Guehi na son zuwa Madrid, Man City da Man Utd na hammaya kan Anderson

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Manchester City da Norway Oscar Bobb zai iya komawa taka leda a Borussia Dortmund a matsayin aro har zuwa ƙarshen kaka, yayin da Crystal Palace da Bournemouth da Newcastle ke ribibin ɗanwasan mai shekara 22. (Mail - subscription required)
Liverpool har yanzu tana son don ɗauko ɗanwasan baya na Crystal Palace da Ingila Marc Guehi a bazara, amma ya fi son ya tafi Real Madrid, da ke son ɗanwasan mai shekara 25. (AS - in Spanish).
Juventus na son ɗanwasan tsakiya na West Ham da Argentina mai shekara 31 Guido Rodriguez. (Sky in Italy)
Tottenham na nazarin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Monaco da Faransa mai shekara 23 Maghnes Akliouche a Janairu. (Mail - subscription required)
Roma na son ɗauko sabon ɗanwasan baya kuma tana harin wasu ƴanwasan gasar Premier biyu da suka haɗa ɗanwasan Tottenham mai shekara 23 da Radu Dragusin da kuma ɗanwasan baya na Chelsea da Faransa mai shekara 27 Axel Disasi. (Sky in Italy)
Juventus ba ta tabbas kan ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Italiya Sandro Tonali da take ɗauko wa a Janairu. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester City na son shan gaban Manchester United kan ɗanwasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila, Elliot Anderson, 23. (Teamtalk)
Fenerbahce ta taya ɗanwasan gaba na AC Milan da Faransa Christopher Nkunku. (Calciomercato - in Italian)
Real Madrid ta shiga hamayya kan ɗanwasan baya na Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck, mai shekara 26, inda Dortmund ta sa farashinsa kan fam miliyan 60. (Sport - in Spanish)
Juventus na tunanin dawo da ɗanwasan gaba na Liverpool da Italiya Federico Chiesa mai shekara 28. (La Gazzetta dello Sport - in Italian).










