Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliya na haifar da cikas a harkokin koyo da koyarwar makarantu a Jigawa
A dumbin makarantun firamare na jihar Jigawa gwamnati ta tsugunnar da wadanda iftila'in ambaliyar ruwa ta shafa.
Kuma har yanzu wadannan mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu, na ci gaba da zama a makarantun duk da kasancewar dalibai sun koma makaranta.
Hukumomi sun ce akwai akalla mutum dubu goma sha biyar da ambaliyar ruwan ta tilastawa ficewa daga matsugunansu inda aka mayar da su makarantun gwamnati har arba'in da biyar.
Mutanen da ambaliyar ruwan ta raba da muhallansu sun kasance suna ci gaba da zama a gefe guda, yayin da dalibai kuma ke ci gaba da karatu a ɗayan gefen.
Makarantar firamaren garin Koye da ke karamar hukumar Miga a jihar, na ɗaya daga cikin makarantun da aka tsugunnar da mutane.
Mutanen da suka fake a cikinta sun shaida wa BBC cewa, haka suke zama cikin azuzuwa tare da kajinsu ga kazanta a ko ina.
Wani magidanci da BBC ta tattauna da shi a makarantar ya ce, a kullum sai sun share wajen da za su yada kafada saboda kazantar makarantar.
"An zo an bamu magunguna da sabulai don mu rika wanke hannayenmu saboda gudun kamuwa da cuta, sannan na bamu tallafin abinci, to amma duk da haka rayuwa muke ba cikin jin dadi ba sai da hakuri."
Muhammad Salisu, shi ne shugaban makarantar firamaren ta Koye, ya shaida wa BBC cewa, kasancewar akwai mutanen da ke zaune a makarantar da suke koyarwa sakamakon ambaliyar ruwa, suna koyarwa da dalibai a cikin matsi.
"Zaman mutane a makarantar na dauke wa dalibai hankali, maimakon su mayar da hankali sai kaga suna kallon mutanen da ke waje, alhali kuma ana koyar da darasi a aji, sannan azuzuwan ma duk an cika su da mutane ala tilas wasu daliban ma a waje muke koyar da su."
Ya ce, su na fuskantar barazana sosai don dalibansu ba sa mayar da hankali yadda ya kamata a yanzu a makarantar.
Gwamnatin jihar ta Jigawa, ta ce tana iyaka bakin kokarinta wajen magance wannan damuwa.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar, Dakta Mai Riga, ya shaida wa BBC cewa, cikin matsugunnan wucin gadi 45 da suka samar yanzu saura 30 saboda wasu sun fara komawa gidajensu.
Ya ce, "A yanzu kuma UNICEF sun bamu tantuna da zamu je mu daura a wadannan wurare saboda mutanen su samu su fita daga cikin azuzuwa don ba wa dalibai damar karatu kafin ruwa ya janye a gidajen nasu su koma."
Dakta Mai Riga, ya ce, "Zamu fara kafa tantunan daga Gwaram zuwa Jahun da kuma Miga."
Baya ga kasancewar mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu a wasu makarantun firamare a Jigawan, akwai kuma makarantu 28 da ruwa ya malale su har dalibai basa iya zuwa makaranta a sassan Jigawan.
Dangane da wannan matsala, kwamishinan ilimi a matakin farko na Jigawan, Dakta Yunusa Lawan Dan Zomo, ya ce sun yi tsarin da karatun yara ba zai tsaya ba duk da wannan matsala ta malale makarantun da ruwa ya yi.
"Duk inda ake da irin wannan matsala, to mu kan tura daliban da makarantunsu ruwa ya shafe su je makarantun da ke kusa da su su rika karatu amma da yamma, inda ainihin daliban makarantar da suka je kuma zasu rika karatu da safe."
Kwamishinan ya ce, idan babu makaranta a kusa da inda ruwa ya malale makarantar firamaren, mu kan ba wa masu garin shawara a samu wani waje ko gidan wani ko ofishi da za a rika koyawa yara karatu.
Ambaliyar ruwa a jihar Jigawa ta raba dubban mutane da muhallansu, sannan akwai mutum 30 da suka rasa rayukansu.
Kazalika ambaliyar ta lalata gonaki da dama, kuma duk da kokarin da hukumomi ke yi, akwai wuraren da wasu ke korafin rashin abinci da ruwan sha, abin da ke nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta yi hubbasa.