Sau nawa ya kamata mu wanke baki a rana?

Wata mata tana goge bakinta

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Yasmin Rufo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Dukkan mu mun ɗauka cewa mun iya goge bakinmu - ana ganin cewa goge baki sau biyu da safe da kuma dare shi ne abin da ya fi dacewa.

Sai dai a cewar ƙwararru kan ɓangaren haƙori, sun ce mutum da ya kasance wanda ya fi goge baki zai iya yin kuskuren da zai shafi haƙorinsa.

Dakta Praveen Sharma, daga jami'ar birnin Birmingham, ya faɗa cewa manya na iya kamuwa da cutar dasashi a wani lokaci, kuma alamu na farko shi ne fitar jini a jikin haƙora.

"Idan tsakiyar haƙorinka suka fara fitar da jini, abu ne da ke nuna cewa kana goge baki yadda ya kamata," in ji shi.

Likitan ya bayyana kura-kurai huɗu da yawancinmu ke yi yayin goge baki, wanda kuma ya kamata a sauya domin inganta lafiyar haƙoranmu.

1. Goge baki sau ɗaya cikin tsanaki ya fi yi sau biyu a gaggauce

Likitocin haƙori da dama sun bayar da shawarar a riƙa goge baki sau biyu a kowace rana - kuma abu ne da hukumar inshorar lafiya ta Birtaniya, NHS ta bayar da shawara a kai.

Sai dai Dr Sharma ya ce abu mafi dacewa shi ne kula da haƙori yadda ya kamata ba wai yawan gobe baki ba.

"Idan kana da lokaci za ka iya yi sau biyu a rana," in ji shi. "Sai dai goge baki sau ɗaya a rana yadda ya kamata ya fi yin sa sau biyu a gaggauce.

Idan kana goge baki sau ɗaya a rana, ya fi dacewa ka goge da yamma kuma ka tabbata ka cire dukkan datti da ke cikin haƙora da duka wuraren da ɓurɓushin abinci zai iya maƙalewa wanda buroshi ba zai iya fitar wa ba.

Ya ce ya kamata a samu buroshi mai kyau wanda zai iya shiga cikin hakori sosai yayin wanke baki.

Dakta Sharma ya bayar da shawarar cewa mutane su riƙa kula da haƙoransu da kuma tsakiyarsu saboda nan ne ake samun cutar dasashi.

2. A fara wanke baki kafin karin kumallo

Mutane da dama na wanke bakinsu ne bayan sun yi karin kumallo, sai dai hakan bai dace ba.

"Abu mafi dacewa shi ne a yi buroshi kafin kari," a cewar Dakta Sharma.

"Idan ka gobe baki bayan ka ci abinci, to kana buƙatar ba da tazara tsakanin cin abinci da kuma yin buroshi."

Saboda sinadaran da ke cikin abinci da kuma ruwan lemu ko gahawa, yana sanyaya haƙori kuma wanke shi nan take zai shafi haƙori.

Dakta Chris ya ba da shawarar cewa a riƙa rintsa baki da ruwa bayan cin abinci don bai wa sinadarai damar fita da kuma jiran aƙalla mintuna 30 idan ana son yin buroshi.

3. Ka da a rintsa baki bayan buroshi

Idan ya kasance kana yawan rinsta baki bayan buroshi, ya kamata ka sauya tunani.

"Za ka iya rintsa man goge baki amma ban da ruwa," kamar yadda Dr Sharma ya ba da shawara a kai. Rintsa bakinka zai fitar da sauran abubuwan da suka maƙale a baki.

4. Bai kamata a riƙa amfani da man goge baki mai yawa ba

Dr Sharma, ya ce za a iya amfani da kowane irin man goge baki, in har yana ɗauke da sinadarai da ya kamata.

"Idan har ya kasance man goge bakin da kake amfani da shi yana da muhimman sinadarai, to ba shi da wata matsala," in ji likitan.

Sinadarin Fluoride yana taimakawa baki yadda ya kamata, musamma wajen cire datti.

Sai dai, likitan hakori da kake ziyarta zai iya ba ka shawara kan irin man goge baki da ya kamata ka yi amfani da shi, idan kana fama da cutar dasashi.

Wanke baki cikin tsanaki

Dr Sharma ya ƙara da cewa ya kamata a samu lokaci don wanke baki yadda ya kamata.

"Ba za ka so wanke baki yayin da kake yin wani wasu abubuwa ba," in ji shi.

Idan so samu, kana buƙatar tsayawa a gaban madubinka da kuma mayar da hankali.

Wasu mutane na ɗaukar lokaci wajen wanke ɓangaren su na hagu, wasu kuma ɓangaren dama - wanda zai iya yin cikas ga ɗayan ɓangare da ba a mayar da hankali a kai ba sosai.

A kula da hannun da ake amfani da shi wajen yin buroshi da kuma tabbatar da cewa an wanke duka ɓangarorin yadda kamata cikin tsanaki.