ke da shekaru huɗu, amma babu wani tallafi.
Uwar da ta ɗauki yarinyar riƙo ta yanke shawarar dakatar da ɗaukar nauyin yarinyar.
Ta ce: "Na kai ta makaranta, na ce mata sai anjima, amma na riga na yanke shawarar ba zan dawo ɗaukarta ba."
"Ina ba da komai na rayuwata don yarinya ta, amma hakan bai isa ba," in ji ta.







