Watakil Rashford ya koma Man U bayan korar Amorim, Juventus na zawarcin Chiesa

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford
Lokacin karatu: Minti 3

Korar da aka yi wa kocin Manchester United, Ruben Amorim za ta iya ba dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, wanda ke zaman aro a Barcelona, hanyar komawa Old Trafford.(Mirror)

Watakila Oliver Glasner na cikin wadanda Man U ke so su maye gurbin Amorim da ta kora.

Shugabanin United na kaunar Glasner, dan kasar Australia mai shekara 51,wanda kwantaraginsa da Crystal Palace zai kare a bazara (Telegraph)

Ita ma Fulham na jiran Manchester United ta tuntube ta kan kocinta, Marco Silva, dan kasar Portugugal. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20 da dan wasan Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, da kuma dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekara 24, duk sun nuna alamun barin Manchester United a watan Janairu idan Amorim ya zauna. (Mail)

Juventus ta fara tattaunawa da Liverpool kan batun bada aron Federico Chiesa, inda dan wasan na Italiya mai shekara 28 ya nuna alamun yana son ya koma kungiyar ta Seria A inda ya shafe kaka biyu tsakanin 2022-2024. (La Gazzetta dello Sport)

Bournemouth ta shirya biyan Yuro miliyan 40 don siyan dan wasan Stuttgart da Jamus Jamie Leweling a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Ghana Antoine Semenyo mai shekaru 25, wanda ke dab da komawa Manchester City, amma kungiyar ta Bundesliga ta yi watsi da tayin na Cherries.(Sky Sports )

Dole Chelsea ta dauki mataki cikin gaggawa idan tana son ta sayi dan wasan Rennes Jeremy Jacquet, mai shekara 20, saboda Liverpool da Arsenal da Real Madrid da kuma Manchester United duk suna sha'awar dan wasan na Faransa (Teamtalk)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barcelona na son Al-Hilal ta bada aron dan wasan Portugal Joao Cancelo, mai shekara 31, yayin da Inter Milan ke zawarcinsa. (La Gazzetta dello Sport)

Crystal Palace na shirin fafatawa da West Ham don siyan dan wasan Norway Jorgen Strand Larsen, mai shekara 25, daga Wolves. (Mail)

Tottenham ta tattauna da Santos kan kulla yarjejeniyar siyan dan wasan Brazil , Souza, mai shekara 19, wanda ke daukar hankalin Newcastle. (Teamtalk)

Dan wasan Ingila Callum Wilson, mai shekara 33, na tattaunawa da West Ham domin kawo karshen kwantiraginsa bayan ya shafe wata biyar a kungiyar (Athletic)

Tsohon kocin Wolves Gary O'Neil ya tattauna da Strasbourg kan zama sabon kocinta inda, kocin na kungiyar Faransa na yanzu Liam Rosenior ke cikin wadanda za su iya maye gurbin Enzo Maresca a Chelsea. (Athletic)

Dan wasan gaban Crystal Palace Romain Esse mai shekaru 20 a duniya ya shirya tsaf domin shafe sauran kakar wasan a matsayin aro a Coventry City.(Sky Sports)