Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko zai yiwu a hana yara amfani da shafukan sada zumunta?
- Marubuci, Tiffanie Turnbull
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sydney
- Lokacin karatu: Minti 6
Ya ɗauki Isobel mai shekaru 13 ƙasa da mintuna biyar kawai ta kauce wa dokar haramta yara amfani da shafukan sada zumunta ta ƙasar Australia, wadda ake cewa a ita ce mafi ƙarfi a duniya wacce ke hana yara amfani da kafofin sada zumunta.
Isobel ta samu sanarwar gargaɗi daga Snapchat, ɗaya daga cikin dandalin sada zumunta 10 da dokar ta shafa, inda aka bayyana mata cewa za a cire ta daga dandalin idan ba ta iya tabbatar da cewa ta wuce shekara 16 a duniya ba.
"Kawai sai na ɗauko hoton mahaifiyata, na saka shi a gaban kyamara, sai ya tabbatar da shekaruna, shi ke nan na samu damar shiga Snapchat." in ji Isobel.
"Akwai ma wanda na ji ya yi amfani da hoton fuskar fitacciyar mawaƙiya Beyonce," kamar yadda ta bayyana.
Daga ranar 10 ga Disamba ne dokar haramcin amfani da shafukan sada zumunta ga yara ƴan ƙasa da shekara a 16 Australia ta fara aiki.
Gwamnatin Austiralia ta ce wannan haramcin – wanda shi ne na farko a duniya kuma iyaye da yawa ke goyon bayansa – an tsara shi ne don kare yara daga abun da zai iya cutar da su da sauran abubuwa kamar cin zarafi ta intanet da ƙoƙarin jefa su cikin miyagun abubuwa, da kuma taimaka musu su samu bacci mai kyau tare da inganta lafiyar jiki da ta kwakwalwa, kamar yadda aka bayyana.
Duk da cewa mahaifiyar Isobel, Mel, ta ba 'yarta damar amfani da TikTok da Snapchat a ƙarƙashin kulawa sosai, tana fatan haramcin zai taimaka wa iyaye kamar ta wajen shimfiɗa iyakoki.
Amma yanzu wannan fata ta fara raguwa, saboda masana da yara kansu suna nuna damuwa kan ko dokar za ta yi tasiri da kuma ko za a bi dokar kuma ana bibiyar ta sosai a duniya.
Ta yaya za a aiwatar da dokar?
A ƙarkashin wannan doka, wadda aka sanar a watan Nuwamban 2024, ba za a hukunta iyaye ko yara saboda amfani da kafofin sada zumunta ba.
Sai dai dandalin shafin zumuntar ne zai ɗauki "matakan da suka dace" don tabbatar da cewa masu amfani da shi sun kai aƙalla shekara 16, in ba haka ba za su iya fuskantar tarar da za ta iya kaiwa ta dala miliyan 49.5 ga manyan laifuka.
Wani gwaji da da aka gudanar ya nuna cewa matakan da ake shirin ɗauka wurin tantance shekarun masu amfani da shafukan za su yi aiki – amma babu wanda yake cikakke, kuma duk suna da nasu raunin.
Amfani da katin shaida (ID) shi ne hanya mafi girma, amma hakan yana buƙatar mai amfani ya miƙa muhimman takardunsa.
Akwai kuma hanyoyin hasashen shekaru daga yadda mutum ke amfani da intanet da na'uarar tantance fuska duk da cewa za su iya yin kuskure, wanda hakan ya sa ba za a iya dogara da su wajen tantance matasa ba.
Tun lokacin da aka sanar da ƙaƙaba dokar, shawarwari kan yadda za a iya kauce wa dokar suka cika shafukan sada zumunta.
Masu goyon bayan tsarin tantance shekaru suna cewa akwai na'uarar da za ta iya hana wannan kaucewar. Hoto ɗaya dai irin wanda Isobel ta ce ta yi amfani da shi bai kamata a ce an iya amfani da shi wajen kauce wa dokar ba.
BBC ta tambayi Snapchat game da haka, kuma mai magana da yawun kamfanin ya ce sun daɗe suna nuna damuwa kan "tangarɗar na'ura " wajen aiwatar da dokar haramcin: "Wannan ma na daga ciki."
Luc Delany, wani jami'i a K-ID – kamfanin da ke gudanar da tantance shekaru a madadin Snapchat – ya ce:
"Wannan fa wata gasa ce ta kullum, domin tabbatar da cewa matakan kariya suna ƙara inganta, kusan kullum."
Isobel, wadda ta ji daɗin yadda ta yi nasarar kauce wa dokar tana da yaƙinin cewa dokar ba za ta yi aiki ba.
"In har aka rufe min shafina, zan samu wata sabuwar manhaja kawai na yi amfani da ita," in ji ta.
Mel ta ce wannan batu ne da za a tattauna, amma ta nuna damuwa kan yadda yara ke shirin komawa wasu sabbin manhajoji idan har aka rufe musu kafofin sada zumuntarsu.
Stephen Scheeler, wanda ya jagoranci Facebook a Australia da New Zealand daga 2013 zuwa 2017, na daga cikin waɗanda ke cewa dandalin sada zumunta na iya kokarin lalata dokar a boye, kuma ba sa tsoron tarar da za a yi musu.
Facebook, misali, na samun irin wannan kuɗi a duniya cikin kasa da sa'a biyu.
"Wannan kamar tikitin ajiye mota ne kawai," in ji shi.
Sannan akwai batutuwan shari'a da ba za a rasa ba. Matasa biyu ma sun riga sun shigar da ƙara a babbar kotun ƙasar, suna zargin cewa dokar ta saɓa wa kundin tsarin mulki.
Kamfanin Alphabet, mammallakin YouTube da Google, shi ma yana tunanin ƙalubalantar dokar. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam da wasu ƙwararrun lauyoyi sun nuna rashin amincewarsu, su ma.
Shin wannan dokar za ta rage illa?
Baya ga tambayar ko za a iya aiwatar da ita, mutane da dama har yanzu suna tambaya: ko dokar za ta rage illa ko kuma ya kamata a yi ta kuwa?
Da farko, akwai damuwa cewa wannan doka na tura yara zuwa amfani da sashen intanet na ɓoye.
Zai iya zama ɓangaren gyam, wurin da ake yawan tasiri ko ɗaure hankalin yara, amma dokar ba ta shafe su ba.
Haka kuma, yara har yanzu za su iya shiga wasu manhajoji kamar kamar TikTok da YouTube ba tare da buɗe shafi ƙunshe da bayanasu ba, abin da zai iya zama mafi haɗari saboda babu tacewa a abubuwan da ake nunawa ko tallace-tallace, alhali a kan ɓangaren yara ana taƙaita irin waɗannan abubuwa.
Ko da yake ana yawan sukar manyan kamfanonin manhajoji kan yadda suke kula da abubuwan da ake ɗorawa ko nunawa, kaɗan ne ke musun cewa suna yin hakan fiye da ƙananan dandali.
Facebook, misali, na da tsarin da ke ankararwa idan wani babba yana yawan tura saƙonni ga yara.
Kimiyyar da ke nazarin hulɗar kafofin sada zumunta da lafiyar jama'a tana da rikitarwa, kuma har yanzu tana ci gaba da canzawa.
Duk da cewa akwai binciken da ke danganta su da mummunan tasiri, akwai kuma hujjoji da ke nuna cewa kafofin sada zumunta na iya zama wata hanyar tallafi ga wasu yara musamman waɗanda ke cikin ƙungiyoyin ƴan luwadi da dangoginsu, wato LGBTQ+ da masu buƙatu na musamman (neurodivergent), ko kuma waɗanda ke zaune a yankunan karkara.
Mutane da dama sun ba da shawarar cewa ya kamata a mayar da hankali wajen tilasta wa manyan kamfanonin dandalin sada zumunta su ƙara tsaurara binciken munanan abubuwan da ke ƙunshe a wadannan shafuka.