Brazil ta hana sayar da wayoyin iPhone marasa caja a kasar

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Brazil ta ce ta hana sayar da wayoyin iPhone wadanda ba su da caja a kasar.
Cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Shari’a a kasar ta fitar a ranar Talata, ta ce ta ci tarar kamfanin wayoyin fam miliyan 2.04.
Hukumar kula da hakkin masu sayen kayayyaki ta kasar ta ce matakin da kamfanin Apple - wanda ke kera wayoyin - ya dauka na rashin sayar da wayoyin tare da cajarsu ya ci karo da hakkin masu saya.
To amma kamfanin na Apple ya ce zai daukaka kara game da wannan matakin.
Kamfanin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zai yi aiki tare da mahukuntan kasar wajen warware matsalar, to amma ya kara da cewa a baya ya sha samun nasara a kotunan kasa a kan batun.
Kamfanin na Apple ya ce,” Muna da tabbacin cewa masu hulda da um sun san hanyoyin da suke bi wajen caja wayoyinsu.”
Gwamnatin ta Brazil ta dauki matakin hana sayar da wayoyin na iPhone marassa caja ne kwana guda kafin kamfanin na Apple ya gabatar da sabbin wayoyinsa ta iPhone 14 da 14 Pro da kuma Apple Watch Ultra.
A shekarar da ta wuce, hukumar kula da hakkin mai saye a São Paulo taci tarar kamfanin Apple £2m, yana mai cewa yadda aka sayar da iPhone 12 da sauran wayoyin da suka biyo bayanta sun saba da ka’idojin hukumar saboda wayoyin basa zuwa da caja.
Tun a 2020 ne bayan da kamfanin na Apple ya gabatar da iPhone 12, ya daina saka caja da hedifon a cikin sabbin kwalayen wayoyin.
Apple ya ce ya yi hakan ne da farko bayan ya daina amfani da adapton agogon Apple a cikin kwalinsa, kuma hakan ya taimaka wajen girman kwali.
Mataimakiyar shugaban da ke kula damanufofin kamfanin Lisa Jackson, ta ce a yanzu suna da adafto fiye da miliyan biyu da suka ajiye su waje guda.
Hukumar kula da hakkin mai saye ta Brazil din ta ce hujjar da kamfanin na Apple ya bayar a kan rashin sanya cajar bata gamsar ba.
Hukumar ta ce ba bu wata shaidar da ke nuna cewa cire cajar zai taimaka wajen kare muhalli daga gurbacewa.
A cewar ma’aikatar shari’ar kasar, hukumar kula da hakkin mai sayen ta ce yakamata kamfanin Apple ya duba wata hanya da zai ce za a bi wajen rage gurbatar muhalli maimakon haka kawai ya cire caja daga cikin kwalin waya.

Asalin hoton, Getty Images
A farkon shekarar 2022 ne, Kungiyar Tarayyar Turai ta amince cewa duk wasu kayan latironin da ba bu caja a ciki to ba su cika ba.
Hukumar ta ce sayar da wayoyin na iPhone ba tare da cajojinsu ba, misali ne tilastawa masu saye su kara kashe kudi don siyen caja.
Hukumar ta ce idan kuma har za a rinka sayar da wayoyin ba tare da cajojin ba, to sai kamfanin na Apple ya rage farashin wayoyin.











