Turai ta ɗimauce da nasarar zaɓen mai ƙin jinin Musulunci a Netherlands

    • Marubuci, Daga Katya Adler
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editar BBC a nahiyar Turai

Nasarar bazata mai cike da ban sha'awa ga Geert Wilders, ɗan siyasa mai janyo ka-ce-na-ce da kuma tsattsauran ra'ayi a zaɓen Netherlands na ranar Laraba, ta ingiza ɗokin jaridu a faɗin duniya.

Masu tsattsauran ra'ayin kishin ƙasa a faɗin Turai sun garzaya suna rige-rigen taya murna ga ɗan siyasar mai ra'ayin tafiya da talakawa, wanda a wasu lokuta ake yi wa laƙabi da Trump ɗin Holland - a wani ɓangare saboda gyaran gashin kansa na shalaman da yake rinawa, da kuma shahararsa wajen ɓarin bakinsa da kalaman gugar zana .

Ra'ayoyin da Geert Wilders ke bayyanawa a bainar jama'a - kamar na alaƙanta Musulmai 'yan ci-rani da ta'addanci, da yin kira a haramta buɗe masallatai da Alƙur'ani - suna matuƙar harzuƙa wasu, ta yadda har sai 'yan sanda sun ba shi tsauraran matakan kariya tun daga 2004.

Kotu ta taɓa samun Geert Wilders da laifin tunzura wariya a tsakanin jama'a, ko da yake an wanke shi daga bisani, sannan an taɓa hana shi shiga Birtaniya a shekarar 2009.

Sai dai masu matsanancin ra'ayi a Turai sun yi imani cewa manufofinsu a yanzu na daɗa samun karɓuwa a wajen rinjayen al'umma.

"Guguwar canji ta zo!" Firaministan Hungary, Viktor Orban ya bayyana, jim kaɗan da ganin sakamakon zaɓen na ƙasar Holland.

Shi ma, kamar Geert Wilders, ya yi fice kan manufar adawa da 'yan ci-rani, da gwale masu sukar aƙidar kafa Tarayyar Turai da mahukuntan Brussels ke yi.

Jagoran Flemish independence ta masu matsanancin ra'ayi Tom Van Grieken, da ya yi fatan samun irin nasarar Geert Wilders a zaɓen Belgium, cikin gaggawa ya shafa fatiha da cewa: "Jam'iyyu irin namu suna kan hanyar mamaye ko'ina a faɗin nahiyar Turai."

To, ko wanne Irin tasiri za mu sa ran gani, ba kawai a ƙasar Netherlands ba, amma har da (ga ƙwararrun jami'an Tarayyar Turai da ke zarya cike da alla-alla a zauruka lokacin rubutu), kan faɗin siyasar Turai?

Ko nasarar Geert Wilders take-yanke ta zo cikin sauƙi kamar yadda ake gani?

Haƙiƙanin gaskiya ma, ko shi kansa mutumin bai yi tsammanin wannan nasara ta samun kujeru masu yawa haka a majalisar dokoki ba. Ana iya ganin rawar murnar mamakinsa a wani bidiyonsa da aka wallafa a shafukan sada zumunta lokacin da yake kallon shigowar sakamakon a ranar Laraba.

Jami'an Wilders kamar yadda aka ba da rahoto kawai sun sun kama hayar wani ɗaki ne da suke amfani da shi a matsayin shalkwatar jam'iyya don wannan zaɓe, kwana uku kafin lokacin. Jam'iyyarsa ta Freedom Party ta samu haɓaka a a ƙarshen yaƙin neman zaɓe.

Abin da ga dukkan alamu ya kwashi masu kaɗa ƙuri'a a Holland shi ne haɗakar:

  • Mayar da hankalin Geert Wilders a kan taƙaita shigar 'yan ci-rani da yaƙi da matsalar ƙarancin gidaje a ƙasar da kuma inganta ayyukan kula da lafiya. Ya rage kaifin kalaman gugar zana na ƙin jinin Musulunci lokacin da zaɓe ya kusanto
  • Ya inganta ƙwazonsa a muhawarorin talbijin na yaƙin neman zaɓe idan aka kwatanta da abokan hamayyarsa.
  • Jam'iyyun siyasa masu rinjayen karɓuwar jama'a su ma sun sanya maganar 'yan ci-rani cikin manyan batutuwan yaƙin neman zaɓensu. Wannan ta sa mutanen Holland da yawa suka yanke shawarar cewa ai suna ma iya zaɓar "na ainihi". Geert Wilders babu shakka ya yi gangami a kan batun 'yan ci-rani tsawon lokaci fiye da kowa, kuma amonsa ya fi ƙarfi a fagen siyasar Netherlands.

Kuma cikin waɗanda suka taimaka wa Wilders samun nasara, amma ba da niyyar hakan ba, har da ɗaya daga cikin abokan hamayyarsa.

Dilan Yesilgöz-Zegerius, jagorar jam'iyyar VVD ta masu matsakaicin ra'ayi ta buɗe ƙofa a lokacin yaƙin neman zaɓe don shiga ƙawance da Geert Wilders. Hakan ya taimaka wajen sassauta kallon da ake yi wa jam'iyyarsa ta masu tsattsauran ra'ayi. Kafin lokacin, manyan jam'iyyun siyasar Netherlands sun yanke hukuncin cewa ba za su yi mulki da shi ba saboda salon siyasarsa.

Ko me duka wannan yake nufi ga nahiyar Turai?

Mai yiwuwa Geert Wilders ne jagoran jam'iyya mafi rinjayen kujeru a majalisar dokokin Netherlands, sai dai ko kusa ba shi da isassun kujerun da zai kafa gwamnati shi kaɗai. Za a shafe tsawon makonni nan gaba ana tattaunawa a fagen siyasa.

Mista Wilders ya amsa cewa akwai buƙatar ya yi sassauci kan wasu manufofin nasa don samun abokan ƙawancen siyasa. Kuma yanzu a wannan lokaci, babu tabbacin cewa Geert Wilders zai kasance firaministan Holland na gaba.

Idan kuwa shi ne, tarukan shugabannin Tarayyar Turai na iya zama masu zafi da ƙarin ɓaraka - saboda dalilai masu yawa.

Mista Geert Wilders dai yaƙin neman zaɓe mai tsanani da alƙawarin cire Netherlands daga Tarayyar Turai. Ko da yake a fili ya amsa cewa tunani ba shi da karɓuwa a wajen rinjayen masu zaɓe a ƙasar, amma yana iya matsa lamba don kaɗa ƙuri'ar raba gardama kan batun "Nexit" (fitar da Netherlands daga Tarayyar Turai).

Hukumar Tarayyar Turai ta faɗa a ranar Alhamis cewa ba ta damu ba. Kuma ta ce ta dogara a kan Netherlands (wakiliyar ƙasar da ta kafa Tarayyar Turai) za ta ci gaba da "shiga ana damawa da ita sosai" cikin harkokin ƙungiyar ƙasashen, in ji Eric Mamer mai magana da yawun Tarayyar Turai.

Sai dai hukumomin Brussels sun - kuma ya kamata su - damu game da haɗin kan Tarayyar Turai wajen tallafa wa Ukraine yayin da aka shafe watanni tun lokacin da Rasha ta fara cikakken mamayen da take yi.

Goyon bayan Ukraine dai akwai matuƙar kashe kuɗi.

Kamar shugabannin ƙasashe wakilan Tarayyar Turai na Hungary da Slovakia, Geert Wilders ma yana adawa da aika wa hukumomin birnin Kyiv ƙarin tallafin kayan aikin sojoji.

Geert Wilders ya ce yana son sanya ƙasarsa Netherlands farko a kan komai; kuma "ya mayar da ƙasar hannun 'yan Netherlands". Wannan tamkar wani furuci ne irin na Donald Trump da ke cewa A Mayar da Amurka ta Sake Zama Ƙasaitacciya ko kuma taken firaministar Italiya Giorgia Meloni na "Italiya da al'ummar Italiya su ne kan gaba a farko!"

Za ƙara amo a kan muryoyin shugabanni a tarukansu, ciki har da Mis Meloni, wajen ɗaukar tsattsaran matsayi a kan batun 'yan ci-rani a Tarayyar Turai da manufofin neman mafaka. Mista Wilders ya yi ta magana a kan "babban bala'in zuwan 'yan ci-rani".

Sai dai zai kasance abu mai matuƙar sauƙi, kamar yadda na yi imani, a yanke hukuncin cewa nasarar zaɓen Geert Wilders, wata manuniya ce cewa masu tsananin ra'ayi ko masu tsattsauran ra'ayi ko masu tunanin tsananin kishin ƙasa ko jam'iyyu masu biyewa tunanin rinjayen talaka - suna "ƙwace iko da nahiyar Turai", kamar yadda wasu masharhanta ke nunawa.

Jam'iyyar Law and Justice ta ƙasar Poland ta yi rashin nasara a babban zaɓe. Jam'iyyar Vox ta Sifaniya ta gaza taɓuka ko kusa da abin da aka yi hasashe a zaɓen ƙasar na lokacin bazara. A Netherlands, tikitin haɗin gwiwa tsakanin jam'iyyar Labour da ta Greens sun taka rawar gani.

Sai dai batun 'yan ci-rani, 'yan ci-rani, 'yan ci-rani da kuma tsadar rayuwa - suna nan a ko'ina mutumya duba a faɗin nahiyar Turai - kuma su ne manyan batutuwan da masu zaɓe ke bai wa fifiko.