Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran

Asalin hoton, IHRights
Mohsen Shekari mai shekaru 23, shi ne mai zanga-zanga na farko a Iran da aka rataye. Kwana huɗu bayan haka, a ranar 12 ga Disamba aka rataye wani matashi Majidreza Rahnavard a bainar jama'a a yankin Mashhad bisa zargin kaifin kishin addini.
Dukkansu, wata kotun juyin juya hali ce a Moharebeh ta same su da laifin "kiyayya ga Allah".
A dokar Iran, ana bayyana laifin da haifar da "rashin tsaro a tsakain al'umma" ta hanayar barazana ga rayuwarsu ko dukiyarsu da makami.
Hukumomin Iran sun matsa wa iyalan 'yan siyasa da ke tsare da kar su yi magana da yan jarida, don haka zai yi wuya a samu hotunan wasu daga cikin mazan da aka yanke wa hukuncin kisa a Iran.
Ga kadan daga cikin abin da muka sani game da wadanda aka yanke wa hukunci, ko kuma wadanda za a iya yanke musu hukuci a kowane lokaci.
Mohsen Shekari

Asalin hoton, IHRights
"Mohsen ya yi aiki a wajen siyar da shayin Gahawa" yana yawan magana kan wasan bidiyo wato Video Game da shayin gahawa," kamar yadda Babak Aghebati ya rubuta, ya ce ya shafe shekaru 20 tare da Shekari a gidan yari.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, tsohon fursunan ya ce Shekari mutum ne mai tausayi da kulawa, kuma ya kadu matuka da samun labarin hukucin da aka yanke masa.
Majidreza Rahnavard

Asalin hoton, IHRights
Iyalan Majidreza sun ce suna sa ran za'a sake shi.
A wani bidiyo da kafar talabijin ta Iran ta nuna, an nuno shi fuskarsa a rufe kuma hannunsa a karye.
Bidiyon ya nuna tsarin da ake bi na turasasa wa masu zanga-zanga amsa laifuka.
Majidreza, cikin kaduwa, bai musanta kai hari kan daya daga cikin 'yan majalisa da wuka ba, amma sai dai ya kafe cewar "ba ya cikin hayyacinsa".
An zartar masa da hukunci kwana 23 da tsare shi.
Ko me muka sani dangane da sauran suma da wata kila su iya gamuwa da makamanciyar irin wannan kaddara?
Babu wani tsayayen adadi daga hukumomin kasar, amma akwai 'yan Iran da aka yankewa hukucin kisa, a cewae kungiyoyin kare hakkin dan adam.
Sun ce wadan da ake kara baza su iya daukar lauyoyi ba, kuma gwamnati na basu lauyoyin da bas kare su yadda ya kama. ana shari'ar cikin kankanin lokaci, ksannan ana tunanin cewar ana samun bayyanai ne ta hanayr azabtar da wadn ake zargi, da cin zarafin iyalansu, da alkawarin yi musu hukunci mai sassauci.
Sahand Noormohammadzadeh

Asalin hoton, IHRights
Sahand mai shekara 26, an yanke masa hukucin kisa bayan an same shi da laifin nuna "kiyayya ga Allah".
An zarge shi da cinna wa kwandon zuba shara wuta, da tare hanya, zarge-zargen da ya musanta.
A wani sautin murya da muka samu daga Sashen BBC Persian, wadanda suka tsare shi, da wadanda suka yi masa tambayoyi, da lauyansa daga baya sun sanar da shi cewar irin hukuncin da aka yanke masa.
Ya ce an yanke hukuci kan makomarsa tun kafin ma a gurfar da shi a gaban shari'a.
"Ina shiga ofishin lauya mai shigar da ƙara ya ce da ni ga shi nan an rubuta a goshi na: hukuncin! A rataye shi!"
Sahand ya zama abin tsokan kan hukucin da aka yanke masa a zaman sa na gida yari.
"Sun kira ni suna sanar da ni lokacin da za'a yanke mun hukunci ya zo" yana fada a cikin sautin muryar, yana mai cewar yana cikin matsancin matsi a cikin kwakwalwarsa.
Hamid Ghare-Hasanlou

Asalin hoton, IHRights
Hamid Ghare-Hasanlou, ma'aikacin asibiti da ke aiki a sashen daukar hoton sassan jikin dan Adam, yana da shekara 53 da matar sa Farzaneh.
Yana daga cikin mutum 15 da aka same su da laifin "cin hanci", wani zargi da ke da alaka da kashe daya daga cikin dakaraun Basij.
Ma'auratan na kan hayarsu ta komawa gida daga zanga-zanga a Karaj, kusa da Tehran, inda suka ga lokacin da aka kai hari kan daya daga cikin yan Basij.
Wani abokin Dr Hamid mai suna Hassani ya fada wa BBC Persa cewa sun so su hana masu zanga-zangar da ke dukan mutumin da ya mutu a sakamakon harin.
"Hamid ya kuma ceci wani malamin addini da aka raunta a ranar," a cewar Dr Hussani.
An kama ma'auratan a wani kame da misalin kafe 2:00 a kan idon 'yarsu mai shekara 13, wadda suka yi wa barazana kan kar ta ce komai game da kamen da suka yi wa iyayenta.
Saman Yasin

Asalin hoton, IHRights
Mawakin Gambara na Iran da ya fito daga yammaicn birnin Kermanshah, shi ma an yanke masa hukucin kisa bayan samun sa da laifin "kiyayya ga Allah".
An kama shi a Teheran kan zargin cinna wa wani kwandon shara wuta, da harba bindiga har sau uku, zargin da ya musanta.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Kurdistan ta ce an azabtar da Yasin Seyedi: "aka ajiye shi a wani tudu mai tsayi, sannan aka lakada masa duka".
A wani faifan bidiyo da aka fitar ranar Alhamis, mahaifiyarsa ta roki Iraniyawa da kasashen ketare su ceci rayuwar danta.
"A wace duniya ce haka ake daukar ran wani don kawai ya cinna wa kwandon shara wuta?" in ji ta tana mai neman taimakon mutane su agaza wa danta tun kafin "a saka igiya a wuyansa".
Mahan Sedarat Marani

Asalin hoton, IHRights
Iyalan Mahan sun ce suna tunain za a aiwatar da hukucin da aka yi masa a kowane lokaci.
"Shari'a ce ta siyasa, kuma ban san me za mu iya yi ba. An mayar da shari'arsa hukucin kisa, " kamar yadda mahifinsa ya shida wa jaridar Iran ta Shargh Daily.
Mahan ya amsa cinna wa wani babur wuta. Wani daga cikin masu kara sun zarge shi da yin haka, da amfani da wuka wanda daga baya aka janye korafin.
"Kar ki damu sanyin raina. Yi hakuri nan da wasu 'yan makoni zan fito," yana mai fada wa budurwarsa a wani sautin murya da aka wallafa a dandalin sada zumunta.











