Gwamnoni nawa za su rage wa jam'iyyar PDP?

Lokacin karatu: Minti 3

Idan har rahotannin da ke yawo cewa gwamnonin jihohin Enugu da na Bayelsa, Peter Mbah da Sanata Douye Diri na shirin ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, suka tabbata to babbar jam'iyyar ta hamayya ka iya zama kyanwar Lami.

A wannan makon ne ake sa ran gwamnonin biyu za su sanar da sauya sheƙar tasu zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Bayanai sun nuna cewa jam'iyyar APC a jihar Enugu ta rushe Kwamitin Gudanarwarta a ranar Alhamis da ta gabata sannan aka kafa kwamitin riƙon ƙwarya duka a ƙoƙarin tarbar gwamna Mbah da jama'arsa.

A zaɓen shekarar 2023, jam'iyyar PDP ta samu nasarar lashe jihohi 9, ƙari a kan jiha ɗaya wato jihar Osun da aka gudanar da zaɓen jihar a 2022, abin da ya sa jam'iyyar ta PDP ke da gwamnoni 10 a faɗin ƙasar.

To sai dai kuma bayan zaɓen 2023 gwamnoni biyu wato na jihar Delta da Akwa Ibom, Sheriff Oborevwori da Pastor Umo Eno sun fice daga jam'iyyar, inda aka bar PDP da gwamnoni 8, ita kuma jam'iyyar APC ta zama tana da gwamnoni 23.

Wannan ya sanya APC ke da gwamnoni uku daga cikin shida a shiyyar Kudu maso kudancin Najeriya, yankin da a baya jam'iyyar PDP ke da ƙarfi cikinsa tsawon shekara 20.

Idan raɗe-raɗin da ake yi cewa gwamnoni biyu na jihohin Enugu da Bayelsa zu ma za su sauya sheƙar zuwa APC, to hakan na nufin yawan jihohin da PDP ke iko da su za su zama guda shida ne kawai.

Gwamnonin PDP bayan zaɓen 2023

  • Ahmadu Umaru Fintiri: Adamawa
  • Bala Muhamamd: Bauchi
  • Douye Diri: Bayelsa
  • Peter Mbah: Enugu
  • Ademola Adeleke: Osun
  • Seyi Makinde: Oyo
  • Caleb Mufwang: Plateau
  • Siminalyi Fubara: Rivers
  • Agbu Kefas: Taraba
  • Dauda Lawal: Zamfara

Gwamnonin PDP da suka koma APC

  • Pastor Umo Eno: Akwai Ibom
  • Sheriff Oborevwori: Delta

Illar sauya sheƙar gwamnonin PDP zuwa APC

"Tabbas, PDP na neman ta rasa ƙarfinta a Najeriya duba da yanayin yadda jihohin da jam'iyyar ta mallaka a 2015 da kuma yadda suke yanzu," in ji Lekan Ige, masani a fannin siyasa, a wata hira da BBC.

"Akwai wani lokaci a wannan ƙasa da PDP ta shugabanci ɓangaren zartarwa da kuma majalisar tarayya, amma yanzu ta zama jam'iyyar adawa. Saboda haka ta bayyana ƙarara cewa PDP ta rasa ƙarfin ikonta a Najeriya." In ji Ige.

Har wa yau, masanin ya ƙara da bayanin cewa " babbar illar sauya sheƙar ƴan PDP zuwa jam'iyya mulki shi ne yadda abin ke faruwa a daidai lokacin da ya kamata su haɗe kansu su tunkari APC."

"Amma yanzu a yadda ake tafiya da wuya jam'iyyar ta iya taɓuka wani abin arziƙi a kakar zaɓe mai zuwa ta 2027. Abin da ke nuna ƙarara cewa jam'iyyar ta durƙushe."

Wace illa sauya sheƙar zai yi ga ƴan Najeriya?

Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano, CAS, ya ce babbar illar da durƙushewar jam'iyyar adawa ta PDP za ta yi ga al'ummar ƙasa ita ce:

"Za a kai lokacin da babu wata jam'iyya mai hamayya mai ƙarfi da za ta rinƙa taka wa jam'iyya mai mulki burki dangane da daidai ko rashin dai-dai."

Gwamnati za ta rinƙa abubuwa gabagaɗi ba tare da shakkar suka daga masu hamayya ba. Misali, mun ga yadda gwamnatin nan ta fasa zaratar da shirye-shirye da dama sakamakon caccakar da jam'iyyun hamayya ke yi kan batutuwa." In ji Malam Kabiru.

Shi ma Akinola Ayobami, wani masani a fanni siyasa a birnin Legas ya bayyana cewa wannan salo yana da haÉ—ari ga makomar siyasar Najeriya.

A cewarsa, wannan tsarin jam'iyya ɗaya na nufin jam'iyya daya ce ke riƙe da mulki, babu wata dama da aka bai wa jam'iyyun adawa su bayyana ra'ayinsu ko ƙalubalantar gwamnatin da ke mulki.

"Idan aka kalli yadda siyasar Najeriya ke tafiya a yanzu, kamar muna tunkarar tsarin jam'iyya ɗaya ne. Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya saba da irin wannan salon a lokacin da ya ke gwamnan Jihar Legas, kuma kamar yana ƙoƙarin amfani da wannan dabarar a matakin tarayya," in ji Ayobami.