Na'urar hangen nesa ta zaƙulo keɓantattun hotunan duniyar Jupiter

.

Asalin hoton, NASA/ESA/CSA/JUPITER ERS TEAM/JUDY SCHMIDT

Bayanan hoto, An samu wannan hoton duniyar Jupiter daga hotuna da dama da aka ɗauka da na'urar telescope

Na'urar hangen nesa mafi girma da ƙarfi a duniya ta gano wasu hotunan duniyar Jupiter da ba a taɓa ganin irinsu ba.

Na'urar hangen nesa ta James Webb ce ta ɗauki hotunan duniyar mafi girma cikin watan Yuli.

Hotunan sun nuna daki-daki yadda haske da guguwa da wata da kuma zobe suka kewaye duniyar Jupiter wani abu da masu ilimin taurari suka ce abin mamaki ne.

An ƙara wa hotunan da aka ɗauka da fasahar hasken infrared launi domin a ƙara fito da fasalin duniyar. An yi haka ne saboda ido ba ya iya ganin abubuwan da fasahar za ta iya gani.

"Ba mu taɓa ganin Jupiter haka ba. Abin da ban mamaki," in ji wata mai ilimin taurari Imke de Pater ta Jami'ar California wanda ya taka muhimmiyar rawa a aikin. "Ba mu yi tunanin hotunan za su fito da kyau ba, maganar gaskiya," in ji ta.

Na'urar ta JWST da kuɗinta ya kai $10bn (kwatankwacin £8.5bn), wani shiri ne da Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (Nasa) haɗin gwiwa da takwarorinta na Turai da Canada.

Wasu labaran masu alaƙa

Nasa ta ce a hoton na Jupiter, wanda aka yi shi daga tarin hotunan da aka ɗauka daga na'urar hangen nesa, haske ya ratsa ta saman kusurwar Arewaci da Kudancin duniyar Jupiter.

Hasken Aurora haske ne a sararin samaniya da rana ke haifar da shi. Sannan ƙatuwar guguwa ta the Great Red Spot da ke iya laƙume duniya, ta bayyana fara.

Hakan ya faru ne sakamakon tana kallon rana sosai. An harba na'urar ta JWST a Disambar 2021 kuma zuwa yanzu ta yi nisan mil miliyan daya (kimanin taki miliyan 1.6) daga duniya. Tana iya gano haske da ya fara tunkarar duniya shekara biliyan 13, lokaci kaɗan bayan babbar fashewar nan ta Big Bang.

Ana sa rai JWST, wadda ake kallo a matsayin wadda ta maye gurbin na'urar hangen nesa ta Hubble, za ta zama babbar na'urar gano abubuwa a sararin samaniya zuwa nan da shekaru 20 masu zuwa.