An dakatar da Fagioli na Juventus wata bakwai kan yin caca

Asalin hoton, Getty Images
Nicolo Fagioli ya kammala kakar bana, bayan a ranar Talata hukumar kwallon kafar Italiya ta dakatar da shi tsawon wata bakwai, saboda karya dokar yin caca.
A wani jawabi da ta fitar, hukumar ta ce ta samu Fagioli da yin caca a wasannin tamaula da kuma yin wasu abubuwan da aka haramta wa duk kwararren dan kwallo yi.
Hukumar ta kara da cewar laifin nasa na dakatarwa ne tsawon shekara daya, amma daga baya ta yi masa sassauci.
Fagloli, mai shekara 22, zai yi aikin kyauta tsawon wata biyar a hukumar da ke kula da kwallon masu tasowa.
Dan wasan, tauraruwarsa na tashe a fagen kwallon Italiya tun bayan komawarsa Juventus a bara, bayan zaman aro da ya je a Cremonese, kuma ya buga wa kasarsa karawa daya.
Hakan na nufin ba zai yiwa Juventus wasa ba, wadda tun farko aka dakatar mata da Paul Pogba a kan laifin shan abubuwan kara kuzari.
Ana sa ran, tsohon dan wasan Manchester United zai koma taka leda a tsakiyar watan Mayu a lokacin saura wasa biyu a kammala Serie A.
Ya kamata a hukunta shi shekara uku, amma ya bayar da tabbacin zai daina caca, kuma ya yarda da duk hukuncin da aka dauka a kansa.
Wannan shi ne hukuncin farko da aka yi a lokacin da Italiya ke shirin fafatawa da Ingila a Wembley ranar Talata a wasan neman shiga gasar Euro 2024.














