Man United na kokawar ɗaukar Anderson, Arsenal na duba yiwuwar siyen Scott McTominay

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na duba yiwuwar siyen Elliot Anderson, mai shekaru 23, a mastyin wadna zai maye gurbin Casemiro, sai dai suna fuskantar gogayyar ciniki da Liverpool da Newcastle, da ake sa ran siyar ɗan wasan tsakiyar na Nottingham Forest kan Fam Miliyyan 100. (Times - subscription required)
Arsenal na duba yiwuwar ɗan wasan tsakiyar Napoli Scott McTominay, mai shekaru 28, yayin da Tottenham, da Everton daManchester United ke nuna sha'awa kan ɗan wasan. (Teamtalk)
Crystal Palace za ta sake farfaɗo da siyen ɗan wasan baya na Sporting Ousmane Diomande a wata Janeru, bayan da suka sa shi a matsayin wanda zai maye gurbin Marc Guehi, a lokacin da ya ke da shekaru, 25 zai koma Liverpool. (A Bola - in Portuguese)
Bayan Liverpool, Liverpool, da Tottenham, da Manchester United, da Manchester City da Arsenal, na son siyen ɗan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekaru 25. (Talksport)
Sunderland ba ta fidda rai wajen siyen ɗan wasan Lazio da Faransa Matteo Guendouz mai shekaru 26 ba a watan Janeru, a lokacin da kwantaraginsa ta ƙare kuma ake sa ran siyar da shi kan fam miliyan 22 zuwa 26. (Northern Echo)
Arsenal daba da kamala dai-daitawa da Bukayo Saka, wajen zamansa a ƙungiyar mafi tsayi, yayin da kwantaraginsa ke shirin ƙarewa a 2027. (Sky Sports)
A ci gaba da neman ɗan wasan gaban da Tottenham ke yi, ta fara mayar da hankalinta kan ɗan wasan Porto da Spaniya Samu Aghehowa, mai shekaru 21.(Teamtalk)
Akwai yiwuwar Chelsea da Manchester United su yi gogayya wajen siyen tsohon ɗan wasan Atlentico Madrid Samu. (Caught Offside)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai yi wuwar ɗan wasan Crystal Palace Chadi Riad ka iya tafiya aro, idan aka bude kakar siyen ƴan wasa, yayin da ɗan wasan Morokon ke ƙoƙarin ƙara ƙwazo wajen atisaye bayan wasu raunuka da ya samu. (Sky Sports)
Wolves na ƙyalla Ido kan ɗan wasan Manchester City James Trafford, a matsayin ɗan wasan da ta ke matuƙar son ɗauka a watan Janeru. (Teamtalk)
Manchester City za ta yi wa Newcastle tayin Trafford da kuma kuɗi don a bata ɗan wasan ingila Tino Livramento mai shekaru 23. (Teamtalk)
Harvey Elliott da yanzu haka ya ke a mastayin ɗan wasan aro a Aston Vila, na kan gaba cikin jerin ƴan wasan da ƙungiyoyi da ke taka leda a gasar Bundesliga da Serie A, ke son ɗaukar ɗan wasan Liverpool ɗin mai shekaru 22 cikin farashi da aka rage. (Football Insider)
Inter Milan na son ɗaukar mai tsaron ragar Argentina Emiliano Martineza kakar cinikin ƴan wasa a watan Janeru mai zuwa, yayin da Aston Vila ke shirin san ya shi cikin jerin ƴan wasan da za ta siyar. (Football Insider)
Crystal Palace sun tattauna da ɗan wasan gaba na Jean-Philippe Mateta, kan sabunta kwantaraginsa yayin da ake ci gaba da samu ƙaruwar sha'awar saiyensa. (Sky Sports)
Liverpool na ƙoƙarin ganin ta ci gaba da riƙe ɗan wasan IngilaJoshua Abe, yayin da Arsenal da Chelsea ke son daukar ɗan wasan mai shekaru 15. (Mail - subscription required)











