Akwai alamun komawa tattauna yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza

Asalin hoton, JACK GUEZ/AFP via Getty Images
- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
Firaministan Israʼila Benjamin Netanyahu ya nuna alamun cewa ƙoƙarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza ya karkata kan matsayar da za ta kai ga sakin dukkanin mutanen da ke riƙe a zirin lokaci guda.
Yarjejeniyar tsagaita wutar da ake son samarwa ta kwana 60 da farko da sakin wasu daga cikin mutanen da ake riƙe da su.
Hamas ta ce wata tawagar shugabanninta na birnin Cairo don "tattaunawar farko" da jamiʼan Masar.
Rahotanni sun ce masu shiga tsakani na ganin wata dama cikin makonni masu zuwa na cimma matsaya.
Bayan tattaunawar da ba ta kai tsaye ba da aka yi tsakanin Israʼila da Hamas ta karye a watan da ya wuce, Israʼila ta sanar da wani shiri mai cike da ruɗani na bunƙasa yaƙinta na soji da kuma mamaye gaba ɗaya Zirin Gaza - ciki har da wuraren da yawancin Falasɗinawa ke neman mafaka.
Sai dai, kafofin yaɗa labaran Israʼila ba sa tsammanin soma wata sabuwar mamaya sai watan Oktoba - wanda zai ba da lokacin a yi shirye-shiryen soji, ciki har da kiran sojoji masu jiran ko ta kwana masu yawa.
A gefe guda kuma, Israʼila ta ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza, kuma Maʼaikatar lafiya ta Gaza ta ce an kashe aƙalla Falasɗinawa 123 a ranar Talata.
Shaidu sun ce Israʼila ta zafafa hare-hare a birnin Gaza, musamman harin soji da ke lalata gidaje.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bidiyo ya nuna fashewa mai girma da hare-hare suka janyo rugujewar gine-ginw a unguwar Zaytoun da ke gabashin birnin Gaza.
Da safiyar Laraba, asibitin al-Shifa ya ce an kashe mutum bakwai ƴan gida ɗaya, inda biyar daga cikinsu yara ne aka kashe a wani tanti a Tel al-Hawa da ke kudancin birnin.
Asibitin Al-Ahli ya ce an kashe mutum 10 a wani hari da aka kai wani gida a unguwar Zaytoun.
Rundunar sojin Israʼila ta ce ta fara sabbin ayyuka a Zaytoun.
Babban hafsan sojin Israʼila ya kuma "amince da babban tsarin aikin rundunar ta IDF a Zirin Gaza."
A wata tattaunawa da gidan talbijin na i24News da ke Israʼila, an tambayi Netanyahu idan za a iya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.
"Ina ganin mun wuce nan," ya ce. "Mun gwada, mun yi duk wani ƙoƙari, mun sha wahala, amma sai muka gano yaudararmu suke."
"Ina so su saki duka mutanen mu dake hannusu masu rai da gawarwakin wadanda suka mutu, wannan shi ne abin da muke so,'' in ji shi.
Har yanzu ƙungiyoyin Falasdinawa masu ɗauke da makamai na riƙe da ISra'ila 50 da suka yi garkuwa da su a harin ranar 7 ga watan Otoban 2023 da Hamas ta jagoranta.
Kuma Isra'ila ta yi amanna cewa akwai kusan 20 daga cikinsu da har yanzu ke da rai.
Netanyahu na shan matsin lamba a cikin gida domin tabbatar da sakinsu da kuma shirinsa na faɗaɗa yaƙin.
A mkon da ya gabata ne dai aka ambato wasu jami'an Larabawa da ba a ambaci sunansu ba na cewa masu shiga tsakani a yankin Masar da Qatar na ƙoƙarin shirya yadda za a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta domin sakin duka Isra'ilawan da ke hannun Hamas.
To sai dai ana ganin tattauanwar ka iya kawo tsaiko akamakon muradin Isra'ila na karɓe ikon Gaza daga hannu Hamas da kuma makaman ƙungiyar.
Masu shiga takanin dai na son a koma daftarin yarjejeniyar na farko na dakatar da wuta ta kwana 60 da sakin wasu daga cikin Isra'ilawan da ke tsare a hannun Hamas, da bayar da damar shigar da agaji Gaza ba tare da matsala ba, kamar yadda ministan harkokin wajen Masar ya bayyana.
Shi kuwa firaministan Isra'ila ya ce manufar Isra'ila game da yaƙin ba za ta sauya ba, yana mai cewa za a kawo ƙarshen yaƙin ne kawai idan an saki duka Isra'ilawan da ake garkuwa da su, sannan Hamas ta miƙa makamanta.
Ya ƙara da cewa dole ne Isra'ila ta samu ikon tsaron ilahirin Gaz

Asalin hoton, BASHAR TALEB/AFP via Getty Images
Hamas ta jima tana kiran yin musayar fursunoni da Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.
Haka kuma ƙungiyar na buƙatar janyewar duka sojojin Isra'ila daga Gaza domin akwo ƙarshen yaƙin.
Ya kuma ce ba za ta amince da ajiye makamanta ba har sai an samar da ƴancin ƙasar Falasɗinawa.
Yayin hirarsa da kafar yaɗa labarai ta i24News, Netanyahu ya jaddada ƙudirin cewa dole ne Falasɗinawa su fice daga Gaza bisa ''raɗin kansu'' su yi hijira, yana mai cewa ba tilasta musu ficewa za a yi am, amma za a ba su damar ficewa da kansu.
''Muna son yin hakan ne domin bai waɗanda ke iƙirarin son taimaka wa Falasɗinawa damar yin hakan'', in ji shi.
Sai dai Falasɗinawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama na gargaɗin cewa tilasta wa Falasɗinawa ficewa daga yankunansu ya saɓa wa dokokin duniya.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗin samun mummunar yunwar da ba a taɓa gani ba a Gaza tun bayan fara yaƙin.
Harin Hamas na Oktoban 2023 ya kashe mutum 1,200 a Isra'ila tare da yin garkuwa da mutum 251 a Gaza.
Yayin da hare-haren Isra'ila suka kashe Falasɗinawa 61,722, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas.
Haka kuma hukumar ta ce mutum 235 ne suka mutu saboda yunwa, ciki har da ƙananan yara 106.

Asalin hoton, ABIR SULTAN/POOL/AFP via Getty Images










