Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya samu Isra'ila da aikata kisan ƙare dangi
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
- Lokacin karatu: Minti 5
Rahoton yana ɗauke da abubuwa masu yawan gaske da ke nuni da hujjojin da rahoton ya ce Isra'ila na aikata laifukan kisan ƙare dangi.
Rahoton ya ce Isra'ila ta karya dokokin kisan ƙare dangi na duniya da aka kafa a 1948 lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta samu.
Kalmar ƙare dangi dai ta fara samun karɓuwar sakamakon kisan ƙare dangin da ƴan Nazi suka yi wa Yahudawa a Jamus.
Isra'ila ta yi watsi da dukkannin zarge-zargen da ake yi mata cewa abubuwan da take yi a Gaza sun karya dokokin ƙasa da ƙasa na yaƙi da na ayyukan jinƙai.
Ta kuma kare abin da take yi a Gaza a matsayin kare kai da kuma ƙoƙarin sakin mutanenta da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda ake kyautata zaton har yanzu mutum 20 daga ciki na da rai.
Har wayau, Isra'ila ta yi watsi da rahoton ta kuma bayyana shi da wata farfagandar ƙin Yahudawa da Hamas ta kitsa.
Kwamitin bincike da hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa ne ya tattara rahoton.
Isra'ila da Amurka sun ƙaurace wa majalisar bisa cewa yana nuna musu rashin adalci.
To amma duk da haka abubuwan da rahoton ya ƙunsa za su ƙara yawan sukan da ƙasashen duniya ke yi wa Isra'ila, wanda kuma yake zuwa daga ƙawayen Isra'ilar na Turai da ma ƙasashen Larabawa da suka gyara alaƙarsu da ita a yarjejeniyar Abraham Accords.
Mako mai zuwa a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a New York na Amurka, ƙasashe kamar Burtaniya da Faransa da Australia da Canada da sauransu za su bayyana amincewarsu ga kasancewar Palasdinu ƙasa mai cin gashin kanta.
Sai dai ana ganin babu wani abu da hakan zai sauya. Zai sauya muhawarar da ake yi dangane da yadda rikici tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa zai ƙare wanda ya fara shekaru fiye da 100 lokacin da Yahudawa masu rajin kafa ƙasar Yahudawa daga Turai suka koma yankin Falasɗinawa da zama.
Benjamin Netanyahu, ya yi alawadai da ayyana Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kai wani abu da ya ce tamkar sakayya ne ga Hamas.
Ya ce Falasɗinawa ba za su taɓa samun ƴancin kai ba a matasayin ƙasar Falasɗinawa saboda hakan zai jefa ƴan Isra'ila a cikin haɗari.
Isra'ilawa masu tsatstsauran ra'ayi sun yi amannar cewa ubangiji ne ya bai wa Yahaudawa yankin su kaɗai.
Yarjejeniyar 1948 ce ta fassara kalmar ƙare dangi, a matsayin wani shiri na lalata wani ɓangare ko kuma baƙi ɗayan wata al'umma saboda addininisu ko ƙabilarsu ko jinsunsu - kamar abin da ke faruwa Falasɗinawa a Gaza.
Rahotan ya yi cikakken bayani dangane da abubuwan da aka yi a Gaza da a gidajen yari.
Ɗaya daga cikin zarge-zargen shi ne Isra'ila na kai wa fararen hula hari da bisa doka ya kamata ta kare da kuma tursasa wa mutane ta hanyar rashin tausayi da ke sa su mutuwa da suka haɗa da amfani da yunwa da ƙishirya da rashin magani.
Bugu da ƙari rahoton ya kuma yi bayani filla-filla dangane da tilasta Falasɗinawa barin matsugunansu kamar abin da ke faruwa yanzu haka a Gaza, inda dakarun IDF suka umarci dukkan fararen hula da su koma zuwa kudanci.
Ana hasashen al'amarin ya shafi mutum kimanin miliyan ɗaya, kuma hare-haren na Isra'ila na ci gaba da wakana kamar hare-hare ta sama da lalata gine-gine da suka haɗa da gine-gine masu tsayi da suka zama alamun birnin Gaza waɗanda IDF ta bayyana da maɓoyar Hamas.
Rahoton ya kuma ce Isra'ila ta ƙaƙaba wasu hanyoyin na hana mata haihuwa wanda hakan ke nufin ɗaura yaƙi da haife-haifen al'umma a Gaza wanda aka ce ya lalata tayi kimanin 4000 da ruwan maniyyi 1000 da ma ƙwayayen da ba a ƙyanƙyashe ba.
Rahoton ya kuma zaƙulo sunayen wasu jami'an Isra'ila guda uku da hannu a aikata laifukan na ƙare dangi.
Mutanen sun haɗa da Yoav Gallant, tsohon ministan tsaro na Isra'ila wanda ya faɗi cewa "Isra'ila na yaƙar dabbobi." Kamar Netanyahu, Gallant na fuskantar sammacin kamu daga kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya.
Netanyahu shi ma ana zargin sa da tunzurawa ta hanyar kwatanta yaƙin Gaza da labarin yaƙin da Yahudawa suka yi da abokan gabarsu da ake kira da Amalek.
A littafin Bible, ubangiji ya shaida wa Yahaudawa da su kawo ƙarshen mazaje da mata da ƙananan yara na Amalek da kuma abubuwan da suka mallaka da ma dabbobinsu.
Jami'in na uku da rahoton ya bayyana shi ne shugaba Isaac Herzog wanda a makon farko na yaƙin ya soki Falasɗinawa bisa rashin yaƙar Hamas. Ya faɗi cewa a ranar 13 ga watan Okotban 2023, "dukkannin ƴan ƙasar ne suke da laifi."
Bisa doka, abu ne mai wuya a iya tabbatar da laifin kisan ƙare dangi. Mutanen da suka kafa yarjejeniyar da ta haramta kisan ƙare dangi da ma'anarta kamar yadda kotun ICJ ta fassara, sun sanya dokoki masu tsauri na tabbatar da hakan.
A kotun duniya da ke Hague , Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila cewa ta aikata laifukan kisan ƙare dangi a kan Falasiɗinawa. Wannan zai ɗauki shekaru masu dama kafin a yanke wannan hukunci.
To sai dai a daidai lokacin da yaƙin ke ci gaba a Gaza har ma yana ƙara ƙazanta saboda sabunta hare-hare da Isra'ila ke yi, rahoton na Majalsiar Ɗinkin Duniya zai ƙara raba kawunan ƙasashen duniya dangane da yaƙin.
A hannu ɗaya akwai ƙasashe da ke buƙatar gaggauta kawo ƙarshen kashe-kashen da lalata dukiya a Gaza da kuma yin alawadai da yunwar da Isra'ila ta gada wa Falasɗinawa sakamakon yaƙin.
Ƙasashen sun ƙunshi Burtaniya da Faransa.
A ɗaya hannun kuma akwai Isra'ila da Amurka. Gwamnatin shugaba Donald trump na ci gaba da samar da tallafin soji da goyon baya ta fuskacin diflomasiyya ga Isra'ila wanda idan da babu su to ba za ta iya ci gaba da yaƙin da take yi a Gazar ba da ma hare-haren da take kai wa ƙasashen Gabas ta Tsakiya.