Abin da ya sa Australia ta haramta wa matasa 'yan 16 amfani da shafukan sada zumunta

Lokacin karatu: Minti 6

Daga ranar 10 ga watan Disamba dole ne kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da ganin matasa 'yan tsakanin shekara 16 a Australia, ba sa buɗe shafikansu kuma su rufe dukkanin shafukan matasan da suke da su yanzu.

Gwamnatin ta ce haramcin wanda shi ne na farko a duniya ta yi ta ne domin rage irin haɗarin da yara za su iya fuskanta a shafukan sada zumunta, wanda zai iya cutar da lafiya da rayuwarsu.

Wani bincike da gwamnati ta yi a farkon shekaran nan, ya nuna cewa kashi 96 cikin ɗari na yara masu shekara 10-15 suna amfani da shafukan sada zumunta, kuma hatta bakwai daga cikin 10 na haɗuwa da abubuwa masu cutarwa da sauyin ɗabi'u.

Wannan ɗabi'a ta kama daga bidiyo na abubuwa marassa kyau ga rayuwarsu har ma da kashe kai.

Darektan ƙungiyar masu raji ta ganin an ƙara yawan shekarun masu amfani da shafukan sada zumunta a Australia, Greg Attwells, ya gaya wa BBC cewa, wannan ba haramci ba ne, mataki ne na ganin yara sun san kansu kafin duniya ta sansu.

Waɗanne shafuka ne haramcin ya shafa?

Zuwa yanzu gwamnatin Australia ta sanar da shafuka tara da dokar haramcin za ta shafa, waɗanda suka haɗa da: Facebook, da Instagram, da Snapchat, da Threads, da TikTok, da X, da YouTube, da Reddit, da kuma Kick.

Haka kuma gwamnatin na fuskantar matsin lamba a kan dokar ta haɗa har da shafukan wasan kwanfuta na intanet.

Saboda fargabar dokar kar ta haɗa da su shafukan irin waɗannan wasanni kamar Roblox da Discord, sun ɓullo da tsarin tantance shekarun masu shiga shafin, don tabbatar da ganin ƙananan yara ba sa amfani da shafin.

Gwamnatin ta ce za ta sake duba jerin shafukan da haramcin ya shafa, domin ƙarawa ko rage su.

Dokar ba ta shafi shafukan YouTube Kids, da Google Classroom, da WhatsApp, sannan yara za su iya shiga shafin YouTube, wanda ba ya buƙatar lalle sai yara yana da rijista da shafin kafin ya shiga.

Ta yaya za a aiwatar da dokar?

Ba za a hukunta iyaye da yara a kan saɓa dokar ba - kamfanonin shafukan ne ke da alhakin aiwatar da dokar, kuma za a ci su tarar da ta kai har ta dala 49.5 a kan laifin da ya yi tsanani ko aka yi yi ta yi.

Gwamnati ta ce dole ne kamfanonin su ɗauki matakan da suka dace don hana yara shiga shafukansu.

Gwamnatin ta buƙaci kamfanonin shafukan su ɗauki matakai daban-daban na ganin sun aiwatar da dokar.

Ta ce, kuma kada shafukan su dogara ga tsarin da masu shiga shafi za su sanar da shekarunsu ko kuma iyaye su tsaya wa 'ya'yansu don yin rijistar shiga shafin.

Kamfanin Meta, wanda ya mallaki Facebook, da Instagram da Threads, ya ce daga ranar 4 ga watan Disamba, zai fara rufe shafukan yara 'yan shekara goma sha.

Sauran shafukan da dokar ta shafa ba su bayyana yadda za su aiwatar da dokar ba.

Dokar za ta yi aiki kuwa?

Ba tare da sanin ainahin matakin da kamfanonin za su bi ba wajen aiwatar da dokar, abu ne mawuyaci a ce shafukan za su iya aiwatar da dokar sosai da sosai.

Amma dai ana nuna damuwa cewa fasahar tantance shekarun masu shiga shafi, za ta iya kuskuren hawa wanda dokar ba ta shafa ba, ta kuma kasa gano wasu yaran da ya kamata dokar ta shafa.

Ana kuma nuna damuwa kan ko tarar da aka ɗora, ta kai yadda ya kamata.

Masu suka na cewa, ko da an aiwatar da dokar yadda ya kamata ba lalle a rage illar da shafukan da suke yi wa yaran.

Shafukan haɗa masoya da na wasan kwamfuta ba sa cikin waɗanda dokar ta shafa, haka su ma AI chatbots, waɗanda ake zargin suna sa yara kashe kansu da hirar batsa da ƙananan yara

Wasu masu sukan dokar kuma na ganin cewa yara matasa da suka dogara ga shafukan sada zumunta a matsayin hanyar mu'amulla da sauran al'umma za su kasance cikin kaɗaici.

Suka ce kamata ya yi a ilmantar da yaran a kan yadda za su yi amfani da shafukan ta hanyoyin da za su ci moriya.

Ministar sadarwa ta ƙasar ta Australia, Annika Wells, ta yarda cewa ba lalle ba ne dokar ta yi tasiri sosai.

Ko akwai fargaba kan kare bayanan mutum?

Haka kuma masu ja da wannan doka suna nuna fargaba kan tarin bayanan jama'a da za a tattara a adana wajen aiwatar da wannan doka , da kuma yuwuwar sakaci wajen adana bayanan.

Ita ma Australia, kamar sauran ƙasashen duniya, a 'yan shekarun nan ta yi fama da tarin matsaloli dangane da saɓa dokokin kare bayanan jama'a, ciki har da yadda aka saci bayanai ko kuma aka sayar ko aka wallafa.

To amma duk da haka gwamnati ta nuna cewa akwai ƙwararan matakai na kariya ga bayanan jama'a.

Daga ciki har da cewa ba za a yi amfani da bayanan ba illa wajen tantance shekaru, kuma dole ne a lalata bayanan da an kammala abin da ake so a yi da su.

Sannan kuma akwai hukunci mai tsanani ga duk wanda ya yi sakaci ko saɓa dokar kare bayanan.

Yaya kamfanonin shafukan suka ji da dokar?

Kamfanonin shafukan sada zumunta sun yi mamaki da jin dokar haramcin a lokacin da aka sanar a watan Nuwamba na 2024.

Sun ce abu ne mai wuya a iya aiwatar da ita, da kuma sauƙin zagaye mata baya ga tarin lokaci da za ta ci na masu amfani da shafukan, bugu da ƙari suka ce tana tattare da haɗari ga sirrin bayanan jama'a.

Haka kuma sun nuna cewa dokar za ta iya sa yara su riƙa shiga miyagun hanyoyi na intanet, da kuma hana matasa mu'amulla.

Snap - kamfanin da ya mallaki Snapchat - da kuma YouTube, sun ce su ba kamfanoni ba ne na shafukan sada zumunta.

Babban kamfanin da ya mallaki YouTube wato Google, shi kuwa an ruwaito cewa har yanzu yana nazari kan ko ya ɗauki matakin shari'a, saboda shigar da YouTube ɗin cikin dokar.

Duk da cewa kamfanin Meta ya ce zai aiwatar da dokar da wuri, amma duk da haka ya ce dokar haramcin, za ta jefa matasa cikin yanayi na rashin tabbataccen tsaro kan manhajojin da suke amfani da su.

A lokacin wani zama na sauraren bayanai a majalisar dokoki da aka yi a watan Oktoba, kamfanonin TikTok da Snap, sun ce har yanzu suna suka ga dokar, amma duk da haka za su aiwatar da ita.

Shi kuwa, Kick, kamfani ɗaya tilo na Australia da dokar ta shafa, ya ce zai ɓullo da matakai ne daban-daban, sannan zai ci gaba da ƙoƙarin tattaunawa da hukumomi kan dokar.

Jami'in wani daga cikin manyan kafanonin da wannan doka ta shafa, na fargabar cewa abin da Australia ta yi zai iya faɗaɗa zuwa sauran sassan duniya.

Ko wasu ƙasashen na da irin wannan doka?

Dokar ta Australia ta haramta amfani da shafukan sada zumunta a kan matasa 'yan shekara 16, abu ne na farko a duniya, kuma sauran ƙasashe za su zuba ido sosai su ga yadda za ta kasance.

An sanya dokoki da matakai daban-daban a wasu ƙassahen duniya domin taƙaita lokacin da yara ke amfani da shafukan sada zumunta da kalle-kalle a waya, don hana su ganin abin da zai iya cutar da su, to amma ba inda aka sanya dokar hana su amfani da shafukan sada zumunta gabaɗaya.

Me ya sa yara ke koƙarin kauce wa dokar?

Matasan da BBC ta tattauna da su, sun ce ai tuni suka fara buɗe wasu sababbin shafukan da shekaru na ƙarya, kafin dokar haramcin ta fara aiki - kodayake gwamnati ta yi gargaɗi ga kamfanonin shafukan, da cewa tana tsammanin ganin sun gano irin waɗannan shafuka sun kuma cire su.

Wasu matasan kuma suna sanar da wasu manhajojin na daban da za a iya komawa a karkata wajensu, ko kuma bayar da bayanai kan yadda za a iya kauce wa dokar.

Wasu matasan , har ma da wasu masu tasiri a shafukna sada zumunta, sun koma amfani da shafukan haɗaka da iyayensu.

Masu sharhi na hasashen za a samu ƙaruwar amfani da manhajar VPN - wadda ke ɓoye sunan ƙasar da mutum ke amfani da intanet - kamar yadda aka yi a Birtaniya bayan fara aiwatar da dokokin ƙayyade shekarun masu amfani da shafukan sada zumunta.

To amma Mista Attwell ya ce: ''E, har kullum yara suna da yadda suke iya kauce wa wasu hanyoyi. To amma hakan ba yana nufin ba za a yi dokar ba. Duk da haka muna da dokoki domin kare rayuwarsu."