Ko Jonathan zai iya zame wa Tinubu barazana a 2027?

Jonathan da Tinubu

Asalin hoton, EPA/Fadar shugaban Najeriya

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu da tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan
Lokacin karatu: Minti 5

Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

To amma cikin wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce ƴan Najeriya na sane da abin da ta kira ''rashin takaɓus'' a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya.

Goodluck ya mulki Najeriya a daidai lokacin da ƙungiyar Boko Haram ke kan ganiyarta wajen ƙaddamar hare-hare kan fararen hula.

A baya-bayan nan dai akwai ƙaruwar kiraye-kiraye tsakanin wasu ƴan jam'iyyar hamayya ta PDP kan tsohon shugaban ƙasar ya fito takara a zaɓen 2027.

Kira na baya-bayan nan ya fito ne daga tsohon ministan yaɗa labaran ƙasar, da wayar da kan jama'ar na zamanin mulkin Jonathan ɗin, Farfesa Jerry Gana.

Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta ce Jonathan ba tsaran takarar Tinubu ba ne, idan aka yi la'akari da yadda mulkinsa ya kasance a baya, da kuma yadda a yanzu ta ce shugaba Tinubu ya inganta ƙasar musamman a fannin tattalin arziki.

Sanarwar fadar shugaban ƙasar ta sa yan ƙasar da dama na ganin ko fadar shugaban ƙasar na fargabar takara da Jonathan ne.

Tinubu na fargabar Jonathan a 2027?

Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

Dakta Ibrahim Baba Shatambaya malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Usman Danfodi da ke Sokoto ya ce la'akari da sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar game da takarar tsohon shugaban ƙasar a iya cewa Shugaba Tinubu na fargabar fafatawa da Jonatahan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Abin da hakan ke nuna shi ne takarar Jonathan ka iya zama barazana ga Shugaba Tinubu da kuma jam'iyyarsa ta APC, saboda wasu abubuwa guda uku'', in ji shi.

  • Ƙima da martabarsa

Malamin jami'ar ya ce ƙima da halin dattaku da Jonathan ke da shi a idanun ƴan Najeriya ne Shugaba Tinubu ke fargaba.

"A zaɓen 2015 lokacin da alƙaluma suka nuna cewa Buhari ne ya yi nasara a zaɓen, kwatsam sai Goodluck Jonatah ya kira shi (Buhari) a waya tare da taya shi murnar lashe zaɓe'', in ji Shatambaya.

Malamin jami'ar ya ce wannan abu da Jonathan ya yi ya janyo masa ƙima da martaba a idanun ƴan Najeriya.

''Don haka fadar shugaban ƙasa ke kallon sa a matsayin babbar barazana ga Shugaba Tinubu a zaɓen 2027'', in ji shi.

Jonathan ne mutum na farko da ya amince da shan kaye a siyasar Najeriya, inda ake ganin ƴan siyasa na kallon zaɓe a matsayin mataki na a mutu ko a yi rai.

  • Manyan ƴantakar biyu daga kudu

Dakta Shatambaya ya ce wani dalilin da zai sa Tinubu ya yi fargabar fafatawa da Jonatahan a zaɓen 2027 shi ne kasancewar sun fito daga yanki ɗaya, wato kudancin ƙasar.

''Ka san siyasar Najeriya, ɓangaranci da addini da ƙabilanci na da matuƙar tasiri, don haka fadar shugaban ƙasar ke ganin idan har Jonathan ya tsaya takara a 2027, to lallai ƙuri'un kudancin ƙasar za su rabu gida biyu, don haka idan aka samu wani fitacce daga arewa a jam'iyyar hamayya zai iya lashe zaɓe cikin sauƙi'', in ji shi.

Arewacin Najeriya ne yankin da ya fi yawan ƙuri'u fiye da kudancin ƙasar.

  • Rashin raina abokin adawa

A fagen siyasa ba a raina abokin hamayya ko yaya yake, a cewar Dakta Ibrahim Shatambaya.

''Wannan ma zai iya zama dalilin da ya sa Tinubu ba ya son takara da Jonathan a 2027'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa shi mai mulki, ba ya raina abokin adawarsa komai ƙanƙantarsa, balle kuma Jonathan da ya kai matakin shugaban ƙasa.

Me ya sa ake kiran Jonathan ya yi takara?

Toshon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Toshon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Dakta Shatambaya ya ce kiraye-kirayen takara da ake yi wa tsohon shugaban ƙasar ba ya rasa nasaba da irin halin dattaku da ya nuna a zaɓen da ya sha kaye a hannun tsohon shugaban ƙasar Marigayi Muhammadu Buhari.

''A lokacin wasu daga cikin muƙarraban gwamnatinsa sun buƙaci a yi amfani a ƙarfa-ƙarfa wajen ƙwace zaɓe, amma sai ya ƙi, ya kuma haƙura tare da bayar da mulki'', in ji shi.

''Inda ya ga dama a lokacin zai iya yin yunƙurin ƙarfa-ƙarfa, amma sai haƙura '', in ji masanin kimiyyar siyasar.

Wannan abu ya janyo masa farin jini ba ga Najeriya kaɗai ma har ma ƙasashen waje, a cewar masanin kimiyyar siyasar.

''Tun bayan saukar sa daga mulki, ya samu martabar da ake tura shi ƙasashen Afirka domin ƙarfafa dimokraɗiyya, saboda abin da ya yi'', in ji shi.

Masanin kimiyyar siyasar ya ce wannan ƙimar ce ta sa wasu ƴan jam'iyyar PDP da ma wasu ƴan Najeriya ke ƙarfafa kiraye-kirayen takatar shugaban ƙasar.

Goodluck Jonathan ya mulki Najeriya daga 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Umaru Musa Yar'adua, kafin ya ci zaɓe a 2011 a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Haka kuma ya sake tsayawa takara a zaɓen 2015 domin neman wa'adin mulki na biyu, sai dai ya sha kaye a hannun tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

Babu wanda muka keɓe wa takara shi kaɗai - PDP

Alamar jam'iyyar PDP

Asalin hoton, PDP

Tuni dai jam'iyar PDP ta sanar wa keɓe wa kudancin ƙasar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, wani abu da wasu ke ganin tamkar share hanya ne ga takarar Joathan.

To sai dai ta ce ba ta keɓe wa wani mutum ɗaya takarar shugaban ƙasar a 2027 ba.

Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce tana da wadatattun mutanen da za su iya tsaya mata takara a zaɓen mai zuwa.

''Muna da mutane masu yawa da suka cancanta, ciki har da jajirtattun gwamnonin da za su iya yin takarar shugaban ƙasa a 2027'', a cewar sanarwar.