Me zai iya taƙaita ikon Shugaba Trump?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Ángel Bermúdez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 7
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alƙawarin aiwatar da wasu tsauraran sauye-sauye a lokacin mulkinsa na biyu.
Bayan rantsar da shi ya sanya hannu a wasu tarin dokoki da suka haɗa da ƙaddamar da dokar-ta-ɓaci a kan iyakar Amurka da Mexico, da ayyana manyan ƙungiyoyin masu hada-hadar miyagun ƙwayoyi a matsayin ƙungiyoyin ta'adda tare kuma da yin afuwa ga waɗanda ke da hannu a tarzomar da aka yi a majalisar dokokin ƙasar ranar 6 ga watan Janairun 2021.
A lokacin yaƙin neman zaɓensa ya yi alƙawarin aiwatar da korar baƙi da ba a taɓa ganin irinta ba a tarihin Amurka, da rage yawan bin matakan gwamnati wajen aiwatar da ayyuka, da rage haraji, da kuma ɓullo da sababbin haraji a kan kayan waje.
Domin cimma wannan burin nasa Mista Trump yana sa ran samun goyon bayan majalisun dokokin ƙasar biyu waɗanda dukkaninsu ke ƙarƙashin shugabancin jam'iyyarsa da kuma alƙalan kotun ƙolin ƙasar da yawancinsu masu ra'ayin riƙau ne irinsa.
To amma akwai tsarin taka masa birki da taƙaita ikonsa da kuma sauran ƙalubale a gabansa kan wannan buri nasa.
Ga wasu abubuwa shida da masana suka ce ka iya taƙaita shirin nasa.
1. Rinjaye kaɗan a majalisun dokoki

Asalin hoton, Getty Images
'Yan jam'iyyar Republican ne ke da rinjaye a majalisun dokokin Amurka biyu - ta wakilai da ta dattijai - to amma rinjayen ba shi da yawa.
Republican suna da 220 yayain da Democrat suke da 215. Kuma akwai 'yan Republican biyu a majalisar wakilai da suka sauka daga kujerunsu a majalisar wakilai kuma ana sa ran wani ma ya biyo baya - hakan zai sa rinjayen ya zama da kujera biyu kawai ko da yake za a yi zabe a kan kujerun a watannin da ke tafe.
Farfesa Mark Peterson masani a kan manufofi da shari'a da kuma siyasa a jami'ar California, Los Angeles ya sheda wa BBC cewa, 'yan Republican suna da hadin kai sosai to amma duk da haka yana da wuya ka iya hada kansu a kan batun da ke da sarkakiya.
A majaisar dattawa Republican suna da kujeru 53 yayin da Democrat suke da 47. Wannan na nufin ba su da gagarumin rinjaye na kujeru 60 da suke bukata su yi yadda suka ga dama - wannana na nufin 'yan majalisa na bangaren hamayya ka iya jinkirta ko ma hana kada kuri'a a kan wata bukata.
Sai dai kuma akwai wata hanya da ake sasanto inda majalisar dattawa za ta iya amincewa da kasafin kudi da rinjaye kadan na kujeru 51.
Farfesa Peterson ya ce 'yan Republican ka iya bin wannan hanya wajen cimma wasu daga cikin manufofinsu.
2. 'Yancin kai na bangaren shari'a

Asalin hoton, Getty Images
Kotun kolin Amurka ta na da alkalai tara, wadanda shugaban kasa ke zabar a duk lokacin da aka samu gurbi.
A yanzu shida daga cikin su taran masu ra'ayin rikau ne- kuma uku daga cikinsu Trump ne ya zabe su a lokacin mulkinsa na farko - to amma wannan ba yana nufin kotun za ta goyi bayan duk abin da yake so ba, kamar yadda aka gani a kan wasu manufofi a baya.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun Kolin ta yi watsi da kudurin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na 2020 da kuma kudurin korar baki da suka shiga Amurka ba bisa ka'ida ba tun suna yara kuma suka girma a can - da ake wa lakabi da Daca.
Bayan Kotun Kolin kamar yadda binciken Cibiyar Pew Research ya nuna kashi 60 cikin dari na alkalan kotun gunduma shugabannin kasar na Democrat ne suka zabe su, yayin da kashi 40 cikin dari na Republican ne suka zabe su.
Duk da wannan zabe da shugabanni ke yi na alkalai, masu shari'ar suna aiki ne bisa doka da kuma tsarin da Kotun Kolin ta bi a baya - a takaice dai bangaren shari'a yana da 'yancin kansa sosai.
3. Gwamnatocin jiha da ƙananan hukumomi

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsarin tarayya na Amurka ya taƙaita sauye-sauyen da shugaban ƙasa zai iya tilastawa a yi.
Kundin tsarin mulkin Amurka - (gyara na 10), ya bayar da iko sosai ga gwamnatocin jihohi - jihohin ne kuma daman suke kula da tsaro da lafiya da ilimi da tallafa wa jama'a da dokokin manyan laifuka da dokokin ƙwadago da dokokin gidaje.
Haka su ma gwamnatocin ƙananan hukumomi suna da ikon da yake a ƙarƙashinsu.
Farfessa Peterson yana ganin 'yan Democrat za su yi amfani da wannan iko su ƙalubalanci gwamnatin Trump a matakin gwamnatocin jiha da ƙananan hukumomi.
Kuma a yanzu jihohi 23 cikin 50 na Amurkar gwamnoninsu 'yan Democrat ne.
Sannan wasu daga cikin manufofin Trump kamar korar baƙi mafi girma da ya ce zai yi na buƙatar goyon bayan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi saboda haka shirin zai iya gamuwa da ƙalubale.
Hukumomin birane da jihohi da dama sun ayyana kansu a matsayin mafakar baƙi - inda suna nuna ƙin amincewarsu da gwamnatin tarayya.
4. Aikin gwamnati na Amurka
A lokacin mulkin Trump na farko, 'yan Republican sun yi ƙorafin cewa ma'aikatan gwamnati sun hana su aiwatar da wasu manufofin shugaban.
Saboda haka a wajen ƙarshen gwamnatinsa, Mista Trump ya zartar da wasu dokoki da suka ba shi damar korar dubban ma'aikatan gwamnati ya maye gurbinsu da magoya bayansa.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, ya sauya wannan mataki, amma Shugaba Trump ya sake sanya irin wannan doka a ranarsa ta farko ta mulkinsa na biyu
Haka kuma ya umarci ma'aikatan tarayya da ke aiki a gida su koma ofisoshinsu.
Ƙungiyoyin masu ra'ayin riƙau da suke da alaƙa da Trump sun tattara bayanai na ƙwararrun da suke ganin za a naɗa su maye ma'akatan gwamnati.
Farfesa Peterson ya ce yana ganin Trump zai gamu da tirjiya sosai ta shari'a da siyasa da hukumomi da kuma ƙungiyoyin ƙwadago a kan wannan shiri.
5. Ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai
Ga alama Mista Trump zai iya ci gaba da fuskantar ƙalubale da suka daga kafafaen yaɗa labarai masu sassaucin ra'ayi da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a na Amurka.
Gamayyar ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'Adama ta Amurka - ACLU - wadda ke da mambobi 1.7 ta ce za ta yi ƙoƙarin hana wasu daga cikin manufofin Trump ɗin misali kan baƙi - ta ce zai raba wasu iyalai.
A ranar Litinin ACLU da sauran ƙungiyoyi suka shigar da ƙara inda suke ƙalubalantar shirin Trump ɗin na hana bayar da 'yancin zama ɗan Amurka ga duk wanda aka haifa a Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu daga cikin masu hamayya da Trump sun damu da yadda wasu kafafen yaɗa labarai musamman bayan matakin Washington Post da LA Times na ƙin bayyana goyon bayansu ga 'yan takarar zaɓen shugaban ƙasa kamar yadda aka saba yi.
An sa ran dukkanin kafafen biyu su goyi bayan abokiyar hammayyar Trump wato Kamala Harris.
Mai jaridar Washington Post - attajiri Jeff Bezos ya ce sun yi hakan ne saboda mutane na ta ganin cewa kafafen yaɗa labarai sun ɗauki ɓangare.
A watan Disamba ya sanar da bayar da kuɗi domin bikin rantsar da Trump kuma ya yi liyafa da Trump a gidan shugaban na Mar-a-Lago a Florida.
Shi ma mai jaridar LA, Patrick Soon-Shiong, shi ma hamshaƙin attajiri ya ce yana tsoron cewa nuna goyon baya da wani ɗan takara ka iya ƙara raba kan ƙasar.
6. Goyon bayan jama'a
Farfesa Peterson yana ganin Trump zai yi la'akari da ra'ayin jama'a. Saboda ya ci zaɓe ne da ƙuri'ar jama'a kashi 49.9 - wato ƙasa da rabin yawan masu zaɓen - ya na gaba da Ms Harris da kashi 1.5 kawai.
Masanin ya ce wannan shi ne ɗaya daga cikin sakamako na kusa da kusa a zaben shugaban ƙasar.
Ya ƙara da cewa hakan ya nuna cewa ba kowa ba ne da ya zaɓi Trump yake goyon bayan manufofinsa duka.
Wannan ya sa masanin yake ganin zai sa gwamnatin Trump ta sassauta wasu manufofinta domin ɗorewar farin jininsa da kuma tabbatar da ganin jam'iyyarsu ta Republican ta yi nasara a zaɓen rabin wa'adi na 2026.

Asalin hoton, Getty
Haka kuma wasu masu fashin baƙi sun ce alƙawuran da Trump ya yi na bunƙasa tattalin arziƙi da rage tashin farashi ka iya cin karo da wasu tsare-tsarensa kamar sanya haraji da kuma batun korar baƙi.
Masanin tattalin arziƙ John Cochrane ( na Cibiyar Hoover) ya ce babban abin dubawa ko tambaya shi ne ta yaya Trump zai iya wanyewa a tsakanin damuwar 'yankasuwar da ke cikin haɗakar da ta zaɓe shi da kuma masu tsattsauran kishin ƙasa da suka mayar da hankali kan batutuwa irin su tsare kan iyaka don hana shigar baƙi da kuma hamayya da China.
Mista Cochrane ya ce, ''wannan tabbas a fili take dukkanin ɓangarorin ba za su samu abin da suke so ba.''
''Wannan shi ne babban batu, kuma shi ne ya sa ba za mu iya hasashen abin da zai faru ba."











