Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mai digiri ta koma soya wainar fulawa da awara a Kano
Habiba Usman Hassan Habiba na ɗaya daga cikin dubban matasan Najeriya da suka ƙirƙirarwa kansu aiki bayan kammala jami'a a Najeriya.
Matashiya mai shekaru 25 da ta kammala karatun digirinta na farko a fannin kimiyyar zamantakewar halittu wato "Biology" a jami'ar North West da ke Kano.
Matashiyar ta fita da kyakkyawan sakamako a shekarar 2024 to sai dai kuma sakamakon rashin samun aikin yi Habiba ta tsinci kanta a sana'ar wainar fulawa da awara.
Habiba ta ce dalilin da ya sa ta fara wannan sana'a shi ne sakamakon rashin son zama ba tare da wani abun yi ba kasancewar neman aiki ya zama wani abu mai wahala.
"Duk da cewa na samu sakamako mai kyau amma idan mutum bai samu aiki ba to dole ne ya nemawa kansa mafita daga baya idan Allah ya kawo aikin sai a haɗa biyu," in ji Habiba.
Burin Habiba dai shi ne nan gaba ta samu wuraren tuyar wainar fulawa da awara masu yawa a birnin Kano.
"Mafarkina yanzu shi ne na ga na kakkafa wuraren sana'ar nan tawa fiye da ɗaya ta yadda duk wani da ke Kano da ke buƙatar cin irin waɗannan abubuwa shi ne ya zo wurina wato Flour Bliss."
Daga ƙarshe Habiba ta shawarci ƴan"uwanta matasa masu digiri da suka kammala jami'a ba tare da samun aikin yi shi ne su nemi ilimi sannan kuma dabarun sana'a ko kuma su ƙirƙiri sana'a. Ka da su raina sana'a komai ƙanƙantarta. Amma dole sai akwai jajircewa da sadaukarwa."
Masu saye
Daga zuwa wurin da Habiba ke gudanar da sana'arta wato 'Flour Bliss" za ka fahimci tana da masu sayen abincinta abin da ke nuni da cewa tana samun cinikin da take buƙata.
Wani abin sha'awa shi ne mafi yawancin masu sayen wainar fulawar ko awarar ko kuma shayin da Habiba ke yi matasa ne kamarta.
Za a iya cewa Habiba ta sauya tunain al'ummar jihar Kano dangane da wainar fulawa da awara da ake yi wa kallo da wasu kayan ƙwalamar da ba kowane mutum ne yake ci ba.
Habiba ta samu karramawa daga ƙungiyoyi da dama da ke son ganin matasa sun tsaya da ƙafafunsu.
Rashin aikin yi a Najeriya
Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, wanda ya nuna cewa an samu ƙaruwar rashin aikin yi a ƙasar da kashi 5.4 a wata ukun farko na shekarar 2024, na ci gaba da ɗaga hankalin mutane a faɗin ƙasar.
Sabon rahoton na nufin an samu ƙarin mutum 300,000 a kan miliyan biyar ɗin da ake da su a ƙarshen shekarar 2023 marasa aikin yi a faɗin ƙasar, wanda hakan ya haifar da cecekuce tsakanin mutane a daidai lokacin da ake fama da tsananin rayuwa a Najeriya.
A watan Agusta ne matasa a Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa, inda dubban matasa suka fito titunan ƙasar suna nuna rashin jin daɗinsu kan yadda tattalin arzikin ƙasar da nasu tattalin arzikin ya taɓarɓare.
Bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa birane ne suke da kashi 6 cikin 100 na marasa aikin yi, inda kuma yankunan karkara ke da kashi 4.3 kamar yadda rahoton hukumar ya nuna a ranar Talata.
Rashin aikin yi na nufin adadin waɗanda ba su da aikin yi, sannan suke fafutikar neman aikin yin.
Yaushe rashin aiki yi zai kau a Najeriya?
Yawanci idan ana batun matsala, hankali yakan koma ne kan batun yadda za a iya magance ta.
Game da yadda za a magance matsalar rashin aikin a Najeriya, Malam Lawal Habib Yahaya masanin tattalin arziƙi kuma malami a kwalejin kimiyya da fasaha a Kano inda ya ce ya danganta ne da yanayin shugabancin ƙasar.
A cewarsa: "Waɗannan abubuwan da na faɗa a baya, su ne ya kamata a gyara. Ya kasance albashin da ake biyan ma'aikata yana ƙaruwa, wato ya zama kuɗin da suke samu yana biya musu buƙata.
"Sannan a inganta tattalin arzikin ƙasar, ya zama ana sana'anta abubuwa. Idan tattalin arziki ya inganta, dole komai zai inganta."
To ko a ɓangaren ƴan ƙasa akwai abin da ya kamata su yi? Masanin ya ce yawanci matsalolin rashin aikin na da alaƙa ne da taɓarɓarewar tattalin arziki, kuma nauyin yana kan gwamnati ne.
"A tare suke tafiya. Idan ɗaya ya ƙaru, ɗayan ma zai ƙaru. Su ƴan ƙasa kamar raƙumi ne da akala," in ji shi,
"Idan gwamnati ta yi abu mai kyau masana'antu za su sana'anta kayayyaki, sannan sauran harkokin tattalin arziki za su haɓaka."