Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ke ƙirƙiro wa Trump manufofin da ke jawo cece-kuce
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
A tsawon shekaru Stephen Miller ya kasance wani mai hanƙoron ganin an samu nasara a tafiyar siyasar Donald Trump. Yanzu, ya zama mai janyo suka.
Turjiyarsa da kuma ba ji ba gani a ɓangaren tsare-tsaren fadar White House, su suka janyo Trump ya ki sassautawa ƴan ci-rani da ke ƙasar kuma ya samu wani ƙarfi na gaske wajen faɗaɗa ikon Amurka a faɗin yankuna.
Ganin yadda gwamnatin Trump ta fara da tsare-tsare masu sauri a 2026 a ciki da wajen ƙasar, shi ya sa ya zama ɗaya daga cikin masu ƙarfin faɗa a ji.
Sai dai, wasu mutane da dama na ɗaukarsa a matsayin mugun mutum.
A Washington DC, an liƙa fostocin Miller a wuraren taruwar jama'a tare da sukarsa, inda jam'iyyar Democrat suka yi kiran ya ajiye aikinsa.
Wasu mambobin jam'iyyarsa ma sun fito fili sun soki wasu tsare-tsarensa.
A tsawon makonni kalilan da suka gabata, Miller ya tsinci kansa a yanayin da bai saba gani ba - wato ya zama wanda ake tattauna batunsa a faɗin ƙasar, inda ake suka da kuma Alla-wadai da matakansa.
Dole ta sa ya saduda - aƙalla na wucin gadi - daga abubuwan da yake yawan yi.
'Jajirtacce ne, ba ya taɓa ƙaraya'
Jim kaɗan bayan wasu jami'an shige da fice na ƙasar guda biyu sun harbi wani mai suna Alex Pretti har lahira a Minneapolis a watan da ya gabata, Miller ya wallafa sakonni da dama a shafin X, inda ya zargi jami'in lafiyar da cewa "ɗan ta'adda" kuma mai "aikata kisa".
Amma mutane ba su ɗauki hakan da mamaki ba saboda irin abubuwan da Miller ya riƙa yi lokacin yaƙin neman zaɓen Trump a 2016. Ya kuma zargi Democrat da "kunna wutar hamɓarar da gwamnati". Sai dai hujjoji sun tabbatar da iƙirarinsa ba gaskiya bane.
Wasu ƙarin hujjoji na bidiyo sun ce duk da cewa Pretti na da bindigar hannu mai lasisi, bai yi wa jami'an tsaron iyaƙa barazana ba kafin a busa masa hayaki mai sa hawaye da kuma harbi har sau goma.
Kwanaki kaɗan bayan nan, Miller ya fitar da wata sanarwa da ke cewa gwamnati ta gano an yi harbi ne bayan samun rahotanni daga jami'an shige da fice da ke yankin na Minneapolis - kuma zai kasance waɗannan jami'ai ba sa bin ka'idoji yadda suka kamata.
Abu ne da ba a saɓa ji ba daga jajirtaccen mutumin - sai dai abin bai gamsar da masu sukarsa na jam'iyyar Democrat ba, waɗanda suka zarge shi da ƙarfafa wa jami'an kwastam da na shige da fice wajen murkushe masu zanga-zanga.
"Miller bai ji kunya ba duk da kashe waɗannan Amurkawa da jami'ai suka yi, inda ta kai har yana ɓata musu suna bayan mutuwarsu," in ji ɗan majalisar Democrat Don Beyer daga jihar Virginia.
"Miller wani mugun mutum ne mai son a zub da jini kuma mara tunani, kuma tsare-tsarensa na saka rayuwar al'umma cikin barazana muddin ya ci gaba da zama kan mulki."
Magana da yawun shugaban ƙasa
Mukamin Miller a fadar White House shi ne mataimakin shugaba kan ɓangaren tsare-tsare da tsaron cikin gida.
"Stephen Miller ya yi wa shugaba Trump aiki yadda ya kamata na tsawon shekaru saboda yana da ƙwarewa, ilimi, jajirtacce kuma mai mubaya'a," kamar yadda sakatariyar yaɗa labarai na fadar White House Karoline Leavitt ta shaida wa BBC.
"Stephen na haɗa kan duka ɓangarorin gwamnati wuri guda don tabbatar da cewa an aiwatar duk wani tsari na cikin gida ko na waje cikin sauri. Nasarar da aka samu a tsawon shekara ɗaya da ta gabata ba zai misaltu ba."
A wani lokaci a shekarar da ta gabata, an riƙa bayyana cewa Miller zai zama mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro a faɗin ƙasar, inda zai maye gurbin Michael Waltz da aka tuɓe - sai dai shugaba Trump ya yi watsi da raɗe-raɗin.
"Stephen ya zarce nan ba kaɗan ba," in ji Trump.
A watan Maris ɗin da ta wuce, a daidai lokacin da Amurka ta kaddamar da hari kan ƴan tawayen Houthi a Yemen, wasu jerin sakonni da aka fitar a shafin Signal sun nuna cewa Miller na da hannu dumu-dumu wajen tsare-tsare, da kuma magana da yawun shugaban ƙasar wajen kai hare-haren.
"Da na ji batun, na gane abin da shugaban ƙasa yake so: A aikata kawai," kamar yadda ya rubuta a cikin wani dandali ɗauke da mataimakin shugaban ƙasa JD Vance da sakataren tsaro Pete Hegseth da kuma sakataren harkokin waje Marco Rubio.
A bara, an ruwaito cewa Miller ne ke da alhakin sa ido a aikace-aikacen sojoji a yankin Caribbean waɗanda ke aikin lalata jiragen ruwa da ake zargi da safarar ƙwayoyi - abin da ya ƙara rikiɗe wa zuwa tumɓuke shugaban Venezueal Nicolas Maduro daga mulki a farkon watan Janairu.
Lokacin da Trump ya sanar daga gidansa na Mar-a-Lago cewa an kama shugaba Maduro, Miller na cikin jami'ai kalilan da ke tsaye a bayan shugaban ƙasar.
Ba a san takamaimen aikin Miller ba a tsarin harkokin waje, in ji Lanza, jami'i a fadar White House.
"Stephen yana da ƙwarewar da ta kai ya san Donald Trump ba shugaba bane na gargajiya, kuma zai so sanin su waye ke kusa da shi don ba shi shawara," in ji Lanza.
"Stephen ya yi aiki mai kyau na kasancewa kusa da Trump da kuma ba da shawara. Ba zai samu nasarar yin haka ba karkashin wani shugaban gargajiya."
Fara harkar siyasa a California
Miller ya fara janyo cece-kuce tun yana karami. Ya halarci makarantar Santa Monica a Los Angeles.
Ya fara ne a shekarar 1999, shekara guda bayan da wata babbar kotun tarayya ta soke haramcin da California ta saka kan shirin taimakawa ƴan ci-rani. Kuma lokaci ne da ƴan ci-rani da ke shiga Amurka ta iyakar ƙasar da Mexico suka ƙaru.
Miller ya karanci kimiyyar siyasa a Jami'ar Duke. Ya samu wata ɗaukaka bayan kare wasu fararen fata uku waɗanda aka zarga da aikata fyaɗe bisa kuskure - wata mata bakar fata ce ta bayyana cewa kariya aka yi musu.
Abu ne da Miller ba zai taɓa mantawa ba a rayuwarsa na Jami'a, kuma shi ne ya ƙara janyo masa farin jinin shiga siyasa.
Jim kaɗan bayan kammala karatu, ya samu aiki a matsayin sakatare a ofishin ƴar majalisar dokokin Amurka, Michele Bachmann daga Minnesota.