Abin da ya sa muryarmu ke canjawa idan muna magana da harshen da ba namu ba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Giulia Granchi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
- Lokacin karatu: Minti 3
Idan kana iya yin yaruka fiye da ɗaya, tabbas za ka lura cewa sautin muryarka na bambanta idan kana yin magana da yaruka mabambanta.
Ni kaina na fahimci, sautin muryata tana sama idan ina Ingilishi yayin da kuma take ƙasa idan ina Faransanci, kuma tana sauri idan ina yaren Sifaniyanci. Kamar kowanne harshe yana fitar da wata sabuwar sauti dabam.
Masana harsuna suna cewa tunaninmu da jikinmu da kwakwalwarmu, har ma da yadda muke ganin kanmu suna taka rawar wajen yin yaruka daban-daban.
"Kamar yin fim ne inda ake ƙwaikwayon harsuna daban-daban domin bayyana kai a matsayin mai magana da wannan harshen." in ji Farfesa Ana Paula Petriu Ferreira Engelbert daga Brazil.
Ta yi bincike kan dalilin da ya sa muryarmu ke canjawa idan muka yi yaruka daban-daban, shin wannan canji gaskiya ne ko kawai tunaninmu ne?
Ta ce harsuna suna zuwa da nasu sautin dabam-dabam. "Misali Jamusanci yana amfani da sautuka daga bayan maƙogwaro, shi ya sa ake jin kamar murya ta fi kaifi. Faransanci kuma sautinsa yana fitowa ne a gaba shi ya sa masu magana da harshen suke matse laɓɓansu wajen magana."
Ta ya ya sautin murya ke canjawa?

Asalin hoton, Getty Images
Yadda muke magana — da yadda wasu suke jin sautin muryarmu — yana fitowa ne daga abubuwa da suka haɗa da yanayin tsarin halittar ɗan'adam da al'adu, da kuma yanayi.
Sautin muryar mutum tana farawa ne daga ƙwayar murya (vocal folds), sannan tana ƙara ƙarfi a hanyar murya (vocal tract), sannan harshe da leɓe, da baƙi suke tsara sautin, kafin ya fita a matsayin magana.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Duk wannan yana ƙarƙashin tsarin yadda jikin ɗan'adam yake aike wa da karɓar saƙo. Idan muna farin ciki ko cikin damuwa, ko baƙin ciki, sautin muryarmu tana canjawa," in ji Renata Azevedo, ƙwararriyar mai kula da magana a Jami'ar São Paulo.
Bugu da ƙari, ilimi da yanki da al'adu suna yin tasiri a sautin muryarmu.
"Kowane harshe yana da sauti na musamman. Misali, Ingilishi yana da wasu sautuka da babu a harshen Portuguese," in ji Azevedo.
Yanayi da al'adu ma suna canza sautin muryarmu. Engelbert ta ce idan mutum yana magana da harshen da ba nasa ba, yanayi da dalilin magana na canza yadda sautin muryar take wanda yake bambanta da yadda ake magana da harshe na ainihi.
A binciken, ta ɗauki sautin muryar wasu ƴan Brazil da ke magana da harshen Portuguese da Ingilishi a Amurka, akwai bambanci sosai: a harshen Portuguese, muryar mata tana sanyi yayin da a harshen Ingilishi kuma muryarsu tana ƙasa da kuma ƙarfi.
Masu sauraro da ke magana da harsuna biyu sun lura da wannan bambancin, suna ganin sautin muryoyi daban-daban suna nuna halaye daban-daban na mutane.

Asalin hoton, Getty Images
Tasowa da harsuna biyu
Ko mutanen da suka tashi suna amfani da harsuna fiye da ɗaya suna nuna ɗan bambanci a sautin muryarsu tsakanin harsunan.
Amma Engelbert ta ce ma'anar magana da harsuna biyu na iya bambanta. "Wani binciken da aka gudanar a shekarun 1990 ya nuna cewa masu magana da harshen Catalan da Spanish ba a samun bambanci mai girma a sautin murya tsakanin harsunan, amma koyaushe akwai harshe ɗaya da suka fi jin daɗin amfani da shi," in ji ta.
Waɗanda suka koya harshe na biyu daga baya yakan nuna bambanci tsakanin harshen gida da sabon harshe, musamman a farkon koyonsu.
Haka kuma yanayi yana tasiri. "Yawan hulɗa da sabon harshe yana sa canjin ya zama na dabi'ar sabon harshen" in ji ta.
Nahwu da kalmomi
Koyon wani yare bai tsaya ba a kalmomi da ƙa'idoji kawai. Mutum na iya koya ta hanyar amfani da shi da kuma jin mutane na asali da fahimtarsu da kallon finafinai, sauraron kiɗa, da karanta adabi suna sa a fi saurin iya harshen kuma yana rage bambancin muryar da ke tsakanin harsuna.
"Yayin da muka nutse cikin al'adun harshe, muryarmu da sautinmu suna bin yanayin harshen cikin sauƙi," in ji Azevedo.
Ta kuma ce yana da muhimmanci a lura da ƙananan abubuwa lokacin magana.










