'Muna cikin tashin hankali': Ƴan ci-ranin da aka kwashe daga Amurka zuwa Panama

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Cecilia Barría, Santiago Vanegas y Ángel Bermúdez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 6
"Don Allah ku taimake mu," shi ne abin da ke a rubuce jikin wata takarda da wasu ƴanmata biyu suka riƙe a bakin tagar ɗakin wani otal da ke birnin Panama City na ƙasar Panama.
Waɗanda ke zama a otal ɗin na iya hangen ruwan teku, yana da ɗakin cin abinci, da wurin kula da jiki da wurin ninƙaya da kuma hanyar sufuri.
Amma yanzu otal ɗin ya zamo masaukin wucin-gadi da ake sauke ƴan ci-rani 299 wadanda aka kora daga Amurka, kamar yadda gwamnatin ƙasar Panama ta sanar a ranar Talata.
Wasu daga cikin ƴan ci-ranin da aka sauke a otal ɗin sun ɗaga hannu domin nuni da cewa an tauye musu ƴancinsu. Wasu kuma sun sagala takardu ɗauke da saƙonnin da ke cewa: "Ba ma cikin aminci a ƙasarmu."
An tura waɗannan ƴan ci-rani zuwa ƙasar ne a wani ɓangare na manufar gwamnatin Donald Trump ta korar baƙin haure daga Amurka, inda suka isa Panama a makon da ya gabata cikin wasu jirage uku.
A baya-bayan nan ne shugaba Panama, Jose Raul Mulino ya amince cewa ƙasarsa za ta zamo wani zango ga mutanen da ake kora daga Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai, daga cikin ‘yan ci-ranin 299 - wadanda suka fito daga kasashen Indiya, da China, da Uzbekistan, da Iran, da Vietnam, da Turkiyya, da Nepal, da Pakistan, da Afghanistan da kuma Sri Lanka - guda 171 ne kawai suka amince za su koma kasashensu na asali.
Hakan na nufin wadanda ba su amince da komawa kasashen nasu ba suna cikin hali na rashin tabbas.
Gwamnatin Panama ta ce za a tura ‘yan ci-ranin zuwa sansanin Darien, wanda a baya aka taba ajiye wasu ‘yan ci-ranin da ke kan hanyarsu ta zuwa Amurka.
A baya, baki na shiga da fita daga otal din cikin sauki, to amma yanzu sojoji ne dauke da bindigogi ke gadin shi.
Daga nesa za a iya hango yadda aka shanya kayan da aka wanke ta jikin taga, a wata tagar kuma wasu mutane ne maza da mata da yara suna daga hannuwansu, suna yin alamar neman a kai musu dauki.

Asalin hoton, Getty Images
'Muna cikin fargaba'
Wata mata ‘yar asalin Iran, wadda ta zauna a kasar ta Panama na tsawon shekaru ta shaida wa BBC cewa ta yi magana da daya daga cikin ‘yan ci-ranin da ke cikin otal din, kuma suna cikin “tashin hankali” bisa tunanin cewa za a mayar da su Iran.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce ta je otal din domin ta taimaka a matsayin mai yin fassara ga mutanen da ke amfani da harshen Farsi, to amma sai aka ce mata akwai wata mai yin fassarar, duk da cewa bayanai sun nuna mata cewa ba gaskiya ba ne.
Ta hanyar amfani da wata wayar hannu a boye, kasancewar an haramta wa mutanen da ke cikin ital din yin magana da mutanen waje, ‘yar Iran din da ke cikin otal din ta shaida mata cewa akwai “yara da dama a cikin otal din” wadanda abin ya rutsa da su.
Sun ce an hana su samun lauya kuma an haramta musu fita daga dakunansu, ko da kuwa suna son su ci abinci ne.
Bayan da kafafen yada labarai suka bayar da labarin ‘yan ci-ranin da ke tsare a otal din a ranar Talata, an kara tsaurara tsaro inda har aka yanke sadarwar intanet din da suke samu, in ji matar ‘yar asalin Iran.
BBC ta tuntubi shugabannin otal din na Decapolis da kuma gwamnatin Panama game da halin da ‘yan ci-ranin ke ciki, sai dai babu wanda ya ce uffan.
Sai dai ministan kiyaye lafiyar al’umma na Panama, Frank Abrego ya mayar da martani da cewa wajibi ne gwamnati ta kare lafiya da zaman lafiyar ‘yan asalin Panama.
A cikin wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna daya daga cikin ‘yan ci-ranin na bayani cikin harshen Farsi, yadda aka tsare subayan sun tsallaka iyaka zuwa cikin Amurka, inda aka fada musu cewa za a kai su jihar Texas, amma sai ga shi an kai su Panama.
Matar da ke cikin bidiyon ta dage kai da fata cewa rayukansu na cikin hatsari idan aka mayar da su Iran sanadiyyar irin matakin da gwamnati za ta iya dauka a kansu.
Ta bayyana cewa tun farko aniyarta ita ce ta nemi mafaka ta siyasa.
Masu nazarin al’amura sun ce wannan abu ne mai wahalar samu ba tare da taimako lauya ba - sannan kuma gwamnatin Panama ta ce ba za ta yi wa mutanen da aka koro irin wannan alfarmar ba.

Asalin hoton, Reuters
'Tsarewar wucin-gadi'
A ranar Talata, Abrego ya ce ‘yan ci-ranin za su zauna na wani dan lokaci ne a Panama karkashin kulawar gwamnati.
“Yarjejeniyar da muka cimma da Amurka ita ce za su zauna a hannunmu na wani lokaci domin tsaron lafiyarsu,” in ji shi.
Ya kuma yi gargadin cewa duk ’yan ci-ranin da ba su son komawa kasarsu ta asali to sai dai su zabi wata kasar ta daban.
Ya kuma a game da haka, Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya da kuma shugaban Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ne za su yi aikin kai su kasar da suke so.

Asalin hoton, EPA
Abrego ya kuma ce an ajiye ‘yan ci-ranin a otal din Decapolis ne saboda yana da girman da zai dauke su.
Wani babban jami’i ya bayyana cewa “ba a tsammanin samun wani jirgin dauke da ‘yan ci-ranin kamar na farko” kasancewar babu yarjejeniya kan hakan.
Panama ta amince ta zamo “zango” ga wadanda za a kora daga Amurka ne bayan wata ziyara da Sakataren harkokin waje na Amurka, Marco Rubio ya kai a kasar yayin da zaman dardar sanadiyyar kurarin da Trump ya yi na “kwato” yancin Mashigin Panama.
Wani mai magana da yawun hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya ya shaida wa BBC cewa hukumar ce ala dora wa nauyin samar da abubuwan bukatu ga mutanen da aka kora daga Amurka.
“Muna aiki tare da jami’ai a yankin domin taimaka wa wadanda abin ya shafa, muna taimaka wa wadanda ke son komawa gida bisa radin kai, sannan mu nema wa sauran mutanen zabi mai aminci,” in ji shi.
“Yayin da ba ma son sa hannu wajen tsarewa ko takura wa mutane, amma daya daga cikin abubuwan da muke son tabbatarwa shi ne mu tabbatar an kula da wadannan mutane cikin mutunci bisa tsari kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada,” in ji shi.











