Goodluck Jonathan: 'An bar baya da ƙura' bayan saya masa fom da wasu ƴan arewa suka yi

.

A ranar Litinin, 9 ga watan Mayun 2022 ne wasu ƙungiyoyin arewa da wata ƙungiyar al'ummar Fulani ta jagoranta suka saya wa Goodluck Jonathan fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC.

Wannan lamari ya kasance babban abin mamaki da ɗaure kai ga ƴan Najeriya ganin cewa Jonathan shi ne babban ɗan takara na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2015 kuma shi ya yi takarar shugaban ƙasa da Muhammadu Buhari.

Duk da cewa a kwanakin baya ana ta ce-ce-ku-ce da yaɗa jita-jita musamman a shafukan sada zumunta kan batun komawar Jonathan APC sakamakon yadda aka ga yana ɗasawa da Shugaba Buhari, amma duk da haka jama'a da dama suna ganin ba abu bane mai yiwuwa ba kuma ba abu bane wanda hankali zai ɗauka a ce Jonathan ya koma APC.

Dalili kuwa shi ne a 2014, Jam'iyyar APC da Jonathan ta yi kamfe inda ta caccaki gwamnatinsa da yi masa kaca-kaca, shi yasa jama'a ke ganin bai kamata a ce duk da irin abubuwan da aka yi wa Jonathan ba ya koma APC kuma ko ya koma bai kamata a karɓe shi ba.

Sai dai kwatsam a ranar Litinin aka shiga ruɗani bayan waɗannan ƙungiyoyi suka saya wa Jonathan fom ɗin takarar shugaban ƙasa naira na gugar naira har miliyan 100.

Jama'a da dama a shafukan sada zumunta sun ta tofa albarkacin bakinsu inda wasu suka yi ta sukar wannan lamari wasu kuma suka yi maraba da shi.

Me jama'a ke cewa kan saya wa Jonathan fom

..

Kamar yadda jama'a da dama ke tofa albarkacin bakinsu, Abel Adams ya gargaɗi Jonathan kan kada ya yarda ya jawo shi a ɓata masa suna ta hanyar yin takara inda ya ce ƴan siyasa sun riga sun ɓata ƙasarsu.

..

Buharee Baba kuma cewa ya yi addu'ar wasu ƴan Najeriya ce aka karɓa da suke cewa a mayar da su inda aka same su a baya ma'ana mulkin Jonathan na 2015.

.

Shi kuma Nasiru Aliyu Bukkuyum fatan alkhairi ya yi wa Jonathan tare da yi wa Najeriya fatan samun shugaba nagari a 2023.

..

A nata ɓangaren, Zahra Mansur cewa ta yi ana wasa da hankalin jama'a inda ta ce har lalacewar ta kai a dawo da waɗanda ake zargi da illata Najeriya su dawo su ɗora daga inda suka tsaya.

Me Jonathan ya ce dangane da saya masa fom?

Jim kaɗan bayan sayen fom ɗin da ƙungiyoyin suka yi, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi watsi da fom din tsayawa takarar shugaban kasa da aka siya masa ba tare da tuntubarsa ba.

A wata sanarwar da mai magana da yawun Mista Jonathan ya fitar, ya ce ''ba mu da masaniya, ba kuma a tuntube mu ba kafin yanke hukuncin sayan fom din.''

"Muna son shaida wa mutane cewa idan tsohon shugaban kasa na son tsayawa takarar, zai sanar da al'umma, ba zai yi danwaken zagaye ba," in ji sanarwar.