Ra'ayi Riga: Kan hasashen saukar ruwan sama a Najeriya 07/03/2025
A shirinmu na wannan makon, mun duba tasiri da gargaɗin cewa ruwan sama zai yi saurin saka a wasu wuraren, sannan zai yi saurin ɗaukewa a wasu yankunan Najeriya, da kuma ko akwai wani shiri da manoma suke yi domin tunkarar wannan yanayin.
A kwanakin baya ne hukumar kula da yanayi ta Najeriya wato NIMET ta fitar da sanarwar hasashen yadda damina za ta kasance a bana. Hasashen ya nuna cewa ruwan saman zai sauka da yawa a Najeriya a bana, kuma akwai yiwuwar ruwan ya sauka kafin lokacin da aka saba a al'ada a wasu yankunan ƙasar.
Sai dai kuma hasashen ya ce za a samu jinkirin samun ruwan a wasu wurare, wasu jihohin kuma za su fuskanci yankewar ruwan da sauri.
Me wannan hasashen yake nufi ga manoma?
Yaya masana suke kallon lamarin?
Wane shiri manoma ya kamata su yi?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.







