Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun zaci ƙarshenmu ya zo': Isra'ilawa na jimamin ƙazamin harin Iran
- Marubuci, Alice Cuddy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporting from Beersheba, southern Israel
- Lokacin karatu: Minti 3
Jim kaɗan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin Iran da Isra'ila, jiniyar ankararwa ce ta tayar da mazauna birnin Beersheba daga barci tun da farar safiya a ranar Talata saboda makaman Iran da suka sauka.
An rubuta cikin saƙonnin gargaɗi da aka tura wa mazauna yankin ta waya cewa "babbar ankararwa". Sai kuma daga baya jiniya ta fara ƙara.
Kamar saura, Merav Manay da iyalanta sun tsere zuwa ɗakin tsira - wani ɓanagare na gidan nasu da aka gina da kankare ninki biyu da kuma ƙofar ƙarfe mai nauyi domin samun kariya daga harin roka.
Lokacin da makamin na Iran ya auka, sun ji gidan ya girgiza kuma babu abin da suka yi sai ɗora hannaye a ka.
"Ƙarar ta yi ƙarfi da yawa har mun zaci ƙarshenmu ne ya zo," in ji ta.
Bayan sun fito, sun tarar da tagogi duka sun ɗaiɗaice saboda girman fashewar. Amma dai bas u ji komai ba.
Merav ta ci gaba da zama a ginin tsawon wasu awanni cikin firgici da rashin tabbas na abin da za ta gani a wajen ginin.
A tsallaken titi kuma, wani gini ne mai kama da nasu ya ragargaje saboda makamin ya faɗa kan sa kai-tsaye.
Mutum huɗu aka kashe a wurin. Wani mai magana da hukumar tsaro ta cikin gida a Isra'ila ya faɗa wa BBC cewa su ma suna cikin ɗakunan tsiran lokacin da makamin ya faɗo.
Bayan harin, likitoci da sojojin Isra'ila sun ruga zuwa Baeersheba domin ceto mutane. Masu aikin sa-kai ne suka share ɓaraguzan da suka cika titunan yankin.
"Ina fatan wannan ne ƙarshen lamarin," kamar yadda wani mutum ya shaida wa BBC.
Jim kaɗan bayan harin na Baeersheba ne Isra'ila da Iran suka tabbatar cewa sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta, sai kuma suka fara zargin juna da karya ta.
Yayin da mazauna Baeersheba ke alhinin wannan hari da ya lalata garinsu, sun kuma nuna damuwa kan ko yarjejeniyar za ta ɗore.
Da yammacin Talata, Oren Cohen mai shekara 45 ya tsaya kan ɓaraguzan gidansa da ke kallon gidan da makamin ya faɗawa. Ya ce ba zai iya ma kallon ginin ba.
"Ina cikin damuwa game da 'ya'yana, sai yanzu ma na lura da abin da ya faru a nan," a cewarsa.
Oren na tare da matarsa da 'ya'yansa uku – masu shekara takwas, 12, da 15 – lokacin da aka kai harin, inda ya ce tagar ɗakin mai nauyi ta wangale saboda tsananin ƙarar harin.
Duk da yadda lamarin ya shafe shi kai-tsaye, Oren ya ce yana goyon bayan yaƙin da Isra'ila ke yi da Iran a lokacin.
"Ina ganin ba mu da zaɓi," in ji shi. "Mun yi abin da ya zama dole ne domin kare kanmu."
Ya ce bai sani ba ko zai "iya dogara" da tsagaita wutar amma ya ce ya yarda da gwamnatin Isra'ila za ta iya tantancewa ko ta cimma duka buƙatunta a Iran.
Lokaci na farko da Merav ta fita domin duba abin da ya rage na unguwar tasu a ranar Talata, ita ma ta ce tana da tabbas Isra'ila ba ta da wani zaɓi ne illa ta ka iwa Iran hari.
"Da ma dole ne wannan ta faru ko yanzu ko nan gaba. Mun shirya tsaf," kamar yadda ta bayyana.