An dakatar da Lewandowski wasa uku a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da Robert Lewandowski daga buga wasa uku a La Liga, bayan jan kati da aka yi masa a wasa da Osasuna a makon jiya.
Ranar 8 ga watan Nuwamba, Barcelona ta je ta ci Osasuna 2-1 a wasan mako na 14 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya
Mai shekara 34, yanzu yana tare da tawagar Poland a Qatar, domin buga gasar kofin duniya da za a fara ranar 20 ga watan Nuwambar 2022.
Dan wasan an bashi kati mai ruwan doraya biyu a karawar, na biyun a dalilin gula da ya yi wa David Garcia da ta kai aka yi masa jan kati.
Shi kuwa Gerard Pigue an dakatar da shi wasa hudu, bayan da ya zagi alkalin wasa da aka yi hutu kan jan katin da ya bai wa Lewandowski.
Shi dai tsohon dan kwallon tawagar Sifaniya, Pigue ya yi ritaya daga taka leda bayan fafatawar.
An dakatar da Lewandowski wasa uku, sakamakon gatsinen da ya yi wa Alkalin wasan da ya bashi jan katin.
Karo na biyu da aka bai wa Lewandowski jan kati a tarihin sana'arsa ta tamaula.
Kenan ba zai buga wa Barcelona karawa uku ba da za ta yi da Espanyol da Atletico Madrid da kuma Getafe, bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar.











