'Yantakarar da ke shirin maye gurbin Fafaroma Francis

Hoton ƴan takara.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴantakarar kujerar Fafaroma (Daga hagu zuwa dama) Cardinal Peter Kodwo Appiah Turkson, Cardinal Pietro Parolin, Cardinal Luis Antonio Gokim Tagle da kuma Cardinal Fridolin Ambongo Besungu
    • Marubuci, Aleem Maqbool
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Religion Editor
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shin wane ne zai zama sabon Fafaroma? Wannan zaɓe na iya yin gagarumin tasiri kan ɗaukacin cocin Katolika da kuma mabiyanta da suka kai biliyan 1.4 a duniya baki ɗaya.

Alamu kuma sun nuna cewa zai kasance zaɓen da ke cike da rashin tabbas saboda wasu dalilai da dama.

Kwamitin manyan limaman fadar Vatican za su yi kyallataccen zama na musamman a Cocin Sistine Chapel domin tafka mahawara da kuma kaɗa ƙuri'a domin zaɓen ɗantakaran da ya kwanta musu a rai, kuma ba za su fito ba har sai an samu wanda ya yi nasara.

Kasancewa kashi 80 cikin ɗari na limaman Fafaroma Francis ne ya naɗa su, wannan shi ne karo na farko da za su gudanar da zaɓen sabon Fafaroma.

A karon farko a tarihi, kusan rabin waɗanda za su yi zaɓen za su kasance ne daga nahiyar Turai.

Duk kuma da cewa akasarin waɗanda ke cikin kwamitin Fafaroma Francis ne ya naɗa su, hakan ba ya nufin cewa dukansu ne suka kasance masu ra'ayin ''sauyi'' ko kuma na ''gargajiya''.

Saboda waɗannan dalilai, yana da wuya a iya yin hasashen wanda za a zaɓa a matsayin sabon Fafaroma.

Ko za su iya zaɓar Fafaroma ɗan nahiyar Afirka ko Asiya, ko kuma za su iya fifita ɗaya daga cikin tsoffin hannun gwamnatin Vatican?

Ga dai jerin sunayen waɗanda ake ambata a matsayin waɗanda ake ganin daga cikin su ne za a zaɓi wanda zai gaji Francis, kuma muna sa ran samun ƙarin haske a cikin kwanaki masu zuwa.

Pietro Parolin

Ƙasarsa: Italiya

Shekarun haihuwa: 70

Pietro Parolin.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cardinal Parolin na Italiya shi ne sakataren harkokin wajen fadar Vatican ƙarƙashin Fafaroma Francis – wanda hakan ya sanya ya kasance babban mai bai wa Fafaroma shawara. Sakataren harkokin wajen kuma shi ne ke jagorantar 'Roman Curia', cibiyar gudanarwar cocin Katolika.

Sakamakon aikin da ya yi a matsayin mataimakin Paparoma, ana iya ɗaukarsa a matsayin wanda ya ke kan gaba cikin jerin ƴantakaran.

Wasu na ganin akwai yiwuwar zai ba da fifiko kan harkar diflomasiyya da kuma jefa cocin a al'amuran duniya fiye da dagewa kan zallar aƙidar cocin Katolika. Masu sukarsa na cewa wannan ra'ayi na iya janyo masa koma baya, yayin da magoya bayansa ke ganin hakan zai iya ƙara masa tagomashi a idon masu zaɓe.

Sai dai ya yi suka kan halasta auren jinsi a duniya, inda ya bayyana ƙuri'ar amincewa da aka kaɗa a jamhuriyar Ireland a shekarar 2015 a matsayin "rashin nasara ga bil'adama".

Masu hasashe sun karkata gare shi amma Cardinal Parolin zai yi la'akari da abin da masu iya magana a Italiya ke cewa kan rashin tabbas ɗin zaɓen fafaroma inda suka ce : ''Duk wanda ya shiga zaman halwar zaɓe yana tunanin shi ne Fafaroma, lallai zai fita a matsayin babban limami ne kawai''.

Cikin Fafaroma 266 da suka gabata, 213 sun kasance ƴan ƙasar Italiya, kuma ganin cewa an yi shekara 40 ba a zaɓi dan Italiya a matsayin fafaroma ba, kuma bisa la'akari da cewa akasarin shugabannin cocin ba ƴan Italiya ba ne, akwai yiwuwar wannan karon ma ɗan Italiya ba zai yi nasara ba.

Luis Antonio Gokim Tagle

Ƙasarsa: Philippines

Shekarun haihuwa: 67

Cardinal Luis Antonio Tagle.

Asalin hoton, Getty Images

Ko Cardinal Tagle zai iya zama Fafaroma na farko daga nahiyar Asiya? Shi dai ya fi Parolin samun sanin makamar aiki a matsayin Fasto - ma'ana ya daɗe a rukunin shugabannin cocin al'umma, a maimakon kasancewa jami'in diflomasiyya na fadar Vatican ko kuma masani kan dokokin coci.

Cocin Katolika na da matuƙar tasiri a ƙasar Philippines, inda kusan kashi 80 cikin ɗari na al'ummar ƙasar suka kasance mabiya ɗarikar ne. A halin yanzu ƙasar tana da mambobi biyar a cikin kwamitin limaman da ke gudanar da zaɓen fafaroma - wanda za su iya kasancewa wani ɓangare mai matuƙar ƙarfi idan har dukansu suka marawa Cardinal Tagle baya.

Ana yi masa ganin mai matsakaici ra'ayi, kuma an yi masa laƙabi da "Francis ɗin Asiya" saboda sadaukar da kai ga al'amuran zamantakewa da kuma nuna tausayi ga baƙin haure kamar yadda marigayi Paparoma ya yi.

Ya kasance mai adawa da haƙƙin zubar da ciki, lamarin da ya kira "wani nau'i na kisan kai" - matsayin da ya yi daidai da ra'ayin Ikilisiya na cewa rayuwar ɗan'adam ta fara ne daga ranar da aka ɗauki cikinsa.

Amma a shekarar 2015 lokacin da yake Archbishop na Manila, Cardinal Tagle ya yi kira ga Cocin ta sake duba ''tsatsaurar'' matsayin da ta ke da ita kan ƴan luwadi, da zaurawa da kuma iyaye mata marasa aure, yana mai cewa tsangwamar da ake yi musu a baya ya yi musu mummunar illa mai ɗorewa inda ya ce kowanne ɗan'adam ya cancanci a nuna masa tausayi da girmamawa.

Ya kasance ɗantakarar zama Fafaroma a zaɓen da aka yi a Shekara ta 2013, lokacin da aka zaɓi Francis.

Shekara 10 da suka gabata an tambaye shi yadda ya ke ganin kallon da ake yi masa a matsayin wanda zai iya zama Fafaroma, sai ya ce : ''Ina yi ma lamarin kallon abun dariya ne.''

Fridolin Ambongo Besungu

Ƙasarsa: Congo (DRC)

Shekarun haihuwa: 65

Cardinal Fridolin Ambongo.

Asalin hoton, AFP

Akwai yiwuwar cewa Fafaroma na gaba zai iya fitowa daga nahiyar Afirka, inda Cocin Katolika ke ci gaba da samun miliyoyin mabiya. Cardinal Ambongo ya kasance babban ɗantakara, wanda ya fito daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC).

Ya kasance Archbishop na Kinshasa na tsawon shekaru bakwai, kuma Fafaroma Francis ya naɗa shi a matsayin Cardinal.

Shi mai ra'ayin mazan jiya ne, inda ya ke adawa da auren jinsi guda, yana mai cewa "aure tsakanin masu jinsi ɗaya ya ci karo da ƙa'idojin al'adun mu, kuma babban aiki ne na assha".

Ko da yake addinin Kirista shine addini mafi rinjaye a DRC, Kiristocin da ke ƙasar sun fuskanci kisa da muzgunawa a hannun ƙungiyar IS mai da'awar jihadi da kuma ƙungiyoyin ƴantawaye. Bisa la'akari da wannan yanayi ana yi wa Cardinal Ambongo ganin babban mai kare muradun Coci.

Amma a cikin wata hira da aka yi da shi a shekarar 2020, ya yi magana game da bambancin addini, yana mai cewa: "A bar ƴan Protestant su zama ƴan protestant, Musulmai kuma su zama Musulmai. Za mu yi aiki tare da su. Amma kowa ya kiyaye addininsa."

Irin waɗannan kalaman na iya sa wasu manyan limaman cocin su yi tunanin bai yi cikakken amanna da maƙasudin aikinsu ba - inda cocin Katolika ke fatan yaɗa aƙidarta a duk faɗin duniya.

Peter Kodwo Appiah Turkson

Ƙasarsa: Ghana

Shekarun haihuwa: 76

Peter Turkson.

Asalin hoton, Reuters

Idan takwarorinsa suka zaɓe shi, Cardinal Turkson shi ma zai zama Fafaroma na farko daga nahiyar Afirka cikin tsawon shekaru 1,500.

Kamar Cardinal Ambongo, ya yi iƙirarin cewa ba ya son aikin shugabancin. "Ban tabbata ko wani yana burin zama Fafaroma ba," kamar yadda ya shaida wa BBC a 2013.

Da aka tambaye shi ko Afirka na da babbar muryar samar da Fafaroma na gaba bisa la'akari da ƙarin mabiyan da Cocin ke samu a nahiyar, ya ce yana ganin bai kamata a zaɓi Fafaroma bisa ƙididdiga ba, saboda "gudanar da lamarin a haka na iya janyo cece-ku-ce.''

Shi ne ɗan Ghana na farko da ya zama Cardinal, a shekara ta 2003 ƙarƙashin Fafaroma John Paul II.

Kamar Cardinal Tagle, Cardinal Turkson ya kasance ɗantakara shekara 10 da suka gabata, a lokacin da aka zaɓi Francis. Masu hasashe ma sun yi iƙirarin cewa shi ne a kan gaba kafin a kaɗa ƙuri'ar.

Makaɗin jita wanda ya taɓa yin wasa a ƙungiyar mawaƙan salon 'funk', Cardinal Turkson ya shahara ne saboda kuzarinsa.

Kamar yawancin limaman cocin da suka fito daga Afirka, ya karkata ne zuwa ɓangaren masu ra'ayin mazan jiya. Sai dai kuma ya nuna adawa da yadda ayyana luwaɗi a matsayin abbban laifi a ƙasashen Afirka ciki har da ƙasarsa ta Ghana.

A wata hira da BBC ta yi da shi a shekarar 2023, yayin da majalisar dokokin Ghana ke tattaunawa kan ƙudirin dokar hukunta masu neman jinsi, Turkson ya ce bai kamata a ɗauki luwadi a matsayin laifi ba.

A shekara ta 2012, an zarge shi da yin hasashen ban tsoro game da yaɗuwar addinin musulunci a nahiyar Turai a wani taron bishop-bishop na fadar Vatican, amma dai daga baya ya nemi afuwa.