Sabuwar girgizar-ƙasa a Turkiyya ta danne mutane da dama

...

Asalin hoton, EPA

Aƙalla mutum shida ne suka mutu a wata sabuwar girgizar-ƙasa, makwanni kaɗan bayan mummunar girgizar ƙasa da ta faru a yankin.

Yanzu haka masu aikin ceto na tonon ɓaraguzan gine-gine domin zaƙulo mutanen da suka maƙale.

Girgizar-ƙasar wadda ta kai 6.4 a ma’auni, ta faru ne a kusa da birnin Antakya, dab da kan iyaka da Syria.

Girgizar-ƙasar da aka samu a baya ta kashe mutum aƙalla 44,000 a Turkiyya da Syria, yayin da ta lalata muhullan dubun-dubatar mutane.

Gine-gine sun rushe sanadiyyar girgizar ta ranar Litinin.

Ministan lafiya na Turkiyya Dr Fahrettin Koca ya ce mutum 294 ne suka raunata, inda guda 18 ke cikin mawuyacin hali.

An yi amannar cewa mutanen da girgizar-ƙasar ta kashe ba su yi yawa ba ne saboda ta faru ne a wurin da mutane suka ƙaurace mawa bayan girgizar-ƙasar da ta faru a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Rahotanni daga birnin na Antakya na bayyana yadda mutane ke cikin tsoro da fargaba, yayin da motocin kai ɗaukin gaggawa ke kai-komo a kan tituna.

...

Asalin hoton, Reuters