An yi jana'izar mutum 10 da ƴar ƙunar baƙin wake ta kashe a jihar Borno

Lokacin karatu: Minti 1

Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da harin da wata ƴar ƙunar bakin wake ta kai a babbar kasuwar kifi da ke Konduga, inda ta ce aƙalla mutum 10 sun mutu, duk da wata majiya ta ce aƙalla mutum 20 ne suka mutu, ciki har da ƴan sa-kai da suke taimakon sojoji wajen yaƙin da ƴan ƙungiyar.

A daren Juma'a na 20 ga Yuni, 2025 ne rahotani suka nuna cewa wata ƴar ƙunar bakin waken ta kai harin a garin na Konduga, wanda ke kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Da yake magana game da harin, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya yi Allah wadai da harin, sannan ya yi kira ga jami'an tsaro su ɗauki matakin gaggawa.

An ga wasu hotuna da aka jera gawarwakin waɗanda harin ya rutsa da su a lokacin da ake shirin yi musu jana'iza a ranar Asabar.

A cikin ƴan watannin nan, Boko Haram sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan jihar Borno, inda suka kahe gomman mutane, suka jikkata wasu, sannan wasu da dama suka bar ƙauyukansu domin samun mafaka.

Kimanin shekara goma da suka gabata, yankuna da dama sun kashe a ƙarƙashin ikon mayaƙan na Boko Haram, kafin sojojin Najeriya suka ƙwato su, wanda hakan ya sa ƴan gudun hijira suka bar sansanoni suka koma gidajensu.

Sai dai ƙaruwar sababbin hare-haren mayaƙan na ƴan watannin na jefa fargaba a zukatan mutane waɗanda suka tsoron hannun agogo na iya koma baya, wanda har gwamnatin jihar Borno ta buƙaci a ƙara wa sojojin ƙasar ƙarfin gwiwa domin su cigaba da aikin da ke gabansu.