Mutum huɗu da za su iya amfana da karɓa-karɓar PDP a 2027

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

A kodayaushe akwai mai nasara da wanda ya sha kaye a tsarin kowace irin siyasa, kuma tuni matakin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ware wa yankin kudancin ƙasar kujerar takarar shugaban ƙasa ya fara nuna hakan tun kafin a je ko'ina.

A farkon makon nan ne jam'iyyar ta sanar da matakin, wanda ke nufin ɗantakararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027 zai fito ne daga yankunan siyasa na kudu maso yamma, da kudu maso gabas, da kudu maso kudu (Neja-Dalta).

Duk da cewa matakin ya zo wa ɗaiɗaikun 'yan ƙasar da bazata, sai dai tuni lissafin waɗanda abin ya shafa ya sauya yayin da ya rage ƙasa da shekara biyu a gudanar da zaɓen.

Matakin PDP, wadda ta shafe kusan shekara uku tana cikin rikici, na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa jagororinta sun amince su bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan takara.

Daga cikin muhimman matsayar da kwamatin gudanarwa na jam'iyar ya ɗauka a taron da ya gudanar ranar Litinin har da cewa shekara huɗu mulkin zai yi a kudanci kafin ya koma arewaci.

Kazalika, shugaban jam'iyyar na riƙo Iliya Damagun ya shaida wa BBC cewa duk muƙaman da ke arewaci, shugaban jam'iyyar, zai ci gaba da zama a Arewan, na Kudu ma su ci gaba da zama a Kudun.

Tsarin karɓa-karɓa na ɗaya daga cikin abubuwan da aka san PDP da shi tsawon shekara 16 da ta yi tana mulkin Najeriya, inda ta dinga rarraba kujeru tsakanin yankunan biyu.

Su wane ne wannan matakin zai fi amfana? Su wane ne burinsu ba zai cika ba saboda matakin? Wannan maƙala ta yi duba kan tasirin da zai yi a siyasar wasu 'yansiyar jam'iyyar.

Goodluck Jonathan

Goodluck Ebele Jonathan mai shekara 67 ba baƙo ba ne a siyasar Najeriya tun bayan da ya zama shugaban ƙasa a 2010 sakamakon mutuwar maigidansa Umaru Yar'Adua a jam'iyyar ta PDP.

Ɗan asalin jihar Bayelsa da ke kudu maso kudu, Jonathan ya ɗan ja baya daga harkokin siyasa, inda har aka dinga raɗe-raɗin zai fice daga jam'iyyar.

Sai dai a watan Yulin da ya gabata PDP ta tabbatar wa BBC cewa ta neme shi ya tsaya mata takarar shugaban ƙasa, tana mai cewa ya amince amma bisa wasu sharuɗɗa.

Masu nazarin harkokin siyasa na ganin Jonathan na cikin na gaba-gaba da wannan mataki na PDP zai fi amfana idan har ya amince da yin takarar, kodayake an ce daga cikin sharaɗin da ya kafa shi ne ba shi tikitin takarar ba tare da hamayya ba.

Ɗan kwamatin amintattu na PDP Farfesa Ibrahim Tsauri ya ce farin jinin Jonathan ne ya sa suke neman ya tsaya musu takara.

"Kowa ya san Goodluck shi ne ya yarda ya faɗi zaɓe, wannan abin ya ƙara masa kima a idanun 'yan Najeriya da duniya baki ɗaya. Duk ɗan Arewa da ya zaɓi Tinubu ya zaɓe shi ne saboda Kashim Shettima, saboda haka muna sa ran ƙuri'un Arewa za su koma wajen Goodluck Jonathan," in ji shi.

Seyi Makinde

Gwamnan jihar Oyo mai-ci, ana yi wa Seyi Makinde kallon ɗaya daga cikin mutanen da ke harin takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP.

Makinde mai shekara 57 zai kammala wa'adi na biyu a matsayin gwamna nan da 2027 bayan zaɓarsa a 2019.

Yana cikin gwamnonin PDP da Ministan Abuja Nyesom Wike ke rigimar iko da su kasancewarsa gwamna ɗaya tilo daga yankin kudu maso yamma da ƙabilar Yarabawa suka fi rinjaye - kuma yankin da Shugaba Bola Tinubu ya fito.

Shawarar keɓe wa kudanci takara za ta amfani da Makinde sosai idan ya yanke shawarar gwada sa'arsa a 2027.

Peter Obi

Tsogon gwamna kuma tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party, Peter Obi na cikin 'yansiyasar adawa da suka ɗunguma zuwa jam'iyar ADC ta haɗaka.

Duk da cewa ya bar PDP tun kafin zaɓen 2023, wasu 'ya'yan jam'iyyar na neman ya koma cikinsu domin ya yi mata takara ko don ganin yadda ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Obi ya taɓa yin takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2019, lokacin da ya tsaya tare da Atiku Abubakar, amma a yanzu ya ci alwashin ba zai sake yi wa wani mataimaki ba, yana mai cewa wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi idan ya yi nasara.

Mai shekara 64, Obi ya fito ne daga jihar Anambra da ke kudu maso gabas, inda ƙabilar Igbo ta fi rinjaye, kuma ya yi gwamnan jihar na wa'adi biyu tsakanin 2006 zuwa 2014.

Masu neman Obi ya koma PDP domin yin takara za su samu ƙwarin gwiwar ci gaba da yunƙurinsu saboda wannan mataki na miƙa takarar zuwa kudanci.

Nyesom Wike

Ana iya cewa tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ya fi shahara a siyasar Najeriya ne tun bayan da ya saka zare tsakaninsa da shugabancin jam'iyyar PDP gabanin zaɓen 2023.

Tun daga lokacin ne yake kokawar neman iko da shugabannin jam'iyyar da ba su bin tafiyarsa, yayin da kuma yake ci gaba da riƙe muƙaminsa a gwamnatin Bola Tinubu ta jam'iyyar APC.

Babu tabbas ko har yanzu yana da sha'awar sake neman takara a PDP, amma idan bai haƙura ba to yanzu zai samu ƙwarin gwiwar shiga takarar kai-tsaye.

A gefe guda kuma, Wike ya lashi takobin kawo wa babbar taron jam'iyyar na ƙasa cikas wanda ta shirya yi ranar 15 ga watan Nuwamba.

'Yansiyar da burinsu ba zai cika ba a PDP

Bala Mohammed

Tun kafin yanzu, an daɗe ana yi wa Gwamnan Bauchi Bala Mohammed kallon ɗaya daga cikin masu son yin takarar shugaban ƙasa a 2027.

Gwamnan mai shekara 66 na cikin wa'adinsa na biyu, kuma ya taɓa bayyana cewa ba zai taɓa jayayya da Goodluck Jonathan ba a wajen neman takara. Shi ne ministan Abuja a lokacin mulkin Jonathan ɗin daga 2010 zuwa 2015.

Wasu masu bin siyasar gwamnan na ganin wannan matakin zai taimaka masa idan ya yanke shawarar zama mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin tsohon mai gidan nasa.

Gwamnan na da damar gadar Jonathan a 2031 - lokacin da zai kammala wa'adinsa na shekara huɗu bayan marigayi Muhammadu Buhari na APC ya katse wa'adin mulkinsa bayan shekara huɗu a 2015.

Aminu Tambuwal

Tsohon gwamnan Sokoto kuma sanata a yanzu, Aminu Waziri Tambuwal na cikin 'yan jam'iyyar haɗaka ta ADC, wanda ya ce ba zai bar PDP ba.

Yana ɗaya daga cikin 'yansiyasar da suka nemi takarar shugaban ƙasa a PDP a zaɓen 2023, amma ya janye wa Atiku Abubakar kafin fara kaɗa ƙuri'a, abin da ya zama mafarin rikicinsa da Nyesom Wike.

Babu tabbas ko yana da sha'awar neman takara a jam'iyyar haɗaka ta ADC, amma tabbas wannan mataki na PDP ya kawo ƙarshen burinsa na neman shugaban ƙasa a jam'iyar idan yana da shi.