Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai biyar da suka sa gobarar Los Angeles ta yi matuƙar muni
Mummunar gobarar daji na ci gaba da ɓarna a sassan birnin Los Angeles, lamarin da ya haifar da matuƙar tashin hankali da asara.
Wannan ita ce gobarar daji mafi muni a tarihin birnin, wadda ta cinye aƙalla kadada 12,500 tare da tilasta kwashe dubban ɗaruruwan mutane. Aƙalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu, sannan an yi asarar gine-gine da dama.
Duk da ƙoƙarin da jami'an kashe gobara ke yi, har yanzu an kasa shawo kan gobarar.
Aƙalla gobara biyar ce ke ci gaba da ruruwa a faɗin yankin, a cewar jami'an hukumar kashe gobara ta California.
Gobarar Palisades, wadda ita ce ta farko da ta tashi, kuma ta kasance mafi girma, tuni ta kona filaye da dama, da suka haɗa da unguwar masu hannu-da-shuni ta Pacific Palisades, unguwar da mashahuran mutane irin su Mel Gibson da Paris Hilton ke da gidaje. Ana binciken musabbabin ta - tare da wasu gobara uku ta suka tashi a yankin.
Wata sabuwar gobara, da aka yi wa laƙabi da Kenneth ta tashi a yankin West Hills ranar Alhamis. Hukumomin yankin sun tsare wani mutum da ake zargi da tayar da ita da gangan.
Katsewar wutar lantarki ya jefa yankunan birnin cikin duhu, kuma cunkoson ababen hawa sun rufe tituna yayin da mazauna birnin ke yunƙurin ficewa. An tilasta rufe makarantu da jami'o'i.
Ko me ya sa wannan gobarar ta Los Angeles ta kasance mai tsanani kuma ta bazu cikin sauri?
1. Yawan tsirrai
Masana sun ce ruwan sama mai yawa a cikin 2024, wanda ke da nasaba da yanayin El Niño, ya haifar da yanayin da ke tattare da haɗarin tashin gobara a lokacin hunturun bana.
Rory Hadden, wani masanin kimiyyar gobara a jami'ar Edinburgh, ya yi bayanin cewa: "Ruwan sama na iya haifar da fitar tsirrai masu yawa, wanda hakan zai iya zama kamar makamashi ga gobara.
Sannan sai kuma a shiga wani yanayi da ke sanya komai ya bushe, kuma sai waɗannan tsirran su bushe da sauri, inda suke zama tamkar makamashi"
Wannan haɗakar tsakanin yanayin damina a shekarar 2024 da kuma lokacin zafi ya biyo baya, ya haifar da "ingantaciyar yanayi ga yaɗuwar wutar daji", in ji masanin kimiyyar gobarar daji Maria Lucia Ferreira Barbosa na Cibiyar Kula da Muhalli ta Burtaniya.
Wannan sauyin yanayi daga yanayi na ruwa zuwa busasshen yanayin ana kiran sa 'hydroclimate whiplash'. Wani bincike na baya-bayan nan ya gano cewa haɗarin tashin gobarar daji a duniya ya yi matuƙar ƙaruwa tun daga tsakiyar ƙarni na 20.
2. Iska mai ƙarfi daga yankin Santa Ana
Iska mai ƙarfi ta rikiɗar da wutar da ta tashi a tsaunukan da ke yammacin Los Angeles zuwa gobarar daji mai bazuwa da sauri, wadda ta bazu da taimakon busassun tsirrai ta kuma mamaye unguwar Pacific Palisades da ke kusa da birnin Santa Monica.
Galibi wannan iskar na tasowa ne da zafi kuma a bushe inda take taimakawa wurin ƙara busar da tsirrai.
"Duk gobarar daji na buƙatar abubuwa uku - wani abin da zai tayar da ita da abu mai ƙonewa da zai zama kamar makamashi da kuma iska," in ji Hadden. Duk da haka, gudun iskar da ke busowa daga hamadar California ta sa wannan gobara ta yi matuƙar muni.
An fi sanin iskar da 'iskar Santa Ana', ko 'Föhn' ko kuma 'hairdryer', tana kuma sanya gobarar daji ta kasance yadda ba a yi tsammani ba.
"Wannan iskar a bushe take sosai. Tana tafiya cikin sauri, don haka da zarar wuta ta tashi cikin sauƙi za ta kama ta kuma bazu cikin sauri," in ji Hadden.
A wasu lokuta, waɗannan guguwar iska na iya haifar da gobara ta hanyar saukar da turakun wutar lantarki, waɗanda ke sanya ciyayi ko tsirran da ke kusa su kama da wuta.
3. Fallatsar garwashi
Ba hura wuta kaɗai iska ke yi ba, iska ta kan kawashi tartsatsi da garwashi waɗanda su ne kan gaba wajen bazuwar gobarar daji, a cewar Hadden. "Abubuwa suna shiga gaban wuta su kawo mata cikas [kamar hanyoyi ko gine-gine]," in ji shi. "Amma babu abin da ya hana tashin garwashi, kuma suna matuƙar tafiya."
Iska na iya tayar da garwashi daga tsirrai masu ci da wuta, ya kuma kai su gaba. Za su iya faɗawa a kusa da wutar, ko kuma su yi fallatsa zuwa nesa su kuma tayar da wata sabuwar gobarar a wani wuri na daban.
"Akwai rahotannin irin tafiyar dogon zango da waɗannan abubuwan ke yi, suna sauka a cikin ramuka a kusa da gidaje ko a cikin furannin ado, su kuma cinna wa gidajen wuta," Hadden ya bayyana.
Idan wuta ta kama gida guda, jami'an kashe gobara na iya magance ta cikin sauƙi. "Amma matsalar ita ce, galibi gomman gidaje ne ke kamawa da wuta a lokaci guda da taimakon garwashi, sannan kowane gida yana samar da ƙarin nasa garwashin," in ji Hadden. "Don haka garwashi na da matuƙar tasiri a tashin gobara ta hanyar tafiya da take yi a iska."
Baya ga lalata kadarori, garwashi na da matuƙar hadari ga mutane. Alec Gellis ya shaida wa CBS News cewa, "Kamar garwashin sun lulluɓe ko'ina ne; babu iskar da mutum zai iya shaƙa," in ji Alec Gellis, yayin da yake bayyana abin da ya faru a lokacin da gobarar ta kama gidan budurwarsa. "Da kyar na iya kai wa ga mota ta."
4. Tuddai da tsaunuka
Tuddai da tsaunuka da ke yankin Los Angeles na ƙara haɓaka haɗarin da ke tattare da gobarar daji. Hadden ya ce "Gobara ta fi yaɗuwa cikin sauri a kan tudu."
"Irin wannan yanayin na iya sanya gobara ta kasance yadda ba a yi tsammani ba kuma hakan zai zame ƙalubale ga waɗanda ke ƙoƙarin yaƙi da yaɗuwar gobarar."
Haka kuma yana kawo cikas a yunƙurin kwashe mutane. Mike Bonin, wanda tsohon ɗan majalisar birnin Los Angeles ne, ya shaida wa jaridar New York Times cewa a yankin Palisades, ƙananan titunan da ke gefen tsaunuka na haifar da ƙarin ƙalubale ga mutanen da ke ƙoƙarin ficewa daga yankin.
5. Sauyin Yanayi
Masana sun ce sauyin yanayi na ƙara haifar da yiyuwar tashin irin wannan gobarar.
"Ba yanayin zafi da bushewa ba ne kawai. Haɗaka ce ta yanayin mamakon ruwan sama da iska mai ƙarfi da kuma tsananin zafi duk a lokaci guda," in ji Hadden.
Binciken gwamnatin Amurka ya nuna cewa waɗannan sauye-sauyen sun ƙara haɗarin tashi da kuma tsananin gobarar daji. "Sauyin yanayi, gami da ƙaruwar zafi da fari, sun kasance muhimman abubuwan da ke haifar da hadarin tashi da kuma munin gobarar daji a yammacin Amurka," in ji Hukumar Kula da ruwan teku ta Amurka.
Bayan da aka fuskanci zafi a cikin bazara gami da rashin ruwan sama cikin watannin baya-bayan nan, California ta kasance cikin matuƙar haɗari.
Ana tsammanin lokacin da aka fi samun tashin gobara a kudancin California na kasancewa ne daga watan Mayu zuwa Oktoba, amma gwamnan jihar, Gavin Newsom, ya nuna cewa a halin yanzu ba a kayyade shi ga wasu watanni na musamman ba. "Babu wani lokacin gobara," in ji shi. "Wannan shekarar ta gobara ce."
Ko akwai fata?
Jami'an hukumar kashe gobara suna da kyakyawan fata yayin da hasashen munin gobarar yankin kudancin California ya ragu sosai.
Sai dai mai hasashen yanayi na BBC, Sarah Keith-Lucas, ta lura cewa ba a hasashen samun ruwan sama a yankin na aƙalla mako guda mai zuwa, wanda ke nufin har yanzu yanayi ne da ke iya haifar da tashin wata gobarar.
Da yake magana a shirin tashar Radio 4, shugaban hukumar kashe gobara ta California, David Acuna, ya kuma yi gargadin cewa iska na iya ƙara haifar da ɓarna a yankin cikin kwanaki masu zuwa.
Kamfanonin masu inshora sun damu da cewa wannan na iya zama ɗaya daga cikin tashin gobarar daji mafi tsada a tarihin Amurka, inda ake tunanin asarar inshorar za ta haura dala biliyan takwas, saboda dimbin kadarorin da ke kan hanyar gobarar.
Babban abin da ya fi muni shi ne yadda aka ƙera tankunan ruwa na birnin ne don kashe gobarar da ke faruwa a ƙaramin yanki, ba wadda ta yadu a yanki mai girman gaske ba. Kayayyakin aikin da ake da su a ƙasa ba za su iya jurewa ɗaukar yawan ruwan da ake buƙata zuwa wurare masu nisa da ake buƙata ba yayin da ake fuskantar matuƙar matsin lamba.