Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ministocin Birtaniya biyu sun yi murabus
Manyan ministocin Birtaniya biyu sun yi murabus sakamakon ce-ce-ku-cen da ake yi kan Firaiminista Boris Johnson.
Ministan kuɗi Rishi Sunak da Ministan Lafiya Sajid Javed duka sun bayar da takardar ajiye aikinsu - lamarin ya jawo matsin lamba matuƙa kan Firaiminista Boris Johnson.
Ana zargin Boris Johnson da yin kalamai da dama masu cin karo da juna. Ko a kwanakin baya sai da aka yi ƙuri'ar raba gardama kan Mista Johnson ɗin.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ministan lafiya Sajid Javed ya wallafa takardar ajiye aikinsa inda ya ce ya yi magana da faraiminista domin ya yi murabus.
"Ba ƙaramar dama na samu ba da na riƙe wannan muƙamin, amma ina baƙin cikin sanar da cewa ba zan iya ci gaba ba," in ji Mista Javed.
Shi ma ministan kuɗi Rishi Sunak a takardar da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa jama'a na son su ga an tafiyar da al'amuran gwamnati da kyau kuma an ɗauke su da muhimmanci.
"Ina ganin wannan ne aiki na ƙarshe da zan yi a matsayina na minista, amma ina ganin waɗannan abubuwan sun cancanci a yi yaƙi saboda da su wanda hakan ya sa zan yi murabus," in ji Mista Sunak.