Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara

.

Asalin hoton, Getty Images

Yaƙin Habasha, tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar Tigray People's Liberation Front (TPLF), ya sake dawowa sosai.

Babu tabbas kan batun komawa teburin sasantawa don kawo ƙarshensa.

Ɓangarorin biyu duk suna zargin juna da sake farfaɗo da faɗan.

Abin da ya fito fili daga bayanan da aka samu a wajen jami’an diflomasiyya na ƙasashen yamma – su ne Rundunar tsaron Ehtiopia da ƙawarta ta mayaƙan sa kai na Amhara da aka fi sani da Fano, sun haɗa kan gagarumar runduna zuwa wannan wajen a makonnin da suka wuce.

A hannu guda kuma, ƙungiyar TPLF ta ƙara inganta rundunarta ta hanyar samar da ƙarin abubuwan buƙata da bayar da horo da makamai, duk da cewa dai ta yi watsi da batun cewa ta sake ɗaukar sabbin dakaru.

A yaƙin da aka yi bara, ta samu nasarar ƙwace manyan makamai daga sojojin gwamnatin, sannnan ana yada jita-jitar cewa ta sayo sabbin makamai daga ƙasashen waje.

Fargaba na ƙaruwa. Sannan, makonni kaɗan da suka wuce, an yi fatan ba da daɗewa ba za a fara tattaunawar cimma yarjejeniya.

Firaministan Abiy Ahmed ya umarci mataimakinsa Demeke Mekonnen, ya jagoranci kwamitin tabbatar da zaman lafiyar, wanda ya fara aiki a wtan Yuli.

Ko kafin sannan ma, rahotanni sun ce Mr Abiy ya sha aika manyan jami’ai da su gana da ƙungiyar TPLF a asirce.

A wasu zama da aka yi a Seychelles da Djibouti, ya bayyana cewa an cimma yarjejeniya cewar dakarun Ethiopia za su ɗage takunkumin da suka sa a Tigray, kuma Eritrea za ta janye dakarun da ta aika don goyon bayan gwamnatin kuma ɓangarorin biyu za su fara tattaunawa a Nairobi, babban birnin Kenya, inda Shugaba Uhuru Kenyatta zai karɓi baƙunci.

Batu na farko da za a duba shi ne na tsagaita wuta ta dindindin.

A gefe guda kuma, Amurka na goyon bayan waɗannan tattaunawa kuma tana aiki da Kenya a kan hakan. 

Nearly five million people are in need of aid in Tigray

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kusan mutum miliyan biyar ne ke buƙatar agaji a Tigray
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yayin da ya kai ziyara Mekelle, babban birnin Tigray ran 2 ga watan Agusta, Jakadan Amurka na musamman Mike Hammer da wasu jakadun ƙungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da “a gaggauta mayar da wutar lantarki da layukan waya da harkokin banki da sauran abubuwa”, tare da buɗe hanyar kai agajin gaggawa, yana mai nuna cewa Mr Abiya ya yi alkawarin yin dukkan wadannan abubuwan.

Haka kuma, jakadan ƙungiyar Tarayyar Afirka, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya yi gum da bakinsa kan toshe hanyar shiga da agajin. Da yake yi wa jakadun bayani, Janar Obasanjo ya dage cewa shi ne babban mai shiga tsakani tare da ba su mamaki inda ya nemi a gayyaci ƙawar Ethiopia, wato Eritrea zuwa tattaunawar.

TPLF ta zargi gwamnati da karya alkawuran da ta ɗauka. Gwamnatin ba ta yarda an cewa an yi wani zama ba. Su ma jakadun ƙasashen duniya ba su faɗi dalilin rashin komawa zaman ba.

A baki ɗaya watan Yuli da Agusta Addis Ababa ba ta bari an shigar da muhimman abubuwan buƙata ba sai ƴan kayan abinci da magunguna da takin noma.

TPLF ta dage cewa Addis Ababa ta ci gaba da toshe hanyoyin shigar da kayayyaki ne don uzzura yunwa ta zama wani makami na yaƙi, kuma ayyukan jin ƙan ba sa wadata.

A wata buɗaɗɗiyar wasiƙaga shugabannin duniya a yammacin da aka fara faɗan, shugaban TPLF Debretsion Gebremichael ya ce: “Muna fuskantar mutuwa a wannan gaɓa ta ko ina muka juya.

Zaɓinmu shi ne ko dai yunwa ta kashe mu ko kuma mu mutu a wajen neman ƴanci da mutuncinmu.

A makon da ya gabata ne rundunar sojin saman Ethiopia ta kai hare-haren bam Mekelle, lamarin da ya shafi wata makarantar renon yara har mutum bakwai suka mutu, ciki har da yara uku, a cewar ma’aikatan lafiya.

Gwamnati ta ƙaryata lamarin inda ta ce ta kai harin ne da nufin samun sansanin sojoji. Rahotanni sun ce an sake kai wani harin sama na biyu a ranar Talata da daddare.

Tigrayans say an air strike caused civilian casualties when it hit a kindergarten

Asalin hoton, TIGRAI TV/REUTERS

Bayanan hoto, Ƴan Tigray sun ce wani harin sama ya jawo mace-macen fararen hula a wata makarantar renon yara

Ƴan Tigray sun nemi MDD ta ba su tankoki 12 na man fetur, abin da ya jawo tur daga manyan jami’an jin ƙai.

TPLF ta ce ta rantawa MDD fetur a watannin baya shi ya sa suka nemi a dawo musu da abinsu, amma yadda suka tambaya da lokacin da suka yi hakan sun nuna cewa ba don ayyukansu na yau da kullum suka tambaya ba, kamar yadda mai magana da yawunsu ya ce.

Rundunar sojin Habasha ta ce wani jirgi ta harbo da yake kai makamai Tigray daga sararin samaniyar Sudan. Kungiyar TPLF ta ƙaryata.

Akwai rahotannin da ke cewa dakarun Eritrea da na Ethiopia suna ta kai komo a Eritrea – a wani waje kusa da kan iyakar Tigray.

Gwamnatin Eritrea ba ta ce komai ba. A ranar Laraba, an ce faɗa ya ɓarke a yammacin Tigray kusa da iyakar Sudan. Kuma bayanai na cewa faɗan na garin Kobo gagarumi ne.

Majiyoyin Tigray sun ce sun samu nasara kan wata gagarumar bataliya inda har suka ƙwace wasu tarin makamai. Amma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Ita ma gwamnatin Ethiopia ta ƙaryata cewa ta tafka asara. Sannan ta umarci kafafen yaɗa labarai da su yi taka tsantsan wajen bayar da rahoto da yadda suke samun bayanai a lokutan rikici saboda kare muradun ƙasar.

Ta ce ta kwashe mutane daga Kobo, kuma rahotanni daga birnin Woldia mai nisan kilomita 50 daga kudu, suna cewa babu sojoji a wajen.

Zuwa yanzu dakarun TPLF ba su koma kudanci ba, ƙungiyar na cewa ba ta da niyyar maimaita abin da ta yi a bara na kutsawa har tsakanin kilomita 200 na babban birnin.

A taƙaice dai mai magana da yawunta ya ƙryata rahotannin cewa TPLF ta ƙwace iko da Woldia.

Taswira

Matsayar TPLF ita ce a yi gaggawar zaman tattaunawa. Duk da cewa ta yi haɗaka da rundunar Oromo Liberation Army, to ba ta da haɗakar da za ta yi gagarumin yaƙi da gwamnatin tarayyar a kudu da yammacin Ethiopia.

Kuma abin da mafi yawan ƴan Tigray ke tunani shi ne za su yi yaƙi don kare yankinsu ne kawai.A yanzu dai babu wani ƙwaƙƙwaran mataki.

Wahalhalu da mace-macen da aka samu a wancan satin ya fito da wani abu da ya kamata a ce Habasha da ƙasashen duniya sun daɗe da sani – na cewa amfani da ƙarfin soji ba shi ne mafita ga yaƙin Tigray ba.