Champions League: Arsenal za ta kara da PSG ranar Talata

Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal za ta karɓi bakuncin Paris St Germain ranar Talata a Champions League da za su fafata a Emirates.

Wasa na bibiyu kenan da kowacce za ta yi a kakar nan, inda Gunners ta fara da 0-0 da Atalanta a Italiya ranar 19 ga watan Satumba.

Ita kuwa PSG ta doke Girona 1-0 ranar 18 ga watan Satumba a Faransa, karon farko da Kylian Mbappe bai yi mata tamaula ba, wanda ya koma Real Madrid a bana.

Wannan shi ne wasa na biyar da za a kece raini a tsakaninsu, Inda Arsenal ta yi nasara ɗaya da canjaras uku a babbar gasar zakarun Turai.

Gunners za ta buga wasan da kwarin gwiwa, bayan da ta doke Leicester City 4-2 ranar Asabar a Premier League a Emirates.

Ranar Juma'a ne Paris St Germain ta yi nasara a kan Rennes da cin 3-1 a gida a Ligue 1.

Wasa da aka buga tsakanin Arsenal da PSG:

A kakar 2016/2017

Champions League ranar Laraba 23 ga watan Nuwambar 2016

  • Arsenal 2 - 2 Paris St-Germain

Champions League Tu 13Sep 2016

  • Paris St-Germain 1 - 1 Arsenal

A kakar 1993/1994

Euro Cup Winners Cup ranar Talata 12 ga watan Afirilun 1994

  • Arsenal 1 - 0 Paris St-Germain

Euro Cup Winners Cup Tu 29Mar 1994

  • Paris St-Germain 1 - 1 Arsenal

Wasannin Champions League da za a kara ranar Talata:

  • Red Bull Salzburg da Brest
  • Stuttgart da Sparta Prague
  • Arsenal da PSG
  • Barcelona da Young Boys
  • Bayer Leverkusen da AC Milan
  • Borussia Dortmund da Celtic
  • Inter Milan da Red Star Belgrade
  • PSV da Sporting
  • Slovan Bratislava da Manchester City