Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 10/11/2024
Lokacin karatu: Minti 1
Filin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu na wannan makon wanda ya ƙunshi wani labari na shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar Equitoral Guinea da wasu hotunansa na bidiyo na lalata da mata suka bayyana.
Sannan ya ƙunshi labarin wata mata da ta yi fice wajen ɓad da kama tana sata a shaguna da manyan kantina a Ingila.
Haka kuma akwai labarain yadda wani tsohon ɗan ƙwallon ƙafa na ƙasar Kolombiya na duniya ya faɗa rami har ya yi karaya tara da rauni a huhu, a lokacin atisaye, da matarsa amma kuma ya rayu.








