Wane ƙarfin iko Fafaroma ke da shi a faɗin duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Lebo Diseko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journaliste religieux de la BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Alƙaluman baya-bayan nan da Fadar Vatican ta fitar, sun nuna cewa mabiya ɗariƙar Katolika a faɗin duniya sun kai biliyan 1.4, kusan kashi 17 cikin 100 na al'ummar duniya.
Don haka ba abin mamaki ba ne ganin yadda marigayi Fafaroma Francis ya tara ɗimbin jama'a a lokacin da ya ziyarci yankin Asia a 2024, yayin da rabin al'ummar ƙasar Timor-Leste da ke kudancin Asiya suka halarci ziyarar tasa a ƙasar.
A shekarar da ta gabata, fiye da mutum miliyan guda ne suka jure wa zafin rana a filin jirgin saman Kinshasa, na ƙasar DR Kongo domin tarbarsa a lokacin ziyarar da ya kai ƙasashen Afirka biyu.
Damar tara irin wannan dandazon jama'ar da kuma yadda suka sadaukar da kai domin halartar tarukan, alama ce da ke nuna irin tasirin fafaroman da kuma Coci Katolika a faɗin duniya.
Ba mabiya ɗariƙar Katolika kawai fafaroma ke jagoranta ba, har da ƙasar Vatican City da gwamnatinta, da kuma Fadar Vatican
A ƙarƙashin dokokin duniya ana yi wa Fadar Fafaroma kallon wani yanki mai cin gashin kai.
A gefe guda fafaroman kan shiga wasu al'amuran duniya a hukumance, sannan yana da hulɗar jakadanci da ƙasashe 184 da ƙungiyar Tarayyar Turai.
Muƙamin fafaroma na shugaban gwamnati da kuma jagoran addini mai mabiya fiye da biliyan guda, ya sanya shi zama ɗaya daga cikin shugabannin addini mafiya tasiri a duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Fadar Vatican na da kujerar sa ido ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ya sa fadar ke da kujera a Majalisar, a matsayin ɗaya daga cikin mafiya tasiri wajen ɗaukar kowane irin mataki a duniya.
Duk da cewa ba shi da damar kaɗa ƙuri'a, amma zai iya shiga tattaunawa kuma ya yi tasiri a kowace irin tattaunawa.
A 2015, alal misali kafin sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi, Fafaroma Francis ya soki abin da ya kira ''rashin tausayi'' ga waɗanda suka fifita muradinsu fiye da ceton duniya.
Ana ganin sanya bakinsa cikin wannan batu, ya taimaka wajen sanya hannu kan yarjejeniyar musamman ga ƙasashen kudancin duniya da a baya suka nuna jan ƙafa.
A farkon shekarar 2024, Fadar Vatican ta hana tattaunawa kan ƴancin mata a taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, bayan da aka samu ƙaruwar matsalolin jinsi da jima'i.
Yarjejeniyoyin da ke kan ajanda sun ƙunshi tallafin kuɗi ga matan da ke kan gaba wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Fadar Vatican da Saudiyya da Rasha da Iran da kuma Masar sun nuna damuwa cewa sharuɗan yarjejeniyar za su ƙunshi sauya wa mata jinsi, inda suka buƙaci a cire saɗarar da ta shafi mata masu neman jinsi.
Duk da shan gagarumar suka, batun ya nuna irin tasiri da ƙarfin ikon da Cocin da ke shi wajen yin tasiri a lokacin ƙulla yarjejeniyar da kai-tsaye za ta yi tasiri kan rayukan miliyoyin mutane.
A shekarar 2014 an ga wani misalin tasirin fafaroman lokacin sasanci tsakanin Amurka da Cuba.
Shugabannin ƙasashen biyu na lokacin, Barack Obama da Raúl Castro sun fito bainar jama'a suka gode wa Fafaroma Francis saboda shiga tsakani da ya yi.
Fafaroma Francis ya rubuta wasiƙa ga duka shugabannin biyu sannan ya gana da su a asirce a fadarsa, domin tabbatar da sasancin.

Asalin hoton, Getty Images
To sai dai taimakon da cocin ta bayar a fannin gina dimokraɗiyya a gomman shekarun baya-bayan nan ake kallo a matsayin babbar gudunmowar da fadar ta bayar, a cewar Farfesa Daved Hollenbach na Cibiyar Addini da Zaman lafiya ta Berkley da ke Amurka.
Majalisar Vatican ta biyu a shekarun 1960 a lokacin da cocin ta sake nazarin koyarwarsa da sharuɗansa kan kare ƴancin ɗan'adam da ƴancin addini, wanda Hollens ya kira ''gagarumar nasara''.
Farfesan ya ba da misali da binciken masanin kimiyyar siyasa, Samuel Huntington, wanda a cewarsa "a lokacin Fafaroma John Paul II, har zuwa farkon Fafaroma Francis, Cocin Katolita na da tasiri mai ƙarfi a kashi uku cikin huɗu na ƙasashen da suka tashi daga mulkin kama karya zuwa dimokraɗiyya''.
Hollenbach ya ce, "an fara samun sauyin yanayi a Sifaniya da Portugal daga gwamnatin Franco da Salazar, sannan kuma ya bazu zuwa Latin Amurka, daga nan ya isa ƙasashe irin su Philippines da Koriya ta Kudu, inda kuma akwai mabiya Katolika masu yawa," in ji Hollenbach.
A cewarsa, ayyukan da Paparoma John Paul II taimaka wajen samar da hanyar tabbatar da dimokuradiyya a ƙasarsa ta Poland, sannan kuma ya ba da gudunmawa ga rugujewar Tarayyar Soviet da yaɗuwar dimokuradiyya a sassa daban-daban na tsohuwar daularta.

Asalin hoton, Getty Images
Tasiri a siyasance
To sai dai, ba koyaushe ba ne fadar Vatican ke nasara wajen yin tasiri ga shugabannin duniya.
Lokacin da Mataimakin Shugaban Amurka J.D. Vance – wanda mabiyin Katolika ne – ya yi amfani da hujjojin addini don tabbatar da manufofin gwamnatinsu kan shige da fice, Faparoma ya rubuta wata wasiƙa da a ciki yake tunatarwa cewa Yesu ma ɗan gudun hijira ne.
Sai dai wani Ba'amurken, Tom Homan, ya mayar masa da martani da cewa ''dole ne Fafaroma ya gyara Cocin Katolika.
A 2020, Shugaban Brazil na lokacin, Jair Bolsonaro ya soki Fafaroma bayan ya ba da shawarar kare dajin Amazon, yana mai cewa: "Fafaroma na iya zama ɗan Argentina, amma Ubangiji na Brazil ne," in ji Bolsonaro.
Tasirin zamantakewar Ikilisiya ya ragu a Turai, tare da nuna cewa ra'ayin mazan jiya game da ƴancin masu neman jinsi, (LGBT+) da ƴancin taƙaita haihuwa, da na zubar da ciki sun ƙare a ƙarni na 21.
Rashin amincewar Fafaroma Francis na barin mata su riƙe wasu muƙamai na shugabanci, kamar limamai da mataimakansu, wata alama ce ta wannan.

Asalin hoton, Reuters
A ƙasashen Latin Amurka, duk cocinan katolika na da matuƙar tasiri.
Cocin kan taka muhimmiyar rawa wajen samar da dokokin zubar da ciki a yankin, amma fiye da shekara 20, ƙasashe irin su Uruguay da Mexico da Argentina da kuma Colombia sun faɗaɗa amfani da tsarin wanda ya saɓa wa cocin katolika.
Haka kuma ƙaruwar mabiya ɗaliƙar evanjelika, ya riƙa barazana ga tasirin ikon cocin.
A Brazil, ƙasar da ke da yawan mabiya ɗariƙar Katolika a duniya, wasu manazarta sun yi hasashen cewa nan da shekaru biyar, ɗariƙar Katolika za ta rasa kambinta na kasancewa mafi rinjayen addini.
Bugu da ƙari, ci gaba da bayyanar da cin zarafin limamai - da kuma rawar da Coci ke takawa wajen ɓoye cin zarafin - sun zubar da kimarta a duniya.
Duk da haka, shugaban Cocin Katolika ya ci gaba da yin tasiri da wasu jagorori kaɗan a duniya suke da shi.
Wannan wani ɓangare ne saboda Fafaroma shi ne shugaban reshe mafi girma na Kiristanci kuma shugaban ƙasa.
Daga sukar shugabannin yaƙi a Sudan ta Kudu zuwa jajanta wa baƙin haure a sansanonin 'yan gudun hijira a Girka, ayyukan Fafaroman - da kuma rawar da Cocin Katolika - ke ci gaba da haifar da muhawara a duniya.











