Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Iran ta riƙa kashe waɗanda take zargi da yi wa Isra'ila leƙen asiri tun bayan ɓarkewar yaƙi
- Marubuci, BBC Persian
- Lokacin karatu: Minti 4
Gwamnatin Iran ta ɗauki matakin gudanar da kame, tare da tabbatar da hukuncin kisa kan waɗanda take zargi suna da alaƙa wajen tattara bayanan sirri ga Isra'ila.
Wannan na zuwa ne bayan hukumomin ƙasar sun zargi wasu da aikata laifin da suka bayyana da "abu mai ɗaga hankali" na yin kutse cikin harkokin bayanan sirrin ƙasar, tare da kwarmata su ga Isra'ila.
Hukumomi a ƙasar sun ce bayanan da aka kwarmata wa Isra'ila ne suka taimaka wa ƙasar wajen samun nasarar kashe wasu muhimman mutanenta a yaƙin.
Daga cikin waɗanda aka kashe, har da kwamandan rundunar juyin-juya-halin ƙasar, da masana nukiliyarta, lamarin da Iran ta alaƙanta da tattara bayanan sirrinta da jami'an hukumar leƙen asirin Isra'ila, Mossad da ke cikin ƙasarta.
Nasarar da Isra'ila ta samu ya girgiza Iran matuƙa, wanda hakan ya sa hukumomin ƙasar suka kama duk wanda suke zargi yana da alaƙa da kwarmata bayanan sirri, inda ta ce ta ɗauki matakan ne domin tsaron ƙasarta.
Amma wasu na zargin wannan wata hanya ce ta hana mutane furta albarkacin bakinsu da hana ƴan ƙasar sakat.
A lokacin yaƙin wanda aka yi kwana 12 ana gwabzawa, hukumomin Iran sun yanke hukuncin kisa tare da zartar da shi kan mutum uku da take zargi da kwarmata bayanan sirri ga Isra'ila. Sannan a ranar Laraba - kwana ɗaya bayan tsagaita wuta - sai ta ƙara zartar da hukuncin kisan kan wasu mutum uku saboda irin wannan zargin.
Haka kuma hukumomin ƙasar sun sanar da kama ɗaruruwan mutane a ƙasar bisa zargin su da kwarmata bayanan sirri, musamman aiki da hukumar leƙen asirin Isra'ila.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun bayyana fargabarsu kan wannan matakan, sannan ana fargabar akwai wasu kamen da suke tafe a nan gaba.
Ma'aikatar tattara bayanan sirrin Iran ta yi ikirarin cewa tana ɗaukar matakin ne "domin yaƙi" da abin da ta kira yunƙurin hukumomin tattara bayanan sirrin ƙasashen yamma da Isra'ila wato da CIA da Mossad da M16 wajen yi mata kutse.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito, wanda kamfani ne da ke da alaƙa da IRGC, tun farkon yaƙin a ranar 13 ga Yuni, "hukumar leƙen asirin Isra'ila ta ƙara baza komarta a Iran."
Sannan ta ruwaito cewa a kwana 12 da suka gabata, hukumar leƙen asirin Iran da jami'an tsaron ƙasar sun kama "sama da mutum 700 da ke da alaƙa da kwarmata bayanan sirri."
Wasu Iraniyawa sun bayyana wa BBC cewa hukumar leƙen asirin Iran ta tura musu saƙonnin gargaɗin cewa lambobinsu sun fito a wasu kafofin sadarwa da suke da alaƙa a Isra'ila. An kuma umarce su da daina mu'amala da shafukan, ko kuma su fuskanci hukunci.
Haka kuma gwamnatin Iran ta ƙara ƙaimi wajen takura wa ƴan jarida masu ruwaito labarai a harshen Pashto a ƙasashen waje, ciki har da BBC da Manoto TV.
Kafar Iran International ta ruwaito cewa IRGC ta kama mahaifiya da mahaifi da ɗan'uwan wata ƴanjaridarta a Tehran domin tursasa mata ta ajiye aiki saboda yadda kafar ke labarai kan yaƙin Iran ɗin da Isra'ila.
Mahaifin ƴarjaridar ya kira ta a waya - wanda ake zargin jami'an tsaro ne suka tursasa shi - yana buƙatar ta ajiye aiki.
Bayan fara yaƙin, an yi wa wakilan sashen BBC Pashto da iyalansu barazana.
Ƴanjarida da suka fuskanci barazanar sun bayyana cewa jami'an tsaron Iran suna neman iyalansu suna musu barazana, sannan hukumomin ƙasar na kiran ƴanjaridar da "mohareb" - kalmar da ke nufin wanda ke yaƙi da Allah - laifin da a dokokin ƙasar mutum zai iya fuskantar hukuncin kisa.
Ita ma tashar Manoto ta ruwaito matsaloli irin haka, ciki har da barazana ga iyalan ma'aikatanta. Wasu daga cikin iyalan ana musu barazana da kalmar "ƙiyayya ga Allah" da cin amanar ƙasa - waɗanda dukansu manyan laifuka ne a dokokin ƙasar Iran.
Masana suna ganin waɗannan tsare-tsaren kama hanya ce ta tsoratar da ƴanjarida tare da tursasa su barin aikin ko barin ƙasar.
Haka kuma jami'an tsaro sun kama gomman masu fafutika, da marubuta da jarumai, a lokuta da dama ba tare da wani zargi ba a hukumance.
Haka kuma akwai zargin an kama wasu iyalan waɗanda aka kashe a zanga-zangar adawa da gwamnati ta mata ta "Woman, Life, Freedom" da aka yi a shekarar 2022.
A lokacin da ake yaƙin, gwamnatin Iran ta taƙaita amfani da intanet, sannan bayan an tsagaita wuta, intanet ɗin bai koma daidai ba.
Taƙaita ƙarfin intanet a lokacin yaƙi da ma lokutan zanga-zangar adawa da gwamnati na cikin tsarin da Iran ke amfani da su.
Sannan hukumomin ƙasar sun doɗe amfani da yawancin kafofin sadarwa na zamani irin su Instagram da Telegram da X da YouTube da ma shafin BBC Pashto a ƙasar, har sai an yi amfani da tsarin Virtual Private Network (VPN) domin samun sadarwa.
Mutane da dama suna zargin bayan tsagaita wutar, hukumomin Iran za su iya komawa cikin gida, su ƙara ƙaimi wajen kamen al'umma, yanke hukuncin kisa da ɗabbaƙa hukuncin, da ma tasa ƙeyar mutane zuwa gidan yari.
Masu nazari na amfani da abin da ya faru a shekarar 1988 a matsayin misali, lokacin da - kamar yadda masu kare haƙƙin ɗan'adam suka ce - an yanke hukuncin kisa tare da tabbatar da hukuncin kan dubban fursunonin yaƙi bayan shari'ar da aka yi a ɓoye cikin ƙanƙanin lokaci, sannan aka binne su a wani makaken ƙabari guda ɗaya.