Me zai faru bayan wa'adin da Wike ya bai wa ofisoshin jakadanci a Abuja ya cika?

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Litinin ne wa'adin da ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike ya bai wa ofisoshin jakadancin ƙasashen duniya kan biyan harajin fili ya cika.

Hakan na nufin cewa ofisoshin jakadancin ƙasashe 34 na fuskantar barazanar rufewa, bayan matakin da aka ga ministan na Abuja ya ɗauka a baya-bayan nan kan hukumomin da ya zarga da ƙin biyan harajin.

Aikin ƙwace filaye da minsitan na Abuja ke yi tun bayan hawan sa kan mulki na daga cikin abubuwan da suka fi tayar da ƙura a cikin ayyukan gwamnatin Tinubu a baya-bayan nan.

Harajin fili wani kuɗi ne da doka ta wajabta wa duk wanda ya mallaki fili ya biya gwamnati, kuma wannan ya haɗa da kowa, hatta ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke Najeriya ba a tsame su daga sauke wannan nauyin ba.

Sai dai hukumomin Abuja, babban birnin Najeriya sun ce mutane da hukumomi da dama sun yi watsi da wannan nauyi da doka ta ɗora musu, inda suke ƙin biyan irin waɗannan kuɗaɗe.

Hukumar kula da birnin tarayyar Najeriya (FCTA) ta ce ana bin ofisoshin jakadacin ƙasashen waje da ke Najeriya bashin jimillar kuɗi naira tiriliyan 3,662, 196 daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Waɗanne ƙasashe abin ya shafa?

Hukumar babban birnin tarayya, Abuja ta ce ƙasashe 34 ne aka samu da laifin ƙin biyan kuɗaden harajin filin.

Ƙasashen sun hada da: Ghana, Rasha, Thailand, Côte d'Ivoire, Philippines, Netherlands, Turkiyya, Guinea, Ireland, Zambia, Iraq, Uganda, Tanzania, Jamus, Congo, Venezuela, Koriya ta Kudu, Trinidad and Tobago, Masar, Chadi, Indiya, Sudan, Kenya, Nijar da Saliyo.

Tun farko a ranar 26 ga watan Mayu ne Ministan Abuja, Nyeson Wike ya bayar da umarnin rufe gine-gine 4,794 wadanda suka gaza biyan harajin fili na aƙalla tsawon shekara 10.

Sai dai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya shiga tsakani, inda aka tsawaita wa'adin da kwana 14, wanda ya ƙare a ranar Litini, 9 ga watan Yuni.

Ko Najeriya za ta iya ƙwace ofisoshin jakadanci?

Bayan cikar wa'adain da minista Wike ya bayar, batun da ke tayar da ƙura shi ne wane mataki hukumomin Abuja za su ɗauka sannan wane tasiri hakan zai yi ga hulɗar diflomasiyyar Najeriya da ƙasashen da batun ya shafa?

Ɓangarori da dama, ciki har da lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Femi Falana sun yi gargaɗi kan tasirin rufe ofisoshin jakadanci wasu ƙasashe a babban birnin Najeriya.

A tattaunawarsa da kafar talabijin ta Channels ranar Litinin, Falana ya ce "Idan muka kai samame a ofishin jakadanci wata ƙasa, hakan zai kawo zazzafar taƙaddamar diflomasiyya ga Najeriya. Ba a yarda da hakan ba."

Wani ƙalubalen da ake tunanin Najeriyar za ta fuskanta kan wannan batu shi ne tanadin sashe na 22 na yarjejeniyar Vienna da ƙasashen duniya suka cimma.

Masana na ganin duk da cewa Najeriya, a matsayinta ta ƙasa tana da ƙarfin iko kan duk wani fili da ke cikinta, akwai togiya a wasu wuraren musamman a ofisoshin jakadanci.

A ƙarƙashin sashen na yarjejeniyar Vienna, wadda ƙasashen duniya, ciki har da Najeriya suka amince da ita, ofishin jakadancin ƙasashe na samun kariya daga tsoma bakin ƙasar da suke ko da kuwa lamarin ya haɗa da zargin rashin amfani da filin yadda ya kamata.

Me dokar Vienna ta ce?

Sashe na 22 na dokar Vienna, wadda ƙasashen duniya, ciki har da Najeriya suka amince da ita ya ce:

1- Ba za a karya dokar harabar duk wani ofishin jakadanci ba. Jami'an ƙasar da ofisoshin suke ba su da damar shiga ciki.

2- Ƙasar da ofishin jakadanci yake a ciki na da aiki na musamman na ɗaukar duk matakan da suka kamata wajen kare shi.

3- Harabar ofishin, kayan da ke ciki da duk wani abu da ke ciki da ababen sufurinsa na da kariya daga bincike, ƙwacewa ko ƙaƙaba wata doka a kansa.