Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da Bala Kaura ya ce kan rade-radin sauya shekarsa zuwa APC
Yayin da ake ci gaba da lissafa gwamnonin da suke sauya sheƙ zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ce yana nan a jamiyyarsa ta PDP daram.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Gwamnan ya musanta hakan ne a wata hira da BBC ta yi da shugaban jam'iyyarsa ta PDP a jihar Bauchi wanda ya yi magana da yawun gwamnan.
Pharmacist Sama'ila Adamu Burga, shugaban jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, ya ce jita-jita ce kawai.
"Da wa aka yi? kuma da wa gwamnan na Bauchi ya yi shawarar sauya shekar? to duk wannan jita-jitace kawai da soki burutsu," in ji shi.
A cewarsa, gwamnan Bauchi Bala Kaura ba zai taba kada kafa ba a kan layin da jam'iyyarsa ta PDP take ba "har sai mun ga abin da ya ture wa buzu nadi."
"Batun jita-jita, mu ma a shafukan sada zumunta muka gani ana ta yaɗawa, mu abin da muka sani shi ne babu wannan magana, kuma hakan ya taso ne daga wajen mutanen da ke adawa da gwamnatinmu a jihar Bauchi domin su tarwatsa mu." In ji shi.
Duk da rikicin cikin gida da jam'iyyar PDP ke fama da shi amma Shugaban jam'iyyar a jihar ta Bauchi, ya ce kansu a haɗe yake yana mai yi ikirarin cewa ana ƙoƙarin neman a razanar da magoya bayansu ne.
"Ina tabbatarwa mutanen Bauchi muna nan a jam'iyyar PDP, kuma kowa ya sani cewa gwamnanmu Bala Muhammed yana daga cikin wadanda ke a gaba-gaba wajen yin adawa saboda tsaftace dimokradiyya,"
"Kuma ba mamaki kila saboda yadda ake gani gwamnonin jam'iyyun hamayya musamman na PDP ke komawa APC , shi ya sa ake wannan hasashe."In ji Shi.
Pharmacist Sama'ila Adamu Burga, ya ƙara da cewa, " Idan ana ganin ko saboda jam'iyyarmu ta PDP na cikin wani rikici musamman na shugabanci shi ya sa gwamnan Bauchi ke son sauya sheka to ba haka ba ne, domin mu jam'iyyarmu ta PDP ba mu da matsalar cikin gida gwamnatin tarayya ce ke da matsala da mu."
A baya bayan nan dai akwai gwamnonin jam'iyyun hamayya a Najeriya da dama da suka koma jam'iyyar APC mai mulki inda yanzu take APC ke da gwamnoni 30.
Masana siyasa a Najeriya na ganin idan sauran gwamnonin hamayyar suka koma APC, to gwamnati za ta rinƙa abubuwa gaba-gaɗi ba tare da shakkar suka daga masu hamayya ba.