Fitaccen mai ƙin jinin Musulunci da ya lashe zaɓe a Netherlands

Fitaccen jagoran masu ƙin jinin Musulunci, Geert Wilders ya yi nasara a babban zaɓen ƙasar Netherlands, da kusan duka ƙuri'un da aka ƙidaya.

Bayan shafe shekara 25 yana majalisar dokokin ƙasar, jam'iyyarsa ta ƙwatar 'yanci mai suna (PVV) na daf da lashe kujera 37, fiye da babbar jam'iyyar hamayya ta ƙawancen masu sassaucin ra'ayi.

"Ba za a taba mantawa da Jam'iyyar PVV ba, mu ne za mu yi shugabanci", in ji shi.

Nasararsa ta bayar da mamaki a siyasar Netherlands, kuma za ta ɗimauta siyasar nahiyar Turai.

To amma domin cika alƙawarinsa na zama "firaministan kowa'', dole ne ya janyo hankalin sauran jam'iyyu domin kafa ƙawance. Yana buƙatar samun kujera 76 daga cikin 150 da ke majalisar.

A lokacin taron jam'iyyar na ranar Alhamis, Mista Wilders, mai shekara 60, 'yan jam'iyyar sun yi masa tafi tare da karrama shi a ɗakin taron da ke cike da kyamarori.

Ya shaida wa BBC cewa "haƙiƙa'' yana da burin tattaunawa da ƙulla ƙawance da sauran jam'iyyu, domin ya zama firaminista.

Shugaban Jam'iyyar PVV ya lashe zaɓen bayan ɓarkewar ce-ce-ku-ce kan batun 'yan ci-rani, inda ya alƙawarta ''rufe kan iyakokin ƙasar'' sannan ya jaddada alƙawarinsa na haramta Al'qur'ani.

Ya kasance cikin yanayi na fushi yayin da yake jawabi kan nasarar da ya samu, inda yake cewa "Muna son yin mulki, kuma za mu yi mulki muna buƙatar samunsu (kujerun 'yan majalisa), kuma za mu same su".

Kafin zaɓen, manyan jam'iyyun hamayya uku, sun ce ba za su shiga gwamnatin Wilders ba, saboda tsare-tsare masu tsauri na jam'iyyarsa. To sai dai suna iya canza shawara saboda gagarumar nasarar da samu.

Jam'iyyar hamayya ta ƙawancen masu sassaucin ra'ayi ƙarƙashin jagorancin tsohon kwamishinan Tarayyar Turai, Frans Timmermans ce, ta zo ta biyu a zaɓen da kujera 25 a cikin kashi 94 na ƙuri'un da aka ƙidaya.

Mista Timmermans ya bayyana ƙarara cewa ba zai shiga gwamnatin Wilders ba, inda ya alƙawarta kare dimokraɗiyya da dokokin Netherlands. "Ba za mu bari wani ya fi wani ba a ƙasarmu.

A Netherlands kowa daidai yake da kowa,; kamar yadda ya shaida wa magoya bayansa.

Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayi ta VVD ta Dilan Yesilgöz, da sabuwar jam'iyyar mai kwarmaton bayanai, Pieter Omtzigt ne suka zo na huɗu a zaɓen, inda kuma dukkansu suka taya Geert Wilders murna game da nasarar da ya samu.

Duk da yake, Misis Yesilgöz na shakkar cewa mista Wilders zai iya samun adadin kujerun da yake buƙata, ta ce ya rage wa 'yan jam'iyyarta su yanke shawara kan matakin da za su ɗauka.

Kafin zaɓen, ta dage a kan cewa ba za ta shiga gwamnatin Wilders ba, amma ba ta yanke hukunci kan yin aiki da shi ba.

Shi kuwa Mista Omtzigt da farko cewa ya yi, sabuwar jam'iyyarsa ba za ta yi aiki da Mista Wilders ba, amma yanzu ya ce a shirye suke su yi wa waɗanda suka zaɓe su aiki".

Nasarar da Mista Wilders ya samu za ta kiɗima mutane masu yawa musamman a faɗin nahiyar Turai, saboda Netherlands na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka kafa ƙungiyar Tarayyar Turai.

To sai dai 'yan kishin ƙasa da jagororin masu matsanancin ra'ayi a faɗin Turai sun yaba da nasararsa.

A Faransa, Marine Le Pen ta ce nasarar ''ta tabbatar da ci gaba a fannin tsaron 'yan ƙasa".

Mista Wilders na buƙatar gudanar da ƙuri'ar raba gardama a kan ficewar Netherlands daga Tarayyar Turai, duk da cewa ya fahimci ƙasar ba ta buƙatar hakan.

Zai ɗauki tsawon lokaci wajen janyo hankalin masu ruwa da tsaki ko abokan ƙawance kafin su amince da wannan muradi nasa.

Ya sassauta kalaman gugar zanansa na ƙin jinin Musulunci a lokacin yaƙin neman zabe, yana cewa akwai ƙarin muhimman batutuwa, kuma ya shirya "jingine" manufofinsa "a firji" kan batun haramta masallatai da makarantun Islamiyya.

Dabarar ta yi nasara, wadda ta janyo masa ninki yawan mambobin jam'iyyarsa ta PVV a majalisar.

Adadin kujerun da kowacce jam'iyya ta samu

Batun ci-rani, ya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan da Mista Wilders ya ce zai magance a jawabin da ya yi ranar Laraba, inda ya alƙawarta magance batun "masu neman mafakar tsunami da batun 'yan ci-rani".

A shekarar da ta gabata 'yan ci-ranin da suka shiga Netherlands sun ninka fiye da 220,000, saboda yawan 'yan gudun hijira sanadin yakin Rasha da Ukraine.

Batun ya haddasa tsananin ƙarancin gidaje har 390,000.

A shalkwatar VVD ta Misis Yesilgöz da ke birnin Hague, magoya bayan jam'iyyar na shirin bayyana burinsu na samun mace ta farko a matsayin firaminsta a tarihin ƙasar.

To sai dai murnarsu ta koma-ciki a lokacin da sakamakon zaɓen ya fara bayyana a allunan majigi, inda suka riƙa kiran junansu a waya domin jajantawa.

Misis Yesilgöz ta karɓi ragamar shugabancin jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayi ne a lokacin da Mark Rutte, wanda ya fi kowa daɗewa a muƙamin firaminsitan ƙasar ya yi murabus daga harkokin siyasa cikin watan Yuli.

Ta je Netherlands ne tana yarinya 'yar shekara bakwai a matsayin 'yan gudun hijira daga Turkiyya, amma kuma tana da tsattsauran ra'ayi kan batun ci-rani.

Wasu daga cikin 'yan siyasa manyan shugabannin Musulunci na zarginta da buɗe ƙofa ga jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta hanyar ɗaukar matakin ƙin yin watsi da shiga gwamnatin Geert Wilders.

Misis Yesilgöz, mai shekara 46 ta yi ƙoƙarin nesanta kanta daga gwamnatin Rutte a lokacin da take ministar shari'a.

Yayin da ake dab da fara zaɓen, an bayyana kusan rabin masu zaɓe, a ƙasa da cewa ba jam'iyya suke zaɓa ba. Kuma da dama sun yanke shawarar ƙin mara mata baya.

Sa'o'i kafin kaɗa ƙuri'ar, Mista Wilders na cike da murna kan damr da yake da ita a zaɓen, inda ya shaida wa BBC cewa ''Ina tunanin wannan ne lokaci na farko a Holland da a cikin mako guda mun samu kujeru 10 a zaɓen."

Ya bayyana jan aikin da ke gabansa na kafa gwamnatin da zai jagoranta, amma ya ce shi mutum ne mai kawo ci gaba, kuma nasarar da gwamnatinsa za ta yi, "Zai yi wa jam'iyyun adawa wahala su watsar da mu".